Sashe 93
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai dai naka ƴaƴan suna gida ko?" DPO ya ce a harzuƙe.
"La shakka."
"To jeka ka kawo Salwa É—in ka kama gabanka."
Wani sassanyan murmushi Kofur Ɗanliti ya yiwa Ummi da zai fita. Harda cewa ta kwantar da hankalinta. Yanzu gaskiya za ta yi halinta. Ƙila ma a yau ta sami damar tafiya.
Tsawar da DPO ya daka masa ce tasa shi gaggawar fita yana ƙananun surutai akan ƙulle mutane ba bisa haƙƙi ba. Ita kuwa Ummi wata muguwar harara ta galla masa da ya juya. Tun zuwansu yake ta rawar ƙafa a kanta. Matan da suka yi mata duka ma ya so basu horo irin yadda ake yiwa masu laifi saidai yana ganin shugabarsu ya fita yana Allah Ya isa. Matar regular ce kuma tantiriya. A tsaye ta fishi nesa ba kusa ba.
Ba a jima ba su ka shigo da Salwa. Ta tsaya musu ƙerere tana harararsu. Ta gane iyayen Hamdi ta kuma gane iyayen Ummi daga kamanninsu.
"Durƙusa" Kofur Ɗanladi ya ce da tsawa saboda haushinta da yake ji.
DPO kai ya girgiza kawai don ya É—ago shi ya ce Ummi ta maimaita abin da ta ce. Nan kuwa ta nuna sam bata san komai akan Taj ba. Salwa ke son shi kuma ita ce tayi masa asiri.
"Lallai ma. To a ina na samo turaren? Ba ke bace ki ka bani?" Salwa ta kalli DPO "Wallahi cewa tayi idan na shafa masa zai saki Hamdi ya aure ni."
"To yanzu me ya haÉ—a ku faÉ—a?"
Salwa ta ce tayi amfani da turaren yadda aka ce amma Taj wulaƙanta ta ma yayi fiye da yadda yake yi a baya.
"Ummi har kin san bin bokaye kuma?" Iyaa ta fashe da kuka.
"Nima bani aka yi Iyaa. Don Allah ku tafi dani gida."
Ba a wani sha wahala ba ta faɗi cewa Alh. Usaini ne ya bata. Kuma a zahiri ga abin da ya ce mata zai faru da Taj saɓanin yadda su ka faɗawa Salwa.
"Aikin ku nayi muku kenan? Kin san mutanen da na rabu dasu saboda tunanin zan sami Taj?" Salwa tayi kan Ummi cikin ɓacin rai.
Kofur Ɗanliti yayi saurin anjige ta kafin ta cakumi Ummi ta faɗi a ƙasa. Abba Habibu da Yaya sun ga ikon Allah. Bayan Ummi ta kwatanta inda za a sami Alh. Usaini. Ta tabbatar musu da cewa akwai chats ɗinsu harma da recording ɗin wayoyinsu a wayarta.
"Damma kin shiryawa rana irin wannan ne?"
"A'a, na dai kula idan muka gama chatting yana bin duka abin da ya turo ya goge. Shi yasa na soma yin screenshot saboda kada a gaba wani abu ya faru ya zame ya barni."
"Allah ma Ya sa kina da wayonki. Irinsu haka su ke amfani da marasa wayo su cuce su."
Ayyanawa Ummi tayi a ranta cewa indai Kofur ÆŠanliti yayi gigin cewa yana sonta, za ta nuna masa rashin mutumcin da zai jima yana yi masa ciwo. Idan ba karambani ba ai shi ma daga gani ya san su ba sa'annin juna ba. Duka duka bai fi rabinta ba a faÉ—i. Tsayi kuwa ba zai wuceta ba.
Gida Abba Habibu ya buƙaci Yaya ta koma tunda kawo Alh. Usaini zai ɗauki lokaci. Babu musu ta tashi. Jikinta yayi matuƙar sanyi. Ka haifi đa ya zama silar zubar mutumcin mutum babu ruwansa da gazawar tarbiyya. Wani duk ƙoƙarin iyayensa sai ya janyo musu magana hankalinsa yake kwanciya.
