← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 96

Sashe 2

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan Ummi da Siyama ya ɗaure. Zee kuwa duk abinta na rashin damuwa yaƙe ta kama yi da taga yanayin fuskokinsu. A kitchen kuma numfashin Hamdi ya kusa ɗaukewa da Yaya tayi musu izinin shigowa.

Abbansu ne a gaba. Sanye yake da jallabiya yana tafe jiki na rangaji irin na riƙaƙƙun mata. Ga hula zanna bukar da ta ɗan sha jiki ya kafa a karkace. Shigarsa dai da ta sani ta yau da gobe. A bayansa wani mutum ne mai jiki wanda da alama shi ne baban su Ummi.

Suna shiga falon ta leƙa ta tagar kitchen ta hango yadda yake magana yana tafa hannuwan mamaki yadda mata su ke yi harda riƙe haɓa.

"Altine kece haka? Ikon Allah." Ya zauna a kujerar kusa da matarsa. "Gaskiya rabuwar zumunci bata yi ba ko kaÉ—an."

Fuskar Iyaa wasai ta amsa gaisuwarsa sannan ta mannawa yaran nata harara. Ba shiri kowacce ta miƙa gaisuwa da girmamawar dole. Ga mamaki ƙarara bayyane a fuskokinsu.

Namiji har namiji Ummi ta ayyana a ranta. Dogo ne don sai yau ta raina tsayin babanta. Jikinsa babu rama amma yadda yake karairaya shi yasa babu mai cewa jikin namiji ne da ya amsa sunansa. Fatar nan dabbara dabbara alamun an sha bleaching a shekarun baya. Yana buɗe baki kuwa haƙoran Makka ne na azurfa a sama har biyu suna maraba da baƙi.

"Kan uban can...ÆŠANDAUDU ne?"

Ta yiwa kanta tambayar a zuci ba don tana neman ƙarin bayani akan zahirin da idanuwanta su ke gani ba.

Abba kuwa da zafin nama ya fita shigo da kulolin abinci ita kuma gwanar ta É—auko Æ´ar wayarta tamkar mai duba wani abu ta soma yi masa hoto a fakaice. Sautin wayar ma a silent ta saka don kada kowa ya gane. Siyama ce kaÉ—ai ta kula kuma a take jikinta ya yi sanyi don ta sani babu ko tantama irin murmushin fuskar yayarta a lokacin na nufin abin da take yi ba na alkhairi bane.
RAYUWA DA GIƁI 2

Batul Mamman💖

Banda hotuna har sautin muryarsa Ummi ta É—auka daidai inda yake kiran Hamdi ta kawo salad. Tana jin kiran ba amma saboda tsoron yanayin da za ta tarar da fuskar Ummi na farincikin samun lagonta sai ta kasa amsawa.

"Abba bari na kira ta." Zee ta miƙe tsaye.

"Matso mu su da plates bari naje."

Tashi ya yi ya tattare gefen jallabiyarsa ya riƙe da hannu ɗaya ya fita. Ya samu ta gama haɗa komai ta lulluɓe da clig (farar leda ta rufe abinci) kamar yadda ya koya mu su. Haɗin ya yi kyau gwanin ban sha'awa. Ya murmusa cikin jindaɗi yana ɗaukan tray ɗin. Ko ƙanƙani bai san wani abu girman kai ba musamman a tare da iyalinsa.

"Allah Ya yi albarka Hamdi. Mu je a ci abinci."

Jingina tayi da sink ta juya masa baya kamar wani abu za ta wanke ta gyaɗa kai. Amsawa da baki zai iya ankarar dashi kukan dake barazanar ɓalle mata.

Shi kuwa kamar ya sani ya ajiye tray É—in ya juyo da kafaÉ—unta.
"Hamdi?"

