← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 96

Sashe 77

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amin Abba. Nagode. Nagode" Ya amsa da murmushi.

"Ni fa ba zan..."

"Bi mijinki ku tafi Hamdi. Sai da safe." Abba ya katseta da sauri.

Yana gama magana yabi bayan su Halliru. Aka barta da Taj. Hannunta ya kamo kada su yiwa Alhaji laifin barinsa jira. Suna zuwa su ka samu ya shiga gaba. Su biyun su ka zauna a baya. Motar tayi tsit. Alhaji ne kaÉ—ai yake jin wani irin farinciki na kasancewa tare da Taj a wannan yanayin.

Ribas Bishir ya yi idanun Alhaji su ka sake sauka akan motar Kamal. Da sauri ya ce da Bishir ya tsaya. Bai yi musu magana ba ya fita ya koma cikin asibitin. Shaf ya manta yaga motar lokacin shigarsu. To me yake yi a ciki basu gan shi a reception ba sannan bai neme su ba? Mota kuma tasa ce babu tantama.

Yana shiga ciki ya nufi wajen Receptionist É—in sai ga Kamal da Mubina suna fitowa daga koridon inda Emergency room yake.

"Kamal?"

Hantar cikin Kamal sai da ta kaÉ—a da ya tabbatar Alhaji yake gani. Ya yiwa Mubina kallon tuhuma sai tayi saurin girgiza kai.

"Baka da lafiya ne?" Alhaji ya tambaye shi.

"A'a. Dawo da ita nayi daga wajen dinner."

A tsanake Alhaji ya kallesu sannan ya ce "Me ka zauna yi to? Naga motarka tun zuwanmu kusan awa guda da ta wuce."

Kamal ya rasa ƙaryar da zai gilla sai Mubina ce ta ƙwato shi saboda yadda taga ya gama ruɗewa.

"Emergency case na samu Baba. Sai yanzu na fito."

"Allah Ya bada lafiya. Amma duk da haka da shi sai ya tafi gida tunda dare ya yi."

Haƙuri Kamal ya bashi. Yana shirin tambayar waye babu lafiya Alhaji ya sake yi masa tambaya.

"Me ma ya zaunar da kai? Ko akwai alaƙa a tsakaninku da ban sani ba?"

Kaɗan daga aikin Alhaji kenan. Faɗin magana kai tsaye ba tare da ɓoye ɓoye ba. Mubina ji tayi kamar ƙasa ta buɗeta shige ciki. Kamal kuma da yake neman mafaka tuni ya cafke wannan damar ya nuna hakan ne.

Tsaf Alhaji ya haÉ—e rai kuwa.
"To ni bana son irin haka? Idan kana neman mace sanar dani ya kamata ka fara yi saboda nayi magana da manyan ta. Amma haka kawai ka É—auko Æ´ar mutane ka zauna a wajen aikinta da talatainin dare irin wannan ai bai yi ba."

"Ayi haƙuri Alhaji."

"Kema da ki ka biyo shi baki kyautawa kanki ba. Na yarda da tarbiyar Kamal a matsayin uba amma ku Æ´aÆ´an zamani ba a ci muki laya. Allah dai ya kiyaye kawai."

Ita ma haƙurin ta shiga bayarwa ba ji ba gani.

Da dai Kamal yaga tarkonsa ya kama sai ya cigaba a haka. Ya karɓi laifin da bai yi ba ya cigaba da bada haƙuri. Sai da komai ya lafa ya tambayi waye babu lafiya. Da yaji Taj ne ai sai ya ture nasa ciwon ya fita. Mubina ma sallama tayi masa ta koma ciki.

"Alhaji mu je mana" ya dawo da ya ankara shi kaÉ—ai ya fita.

"Jeka. Likitan da ya duba shi zan tambaya game da wani bayani da ya yi min."

