← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 96

Sashe 18

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin dandazon mutanen da su ka zo taron harda ƴaƴa da jikokin Alh. Hayatu Sule. Akwai jikarsa Firdaus ƴar wajen babbar ƴarsa Hajiyayye cikin masu fita. Yarinyar mutuniyar Taj ce sannan bata san ya zo gari ba. Rabonta da shi tun tana ƴar ƙarama. Shi yasa da Hajiyayyen ta gayyaci ƴan uwanta zuwa graduation shi ya fara amsawa zai je. A cikin hayaniyar programs ɗin da ake gabatarwa da hirar ƴan uwansa yaji wayarsa tana vibrating. Sunan Amma ya gani ba shiri ya tashi yana neman wurin da zai iya amsa wayar ba tare da hayaniyar ta hana shi jin me take cewa ba. Kamar ance ya kalli damansa ya hango wata yarinya tana tafiya da sauri sauri ta nufi bayan Admin block. Sanye take da ankon ƴan graduation ɗin da gown ɗinsu. Ta riƙe hular a hannu. Ɗaurinta na Maryam Babangida ya zauna đas a kanta. Sai ɗan mayafi da ta yafa a kansa ta rufe wuyanta da shi.

Numfashinsa kusan ɗaukewa ya yi da ganin yarinyar kamar yau ya fara ganin mace. A kallon farko ya iya tantance tsayinta da yake matsakaici. Fatarta da yake iya gani a fuska tayi daidai da wankan tawarɗa da ake kiran masu sirkin fari da baƙi. Fuskar ya sake kallo wadda ta fizgi duk wani rational tunanin dake yawo a kansa. A cike take da duk wani abu da yake muradi a wurin mace. Ga ƙarin kwarjini da nutsuwa da yake da yaƙinin tana da su daga yanayin tafiyarta. Wayar da yake son ɗauka tuni ya manta da ita har ta katse.

Kamar ana ingiza shi ya bi ta. Idanunta a rufe lokacin da ya hangota. Ta sanya hannu ta rufe kunne tana karanto abin da ta haddace.

Sannu a hankali ya dinga takowa gabanta har ya rage babu nisan kirki a tsakaninsu.

Ƙamshin da Hamdi taji yana ta kusanto ta ne ya hanata buɗe ido. A zuciyarta ta gama tsorata don an saba faɗin akwai ƙwanƙwamai a bayan Admin block. Wai ba a ganinsu sai dare. To me ya fito dasu da hantsin nan lokacin da ake ta kai kawo a makarantar?

Taj na jin yadda ta ja numfashi ta kasa saukewa da ya matso. Ya saki murmushi.

"BuÉ—e idonki."

Hamdi ta tsuke baki don in ta sami wuri akwai tsiwa. To yau dai aljanu za ta nunawa bata tsoronsu don kada su maketa a banza. Ta sha jin labarin idan baka nuna tsoronsu ba, ba sa yiwa mutum komai.

"Anƙi ɗin. Tsakanina da aljani nan gani nan bari. Na riƙe Ayatul Kursiyyu."

Dariya Taj ya yi a hankali ya a jin wani irin abu na bin jikinsa.

"Ni ba mai cutarwa bane so you can open your eyes."

Ido ɗaya ta ɗan buɗe a hankali ta tabbatar mutum ne sannan ta buɗe ɗayan. A lokaci guda idanuwansu su ka sarƙe cikin na juna sai dai Hamdi bata iya zurfafa kallon ba ta kawar da kai. Babu abin da zai sa ta iya jurewa kallon idanun mutumin dake gabanta masu kaifi da su ka tsareta. A zuciyarta kuwa sai da ta kira sunan Allah saboda tunda take bata taɓa ganin wani namiji taji ina ma ace....ba sai a kan wanda yake gabanta.

A daidai lokacin su ka ji sanarwa ta sipika.

"Bayan wannan gajeriyar diramar da za ayi mana mai taken Ilimi a Karkara, za mu saurari speech daga bakin overall student É—in makarantar nan Hamdiyya Habib."

Wani haÉ—aÉ—É—en ruÉ—ani Taj ya gani a idanun yarinyar gabansa. Da haka ya gane ita ce aka ambaci sunanta.

Takardar hannunta yaga ta kalla kamar za ta yi kuka.

"Kin taɓa ganina?"

"A'a."

"Good. Ki yi imagining ni ne duka mutanen wurin can sai ki yi speech É—in naki na ji."

Kamar ta ce a'a sai dai ta gyara tsayuwarta. Ta rufe ido.

"Open your eyes and think of ..." ya kalleta "Wa ki ka fi so a duniya?"

"Iyayena."