Ai suna haɗa ido sai kawai ta fashe da kuka. Zuciyarta tamkar ta fashe saboda baƙincikin da take ji. Wani abu mai masifar ɗaci ya dinga kai komo a cikin ƙirjinta. Duk gidan tana da yaƙinin tafi kowa takaicin fita tsatson bawan Allahn nan. Ranta yana ƙyamarsa. Albarkacin karatun addini yasa ta daina danganta shi da munanan kalmomi da fata a zuci kamar yadda take yi a baya. Asalin da mutane ke tutiya dashi Yaya ta janyo sun rasa ta da haifesu tare da tubabben Ɗandaudu. Mutumin da har yau idan aka yi rashin sa'ar gamuwa da tsofaffin abokansa sai kaji ana kiransa Simagade.

Hankalinsa tashi yayi da ganin hawayenta ya dinga tambayarta damuwarta. Da bata ce komai ba ya yi yunƙurin rungumeta domin rarrashi amma sai ta banƙare jiki ta ja baya. Dama can ta saba yi masa haka don shi tarairayar yara sai dai wani ya koya a wurinsa. Na yau ne da ya sanya masa shakku tunda ya san ta kan bari sai dai ta zare jiki da wuri. Kallon tuhuma ya bita da shi sai ta wayance ta ɗago hannun da ta yanke ta nuna masa.

"Ya Salam" ya ce da ƙaramar muryarsa "Sannu. Jeki falo ki jira ni."

Tray ɗin salad ɗin ya ajiye ya fita cikin ruwan nan mai ƙarfi ya shiga ɗakinsa. Haƙƙin iyaye da a kullum shi ne jigon dake hanata fito masa da zahirin abin da take ji game da shi yasa ta ɗauki tray ɗin. Idonta da na Ummi su ka haɗu taga abin da take gudu muraran a tare da ita. Jikinta ya sake yin sanyi.

Sallamar Abba ta dawo da ita duniyar mutane. Ya zauna akan hannun kujera ya ce ta kawo hannunta. Ɗan akwati gare shi irin na gidan ƴan boko da ya adana magunguna da kayan taimakon gaggawa. Ya umarci Zee da zubawa kowa abinci shi kuma ya zauna bawa ƴarsa kulawa. Spirit ya dangwala a jikin auduga ya goge ciwon. Ga azabar zafi saboda ba ƙaramar yanka bace amma ko uhumm ta kasa cewa. Allah Ya sani zafin da take ji a zuciyarta yafi raɗaɗin ciwon. Saboda yadda ta ƙyamaci rayuwar mahaifinta bata ƙaunar gabaɗaya abokan sana'arsa. A son ranta namiji ko ruwan zafi aka ce ya dafa ya dawo ya ce ya ƙone saboda rashin iyawa. Namiji mai shiga kitchen ba zai taɓa yi mata kwarjini ba balle har taga ƙimarsa.

Dressing sosai ya yi mata ya kawo auduga ya É—ora ya manne ta da plaster. Gwani ne sosai ta wannan fannin wurin son ganin komai ya tafi daidai kamar wani bature. Ire iren abubuwan nan harda Abban da yasa su ke kiransa kamar ba talakawa ba duk bata so. Cikakken namiji bahaushe a wajenta ai Baba ake kiransa ba wani iyayin Abba ko Daddy ba.

Kowa sannu yake mata tana amsawa da ka. Da kuma wannan damar ta samu ta gudu ɗaki ta kwanta. Ba ita ta sake fitowa ba har sai da baƙin su ka tafi bayan Iyaa da su Ummi sun leƙo sun mata sallama.

***

"This is crazy Taj. Waye yake tattara duka ƙwansa ya sanya a kwando guda?"

Wata kamilalliyar dattijuwa sanye da doguwar rigar bacci da ƴar hula ta furta da takaici. Huci take cikin ɓacin rai tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune yana murmushi kamar abin da take faɗi da wani take a talabijin ba shi ba.

"Tajuddin!" Ta kira shi da ƙarfi da gargaɗi.