Baba Maje ma ya ce Iyaa ta tafi ta nuna zama za ta yi. So take taji ƙarshen wannan abu da Ummi ta zama sakarya wajen jagosarsa.
Minti ashirin bayan tafiyar Yaya sannan aka zo da Alh. Usaini. Tun a waje yake ta bala'i da zage zage. Da yaga Ummi sai ya taɓe baki.
"Kina da shaidar nunawa kice da hannuna?" Ya kalli Salwa "ke kin sanni ne?"
"Kaga ka ajiye wannan surutun zai amfane ka a kotu."in ji DPO
"Kotu??" Salwa da Ummi su ka maimaita cikin tashin hankali.
"Ƙwarai kuwa. Kafin lokacin muna buƙatar shi Taj ɗin a nan."
Ranar har dare suna station dai. Taj da Hamdi su ka zo aka maimaita komai. Ya dubi Alh. Usaini ya ce masa da shi da su Salwa duk ya yafe musu ya juya ya fita. Fitarsu ke da wuya mahaifin Alh. Usaini ya je. Bayan ya gama zagi da ci masa mutumci a gaban mutane yace ba zai bashi shugabancin komai cikin kadarorinsa ba. Gado ma ba don Allah ne Yayi da Kansa ba tabbas da ya ce ba zai gaje shi ba. A ƙarshe ya fice. Su Baba Maje ma su ka kama gabansu. Abba Habibu ne ya karɓi Ummi albarkacin iyayenta. Salwa ma an saketa amma ko da ta fito ta rasa inda za ta tafi.
***
Da Hamdi ta shiga ɗaki a kwance ta sami Taj amma ya juya mata baya. A hankali ta lallaɓa ta hau gadon ta kwanta a bayansa. Hannunta ɗaya ta zura ta ƙarƙashin jikinsa, ɗayan kuma ta gaba ta haɗe su ta rungume shi.
"Kuka kake yi ne?"
"Tsokana ta ma kike yi?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba.
"Ƙorafi dai na zo yi. Ta yaya zan aureka kuma ace safe, rana da dare duk ni ce a kitchen. Gaskiya da sake."
Tashin da bai yi niyya ba yayi.
"Kin manta halin da nake ciki ko kuwa da gaske tsokanar ce?"
Hamdi ta ce "Ka faÉ—a min damuwarka ne? Ba da kaina na nemo amsar ba?"
"Da ki ka nemo ba ki ji tausayina ba?"
"Girkin ne ba za ka tayani ba kake tada zancen?" Ta kyaɓe fuska.
Taj ya riƙe baki da yaga da gaske idanunta suna neman zubo da ƙwalla "Abu ya same ni amma saboda ƙarfin hali ke ce da ɓata rai da shirin kuka?"
"Na fi ka shiga tashin hankali. Ka da aka mana aure hancin ka da baki duk suna aiki. Yanzu da haka ta faru sai anyi min cikon sadaki." Tayi kicin kicin da fuska.
Taj bai san lokacin da ya soma dariya ba "cikon sadaki fa kika ce?"
Ta goge ƙwallar ƙarya "Eh mana. Na baka tausayi ko?"
"Haƙƙun."
"Zan iya yafewa in za ka yarda ka fito daga É—akin nan mu shiga kitchen."
"Hamdi..."
"I'll be your nose" ta tsaya akan gwiyoyinta akan gadon ta goga hancinta da nasa "and your tongue." Ta rataya hannuwanta a wuyansa ta sumbace shi "I'll be you har ka sami lafiya."
Ƙanƙameta Taj yayi. Ta dage ta ƙi barin raunin zuciyarta ya bayyana balle tayi kukan da take ta dannewa.
"I love you."
"Me too" ta faÉ—i har lokacin wuyanta na kafaÉ—arsa.