Da sauri Kamal ya wuce. Alhaji ya bi shi da kallo har ya fita sannan ya koma reception jiki babu ƙwari. Gabaɗaya Kamal ɗin ya sauya sosai. Tun rashin lafiyar kwanaki da aka ce allergy ne ya lura yaron nasa ba yadda ya saba yake ba. Ya dai haƙura da yawan tambayarsa ya jiki ne da yaga yana harkokinsa na yau da gobe babu fashi.

"Doctor ɗinnan da muka gama magana gobe ƙarfe nawa za ta tashi? Akwai patient da nake son ta duba min na manta ban faɗa mata ba."

Wani É—an littafi mutumin ya duba ya ce "yau bata da night (call), sai 3 na yamma kuma za ta shigo goben. Yanzu ma na san alfarma kawai ta yi masa tunda ya saba zuwa amma she is off."

"Shi wa kenan?" Alhaji ya ɓoye matsanancin tashin hankalin da ya kama shi.

"Wanda ka gansu tare."

"To nagode"

Wani irin sanyi mai farawa daga cikin ƙashi ne ya dirarwa Alh. Hayatu. Kamal bashi da lafiya kuma yana ɓoye masa.

Fargabar da ya dawo mota da ita ce ta hana shi sakar musu fuska yadda ya yi niyya.

"Alhaji ko su dawo motata?" Kamal ya tambaye shi bayan ya zauna mazauninsa.

Ba tare da ya kalli inda Kamal É—in yake tsaye da Taj ba ya ce "Tunda cinyesu zanyi ko?"

"Tuba nake." Kamal ya faÉ—i yana dariya "Happy mu haÉ—u a gidal"

Motarsu Alhajin ya koma shi kuma Kamal ya ja tasa shi kaɗai. Yana murna da Alhaji ya hana su biyo shi domin da sun ƙara lokaci a tsaye Taj zai cigaba da yi masa tambayar ƙure.

A motar ma duk da ba hira suke ba amma Alhaji sai da ya tambayi Taj ko Kamal ya faÉ—a masa me yake yi a asibiti cikin dare. Amsar bata sauya daga irin wadda ya bashi ba da kansa ba.

Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Kowa ya yi shiru har aka isa gidan. Da su ka isa tsayuwa su ka yi a bakin motar don basu san ina za su nufa ba kuma. Alhaji da ya san jiransa suke yi sai lokacin ya ɗan saki fuska bayan isowar Kamal. Wayar Inna ya kira kuma bai yi mamakin da bata yi bacci ba ta ɗauka. Ya ce mata ta fito akwai baƙuwa.

Inna ta taso da hijabinta don dama sallah kawai take yi tana addu'o'i. Da ta buɗe ƙofar sakin baki tayi kafin kuma ta fito waje sosai inda suke ta rungumo Hamdi.

"Alhaji lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau. Kawai dai naga bai dace ta koma gida a daren nan ba tunda matar aure ce."

"Haka ne" Inna ta gyaɗa kawai cike da mamakin da yaƙi ƙarewa "shi kuma wannan gidan Ahmad za a kai shi ko?"

"A'a" Alhaji ya amsa mata da wani irin murmushi a fuskarsa. Haka kawai yake jin son kyautata mata ko don yadda hankalinta ya tashi É—azu "a gidan nan zai kwana."

Wani irin farinciki mara misali ya sake mamaye Taj. Kamal kam rungume shi ya yi yana faɗin "mun gode Alhaji. Allah Ya ƙara girma. Ya ja kwana. Mun gode"

Ya dafa kafaÉ—ar Taj É—in "Happy zo mu je ka kwanta."

Sake basu mamaki ya yi da cewa "Kada ku takura, ya kwana a ɗakin ƙasa na ɓangare na."

Wai kuma sai ya juya zai shige ciki. Inna har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi ta juya ita ma da sauri tana mai danne kukan da take shirin yi. Taj kawai ta kalla taga yadda furucin mahaifinsa na ƙarshe ya kawo wani irin hasken annuri ya shifiɗe masa a fuska. Sai hamdala da take ta karanta daga laɓɓansa. Abin da ake jira kuma ake ganin kamar ba zai yiwu ba ne ya faru a lokacin da ba a zato.