"Yes Ma" ya miƙe tsaye gami da sara mata. Ta sake tamke fuska.

Shi ma da alama ya gama shirin bacci ne don wandon jikinsa three quarter da singileti basu yi kama da kayan mai shirin fita ba.

"Ina wasa da kai ne?"

Ya girgiza kai.

Abin da ta san za ta yi ya dawo da hankalinsa gareta yadda take so ta aikata.

"Ko don kaga ba ni na haifeka ba? Shi yasa ban isa..."

"Amma gorin haihuwa kuma za ki min. Has it realy come to that?" Ya yi ƙwalƙwal da ido.

Jikin Amma a take ya yi sanyi. Taj ya yi wani É—an banzan murmushi a bayan idonta sannan ya cigaba da magana.

"Idan baki aminta da abin da nake so ba ai ina ganin ba sai kin tuna min cewa ni ba É—anki bane."

"Ba haka nake nufi ba. Kai ma ka sani."

Marairaice mata fuska ya yi sosai ta yadda ya san hankalinta zai tashi. Ya kuwa yi nasara don faÉ—an da ta É—auko da gaske sai ya koma laluma.

"Taj bana son kayi abin da zai zama ganganci. Bayan duk irin abubuwan da ka jure a baya kada wannan step ɗin ya bada ƙofar da za a yi maka dariya."

"Amma da Happiness mu ke komai. Mun yi survey na yadda malls su ke saurin dakushewa..."

"Durƙushewa dai ko?" Ta ci gyaransa ba tare da ta ɓoye takaicinta ba.

"Yeah, durƙushewa. So after the survey mun gano wasu reasons da suke kawo failure na business ɗin."

Zama tayi bayan ta gama sauraronsa tayi ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa take guje masa wanda idan ba É—an fito dasu tayi ba da wuya ya gane inda ta dosa.

"Shekararka nawa a ƙasar nan Taj?"

"10 years" ya amsa kai tsaye.

"And for those years you have been working non-stop kana tara kuɗi. Cikin ikon Allah kuma ka sami nasarar cin gasar nan ka sami maƙudan kuɗaɗe da sponsorship. Sai kawai na yarda da shawarar gina ƙaton mall irin wannan lokaci ɗaya da duka kuɗin? Kai baka hango ganganci a cikin yin haka ba?" Ta nuna zanen ƙayataccen ginin da yake kan laptop ɗinsa wanda nuna mata da ya yi ne ya kawo rigimar.

Marairaice fuska yayi "Tafiya ce ba kya so nayi ko Amma? Nayi miki alƙawarin zama har ki yi ritaya."

"Bani da son kan da zan yi amfani da gudun zaman kaɗaici na daƙile maka rayuwa."

Bakinta kawai ya kalla ya yi murmushi. Wata hausar idan ta É—auko duk nacinsa sai ya tsinci kansa da rashin ganewa. Laptop É—in ya rufe ya fuskanceta.

"Yanzu me kike so nayi?"

"Ka fara da restaurant É—in mana. Idan kaga riba sai ayi planning for expansion."

Tana gama magana ya sake buɗe laptop ɗin ya nuna mata sakamakon bincikensu. Tabbas akwai ƴan kasuwa da yawa a Kano. Tada ginin mall ba wani abu bane a wajensu. Kuma yana samun karɓuwa sosai. Ayi ta tururuwa ana zuwa. To amma fa bayan lokaci ƙanƙani yawanci da wuya ka sami motoci biyu sun ziyarci wurin. Wasu ma kayansu har ƙura su ke suna expiring saboda rashin zuwa. Da wannan su ka haɗa bayanai wurin yin abin da ya saɓawa wanda mutanen su ka saba dashi.

"Kinga na farko zamu yi shi a wurin da bai yi nisa da talaka da mai kuÉ—i ba."

Bata ce komai ba. Ya ƙura mata ido sai ta gyaɗa kai don ya cigaba.
Chapter 2 · 0% Book details