A ranar bata yarda sun sake komawa wannan zancen ba. Sai ma mitar da take yi wai ta rasa sunan da za ta dinga kiransa. Ya Taj É—in da take jindaÉ—in faÉ—a shi taji Salwa na kiransa dashi. Yana dariya ya ce
"Ki kirani Malam kawai?"
Ita ma dariyar tayi ta ce "Happy ya ishe ni. "
***
Washegari Taj yaje gida ya faɗawa su Inna abin da ya faru. Da Salwa ta san illar baki da bata janyowa kanta abin da zai sa ta shiga bakin mutane ba. Hajiya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta kira Alhaji ta faɗa masa. Hankalinsa ya sake tashi fiye da baya. Bayan sun gama jajantawa juna ya kira sauran matansa. Sun jima suna magana da Inna yana kwantar mata da hankali. Ya ce su dage da yin addu'a. Shi kuma zai san yadda yayi da Alh. Usaini. Yadda su ka ƙulla abin su za su kwance in sha Allah.
"Kun sa ranar dawowa ne?"
"A'a. Za mu yi magana daga baya."
Ajiye wayar yayi yana ta juyayin abubuwa. Case ɗin Taj da Kamal ba ɗaya bane amma a ƙalla mahaifiyar Taj ta san abin da ya shafi ɗanta. Addu'arta tana kai masa. Hajiya fa? Ta ina zai fara? Duk da haka dole ta sani zuciyarsa ta faɗa masa.
Kamar haÉ—in baki a daren ranar Yaya Hajiyayye ta kira shi tana tambayar saura kwana nawa su dawo.
"Mene ne?"
"Alfarma zan roƙa ku ƙara lokaci. Nan da kwana shida zamu taho in sha Allah."
"Ba na ce Taj ya bari Hamdiyya ta sami visa ba?"
Yaya Hajiyayye tayi dariya "ai ta samu. Surprise mu ka so yi muku. Yanzun nan nayi tunanin kada fa garin surprise mu yi saɓani."
Farincikinsa ya nuna. Ya ajiye wayar sai yaji sanyi yana ratsa shi. Yaya zsi yi da matansa? Dama yana kusa ne da sauƙi.
Haka nan ya yi ta maza ya kira Hajiya. Tunda taji ya ce ta keɓe za su yi magana gabanta ya faɗi. Ya fara da wa'azi ds tunatarwa akan sharuɗan imani.
"Na yarda da ƙaddara. Ka faɗa min kawai me na rasa." Ta ce da rawar murya.
"Baki rasa ba amma duk wani hope yana neman ƙare min."
Jikinta taji yayi nauyi ta sami waje ta zauna. Duk yadda Alhaji ya so rage mata raɗaɗin da za ta ji ta hanyar amfani da kalmomi masu kwantar da hankali abu ya faskara. Kamal yana dab da rasa rayuwarsa saboda rashin dacen mai bashi ƙoda.
Yayi zaton za ta yi kuka sai yaji shiru. Can ta numfasa.
"Yaushe ne akwai jirgi kurkusa?"
"Zan bincika..."
"Ka duba ka biya mana. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Sai ta katse kiran.
Alhaji ya yi ta kiranta taƙi ɗauka. Mama ya nema yace su haɗu da su Inna yana da magana. Su ukun nan kuka suke yi babu mai rarrashin wani. Su ka shiga ɗakin Hajiya su ka sameta tana haɗa kaya.
"Ku ma ku gaggauta haÉ—awa domin ko gobe aka sami jirgi zamu tafi tare ko?"
Cikin kuka Umma ta ce "dolenmu Hajiya." Inna da Mama kuwa ko bakin magana babu.
Basu bari yaran sun sani ba. A kwana uku aka gama yi musu komai. Yaran nasu suna ta mitar me yasa basu jira su tafi tare ba. Mama tayi ƙarfin halin cewa mijinsu ke nemansu. Aka mayar da abin shaƙiyanci ana dariya.