← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 96

Sashe 8

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huɗu suka kama hanya. Mama da Inna ba su san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj ɗin da su ka shiga bai ɗauka ba. Da tambaya su ka ƙarasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ƙudaje. Basu wani sha wahala ba su ka hango tebura huɗu na ƙasashen da su ka rage a gasar. A yau za a fitar da wani team ɗin sai ya rage uku. Washegari idan an yi na ƙarshe a fitar da na ɗaya, na biyu da na uku.

Cikin wata irin nutsuwa da tsantsar ƙwarewa Taj yake aiki. Shi da Wakili girkinsu cikin tsari yake kamar sun manta da lokacinsu na tafiya. Wannan nutsuwar ita tafi burge alƙalan gasar. Masu sauri saurin cimma lokaci kuwa daga kwano ya faɗi ya fashe sai ka ji su na washhh, mai ko ruwa mai zafi ya fallatso mu su saboda garaje.

Tunda Alhaji ya yi tozali da ɗan nasa wani abu mai masifar ɗaci ya sami wurin zama a maƙogaronsa. Taj yake gani sanyi da dogon wando baƙi da riga yellow mai tambarin makarantar sai apron fari tas ɗaure a ƙugunsa. APRON!?

Inna kuwa tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi. Tunda ta nunawa Mama shi bata sake iya cewa komai ba. Maman ce ma ta iya yin magana da ƙyar.

"Ahmad me idona yake gani?"

"Gasar girki ce" ya bata amsa a sanyaye.

"Ku zo mu koma." Alhaji ya ce da matansa "Kai kuma ka jira ya gama ka taho min da shi."

Ahmad ya so raka su amma ya nuna masa yawo a ƙasar da ba tasu ba, ba baƙon abu bane gare shi. Haka su ka tafi babu mai cewa komai. Da isarsu Alhaji ya ɗauko magungunansa na hawan jini ya watsa sannan ya ce kada wanda ya tashe shi sai Taj ya iso. Dama ɗaki uku ya kama musu. Sai su ka koma ɗayan.

Ido cike da ƙwalla Inna ta ce "Yaron nan so yake ya jaza mana tashin hankali ko me?"

Kallonta Mama tayi ta girgiza kai.

"Matsi da takura yaro bai fiye haifar da É—a mai ido ba. Taj ya yi masa biyayya an sami abin da ake so. Mene ne aibu don ya É—an waiwayi burinsa? Don fa mun haife su ba yana nufin dole su rayu kwatankwacin tamu rayuwar ko ra'ayi ba."

"Kayya dai Mama. Rayuwar yara sai da nuna hanya daga iyaye."

"Nima ban musa ba. Amma babu inda addini ya bawa iyaye damar tauye ƴaƴansu akan abin da bai saɓawa addinin ba. Baki ji malamai suna faɗin ko sakin aure indai ba bisa adalci ba, iyaye basu da hurumin tilasta shi ba? Girkin nan kuma maza nawa ke yi? Mene ne aibu a ciki tunda ba daudu yake ba?"

Inna dai duk a tsorace take ta ce "tunda mahaifinsa ba ya so sai ya haƙura ko don neman albarka."

Mama gani tayi cigaba da nunawa Inna illar takura tayi yawa ga É—a mai biyayya bata da amfani ba sai taga Innar ta kasa fahimta. Idan ta matsa kada abin ya yi kama da tana son sanya shi yin bore. Zaman jiran tsammani su ka yi har bayan Isha.

*
Sakamakon gasa yau dai da su Taj ya tashi. Cikin nasara da taimakon Allah su ne su ka yi na É—aya. Yawan makinsu idan an haÉ—a da na kwanakin baya ya basu damar iya yin na É—aya gobe in sun dage. Banda ihun murnar Æ´an Nigeria da su ke makarantar ba ka jin komai. Yanzu ya rage teams uku. Gobe za a fitar da na É—aya, biyu da uku. Da su ka fito za su tafi Wakili ya tare shi da godiya.

"Ban san a ina ka koyi girki wanda yasa talent É—inka ya zarce na kowa a nan ba. Your are truly amazing."

Taj ya yi murmushi "ai ban kai ka ba."

"Magana ta gaskiya ake yi. Idan muka yi nasara na san albarkacinka na ci. Saboda haka ina roƙonka don Allah gobe ka dage fiye da kullum. Samun karatun ya fiye min akan kuɗin da za a bawa na biyu ko na uku."

Murmushi Taj ya sake yi da alƙawarin in sha Allahu gobe zai yi bakin ƙoƙarinsa.

Da tallafin gwamnati Wakili ya sami tahowa karatu. Ya gama degree kamar Taj amma yana tsoron komawa gida yanzu. A ƙauye su ke. Gashi samun aiki yanzu ya koma wa ka sani, wa ya san ka. Tunda yana aiki a wani gidan abinci a nan yana samun abin turawa mamansa da ƙanne ba zai so ƙarewar visa yasa shi komawa gida a sake naɗe hannuwa ba.

*

Murnarsa ta koma ciki da Ahmad ya faÉ—a masa tare da su Alhaji su ka zo akan hanyarsu ta zuwa hotel É—in.

"Yaya don Allah kada ka sanar dashi zancen competition É—in nan."

Cije leɓe Ahmad ya yi wanda yasa Taj tambayarsa ko ya faɗa hankali a tashe.

"Tare mu ka shiga inda ku ke girkin. Ya riga ya gan ka."

Bayan karanto duk wata addu'a da ya sani ta neman sauƙi, bai sake cewa komai ba har su ka isa hotel ɗin. Kai tsaye ɗakin Alhaji su ka je su ka tarar da Inna da Mama a zaune jigum. Jikin Alhaji har ya soma tsananta saboda damuwar da ya sanya a ransa.