"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min. Ina roƙon Allah Ya kawo maka ɗauki ta inda ba ka zato akan duk masifa ko rashin kwanciyar hankalin da zai tunkaroka. Na gode Yaya Hayatu."

Yau ake kira farar rana. Rabon da Zainabu Abu ta kira Alhaji da sunan da ta saba kiransa a matsayinsa na É—an uwanta ya manta. Yana son ya juyo ya bata amsa daidai da addu'ar da tayi masa amma ga Æ´aÆ´a da suruka a wajen. Don kada ya bada kansa sai ya gyaÉ—a kai kawai.

Hamdi ta ajiye fushinta a gefe domin wannan abu maƙiyi ne kaɗai ba zai taya Taj murna ba. Ita da bata cika son magana ba sai take jin ya kamata ta ƙara nunawa Alhaji cewa mahaifinta ya horar dasu da kyakkyawar tarbiyya. Da wannan tunanin a duƙa har ƙasa a gefen Inna. Muryarta a hankali cikin nutsuwa ta ce,

"Allah Ya saka da alkhairi Alhaji. Allah Ya bamu ikon faranta maka fiye da yadda kayi mana. Mun gode."

Sai yanzu ya yi magana "babu komai. Ku shige ku kwanta."

Inna dama jira take ta sami damar yin kukan farinciki. Da sauri ta wuce ciki. Tana riƙe da hannun Hamdi har ɗakinta. Ƴan kwanan kowa ya kwanta banda mutum biyu Badi'a da Sadiya da su ka san Taj babu lafiya. Basu tashi matan gidan ba su ka zauna jiran su Alhaji. Suna ganinta da Hamdi ta yi musu bayani kafin ma su tambaya.

"Aikin babanku ne ya taho da ita daga asibiti wai dare yayi."

Badi'a ta ce "to ina Taj É—in?"

Da wata irin murna ta wanda yake cikin zaƙuwar bada labari ta sake cewa "Alhaji ya dawo dashi gida"

Sai kuma ta faɗi cikin sujjada tana yiwa Allah kirari. Hanyar fita Sadiya tabi za ta fita ta fesawa ƴan uwanta Inna ta dakatar da ita. Ta nuna mata dare yayi ga gajiyar da aka kwaso. Da ƙyar Sadiya ta haɗiye zancen ta haƙura sai asuba.

"Hamdi akwai ruwa a heater. Ki É—an watsa ruwa don jikinki yayi daÉ—i sai ki kwanta."

Babu musu ta tashi za ta shiga banɗakin da Inna ta nuna mata. Jikinta tayi tsamin gajiya sosai. Innar ta bata wata doguwar riga da ƴar hula ta shige dasu. Kafin baɗakin akwai wani ɗan wuri da aka saka shoe rack da wani ɗan tabur inda aka ajiye mai da turaren jiki irin oils ɗinnan na Scentmania irin nata. Nan ne wurin shafa mai sannan mutum ya shiga ɗaki ya ƙarasa shafe shafensa. Wanka tayi ta ɗauro alwala. Tana fitowa ta samu su Sadiya sun kwanta. Sai Inna dake sallah. Dama tana kunyar yadda za ta kwanta ɗaki ɗaya da mahaifiyar Taj. Da taga tana sallah kawai sai ta zauna. Ita kuma Inna da ta idar ta tambayeta me ya hanata kwanciya.

"Nima sallar zan yi Inna."

Wani murmushin farinciki da Inna tayi ya nuna tsantsar jindaɗinta. Ta bata hijab su ka yi raka'a shida sannan Hamdi ta soma hamma. Sai tayi kamar ta idar. Ai kuwa akan abin sallar Hamdi tayi bacci. Wannan qiyamul laili da tayi tare da Inna kuwa ta saya mata wajen da babu wata mace da za ta taɓa auren Taj ta mallaki wannan gurbi. Kaɗan daga sirrin Tahajjud!
Chapter 77 · 0% Book details