"To ni ne su. Ki sa a ranki su kaÉ—ai ne a wurin."

Sallama tayi da rawar murya ta soma da gabatar da kanta amma ta kasa faɗin sunanta ma. Sai komawa baya take yi. Taj ya karɓi takardar ya dunƙuleta a cikin hannunsa bayan ya karanta a gurguje.

"Bayan godiya ga school da iyayenki za ki bawa students shawarar karatu. Do you realy need a paper to say all that?"

Hamdi ta ƙifta idanu "no."

"Then say what you truly want to say from your heart. You will be fine in sha Allah."

Haka kawai magana da shi ta sanya mata wata irin nutsuwa. Ta tattare doguwar rigarta sama kaÉ—an ta dube shi da murmushi a fuskarta.

"Thank you."

Ya so sake cewa wani abu amma tunawa da ya yi tana buƙatar nutsuwa kafin ta iya yin abin da ke gabanta sai ya barta ta tafi. Ya raya a zuciyarsa idan an gama taron zai nemeta.
RAYUWA DA GIƁI 10

Batul Mamman💖

***

Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana.

Mantawa tayi da kowa da komai ta yi taƙaitaccen speech ɗinta mai ma'ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. Ɗalibai ƴan ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ƙarfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ƙara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta.

Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu'ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ƙayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluɓe da ledar ado aka ɗaure. Ya miƙa mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah.

"Allahu Akbar" Malamin da yake MC ya faÉ—i, sai É—alibai da iyayen yara su ma su ka amsa.

Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage ɗin idanunta cike da ƙwallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ƴaƴan ƴan uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro ɓangaren maza aka yi murnar tare da shi.

"Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ƙarfe biyu nan."

Halifa ya ƙara da cewa "ana can ana haɗa miki ..."

Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ƙeya.

"To fesal uban zance."

Hannu Hamdi tasa ta saƙalo kafaɗarsa tana dariya "rabu da ita Halifa. Idan ka faɗa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision ɗina."

Da sauri Zee ta riga shi faÉ—a.
"Walimar Æ´an gida za ayi miki"

"Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ƙwalama za a sayeki cikin sauƙi" cewar Sajida tana taɓe baki.

Kayan nata ta nuna musu su ka haɗu da cousins ɗin nasu aka kwaso cikin ƙanƙanin lokaci. Ta koma cikin ƴan uwanta ɗalibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta.

Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na ɗazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faɗa idan su ka ɓata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa.

*

Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matuƙar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaɓi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haɗa biyu ba. Mijinta shekarsa huɗu da ritaya ya koma gida gabađaya.

"Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo."

"Ba ki faÉ—a mata ba daÉ—ewa zan yi ba?"

"Nayi mata bayani duk taƙi ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?"

Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ƙyar ta haƙura bayan ya yi mata alƙawarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma ɗin inda take zama da amaryarsa da yaransa.

Yana dawowa cikin ƴan uwansa Firdaus ta janye shi tana ta nunawa ƙawayenta Uncle Taj. Daga hoto ɗaya sai da aka yi yafi goma. Masu ƙyasawa da yawa su ka kasa ɓoyewa. Shi dai ya biye mata ne kawai saboda ko a cikin jikokin gidan ita ce ƴar gaban goshinsa. Indai ana hutu tana yawan kiransa. Ana hoton da hayaniyar amma idanunsa yarinyar nan Hamdiyya Habib su ke nema. Da bai ganta zuciyarsa bata kawo komai ba tunda yana da yaƙinin Firdaus ba za ta kasa saninta ba. Bai san Hamdi bata da ƙawa ba. In ka cire sunanta ko sunan unguwarsu babu wadda ta sani.

***

Washegari jirgin ƙarfe bakwai ya bi zuwa Abuja. Idan buƙata ta biya so yake ya dawo a ranar don yanzu ya matsu ya koma wurin Amma. Da yake tun dare ya sanar da Daddy mijin nata cewa yana tafe, yana isa direba ya zo ya ɗauke shi.

Iyalan gidan ba baƙinsa bane tunda su na yawan kai ziyara America har Hajjo. Ƴan mata uku ne ƴaƴan kishiyar Amma da ake kira Anti. Su ma duka sun saba da shi. Dama tun zuwansa yana son tahowa Abujan su gaisa amma aiki ya hana. Tarba mai kyau ya samu daga Antin da ƴaƴanta. Sai da ya ci abinci ya ƙoshi sannan aka yi masa ido ɗakin Hajjo.

A hakimce kan kujera ya sameta ta kashingiÉ—a tana danna remote.

"Wannan zuwan na san na Jamila ne ba don neman albarkar tsofaffi ba."
Chapter 18 · 0% Book details