Wuri ya samu kusa da Mama ya zauna jikinsa a matuƙar sanyaye. Shiru yana jira a fara yi masa faɗa amma babu wanda ya yi magana. Cike da fargaba ya rarrafa gaban Alhaji kai a ƙasa.

"Don Allah..."

Tassss. Alhaji ya tsinke shi da marin da ya gigita shi. Inna tsam ta miƙe ta fice daga ɗakin don ba za ta juri gani ba. Ko da ta koma ɗaya ɗakin fashewa tayi da kukan da bata san na mene ne ba. Tana tausayin ɗanta. Tana kuma son ya sami damar cikar buri sannan kuma tana so ya yiwa mahaifinsa biyayya.

Sake ɗaga hannu Alhaji ya yi zai kuma marinsa cikin zafin nama Mama ta riƙe hannun da sauri.

"Ka dubi Girman Allah kayi haƙuri."

"Ki sakar min hannu" ya miƙe tsaye da fushin da yafi na farko yana mai fincike hannunsa.

"Haba Alhaji. Mene ne aibun girki a wurin namiji da har za ka kasa bawa yaron nan damar cikar burinsa."

"Buri? Buri fa ki ka ce A'i?" Ya nuna ƙirjinsa "ɗan cikina ki ke so na bari ya yi daudu?"

A hasale ta bashi amsa saboda har ga Allah tana ganin da gangan kawai yaƙi fahimta balle ya sassautawa ɗan.

"Mece ce alaƙar girki da daudanci? Maza nawa ka gani da wannan sana'ar kuma ba su lalace ba? Ka kyautata masa zato mana ka bi shi da addu'a."

"Ni ki ke É—agawa murya?"

Ko É—ar bata ji ba ta ce "Gorin haihuwar namijin za ka sake yi min?"

Ahmad ya fice kiran Inna. Taj kuma jin yadda rigima take son tasowa tuni ya dawo daga duniyar raÉ—aÉ—in marin da aka yi masa.

"Mama bashi haƙuri mu fita." Ya durƙusa a ƙasa "in sha Allahu nima ba zan sake tada maganar nan ba."

Hannun Mama ya ja su ka haÉ—u da Inna tana dawowa É—akin da jan ido. Ganin sun fito ita ma ta bi bayansu ita da Ahmad.

Kamar wancan lokacin yanzu ma nasiha game da mahimmancin yiwa iyaye biyayya su ka yi masa. Ya kuma karɓa hannu bibbiyu da zuciya ɗaya.

Ƙarfe goma da rabi na dare saƙon Wakili ya shigo wayarsa. Tuni akan fitowa da wuri ya soma yi masa. A ƙarshe kuma ya yi rubutu kamar haka.

"...My mum said we should keep reciting this Du'a tonight being friday night and tomorrow when the competition begins. RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FAQIR. I will continue to thank Allah for bringing you my way no matter the outcome. Working with a pro like you is truly an honour. Thank you Happy Taj."

Duk iya sata ta bacci daidai da sakan guda Taj bai runtsa ba. Shaf ya manta ba shi kaɗai bane a gasar har ya yiwa su Inna alƙawarin haƙura. Gashi daga cikin dokokin gasar duk wanda abokin girkinsa bai zo ba har aka fara da minti goma sha biyar sun zama disqualified. Anya zai iya samun kwanciyar hankali idan ya zama sanadiyar rugujewar rayuwar wani?

Kafin asuba babu irin tunanin mafitar da bai yi ba. Yana idar da sallah ya fice daga hostel zuwa hotel ɗin su Alhaji. Bai tsaya neman abin hawa ba saboda ƙarancinsu a wannan lokacin. Sannan babu wata tazarar azo a gani ma. Da gudu gudu ya isa yana faman haki. Kai tsaye ɗakin Ahmad ya fara zuwa. Da ba a buɗe ba ya durƙusa a bakin ƙofar yana mayar da numfashi.

Zaman kimanin minti shabiyar ya yi sannan Ahmad ya dawo.

"Lafiya me ya fito da kai da asussuba haka?"

"Alhaji yana É—akinsa? Ya tashi?" Taj ya tashi ya ma manta da gajiyar jikinsa.

Yanayinsa na rashin nutsuwa Ahmad ya fara dubawa kafin ya shige masa gaba zuwa ɗakin Alhajin. Shi kaɗai ne a ɗakin don matan nasa sun yi yaji saboda abin da ya faru jiya. Sanye yake da farar jallabiya yana fitar da daddaɗan ƙamshin turaren larabawa. Gemunsa mai sirkin fari-fari da baƙi ya ƙarawa fuskarsa kwarjini. Kamanninsa da samarin ƴaƴan nasa ta sake bayyana.

Gaishe shi Taj ya yi ya faɗi buƙatarsa kai tsaye. Ahmad na ji ya fita da sauri ya kira su Inna don su dakatar dashi kafin maganar ta lalace. Sun shigo daidai lokacin da Taj yake cewa,

"Ba don kaina nake son zuwa ba. Nayi maka alƙawarin ko na nawa mu ka yi ba zan karɓi komai daga gare su ba. Izini kawai nake nema kada rashin zuwana ya zama silar rushewar ...."

"Tajuddin!"

Durƙusawa ya yi duk da kiran sunan nasa ya kiɗima shi cikin ƙanƙan da kai ya shiga magiya kafin ma ya ji me Alhajin zai ce. Wannan ya ƙara tunzura mahaifin nasa sosai.
Chapter 8 · 0% Book details