← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 96

Sashe 85

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gaske...ba a taɓa cinye Taj da magana. Hankali kwance ya lauya zancen ya fitar da kansa.

Abincin da ba a ci ba kenan. ÆŠakinta ya rakata wanda yake da Æ´ar tazara da nashi ta shiga wanka shi kuma ya koma falo. Yana kwashe abincin nasu yana rausaya. A fridge ya ajiye komai inda ba za su lalace ba. Ya É—auki robar youghurt É—aya ya kai É—akin Hamdi da kofi sannan ya tafi nasa É—akin.

Youghurt ɗin ta fara sha tana mamakin yadda aka yi yunwar da take ji ta ɓace. Ta gama shirinta tsaf yadda aka yi mata huɗuba a gida. Sassanyan ƙamshi yana tashi koina a jikinta. Ta kawo hijabinta har ƙasa ta ɗora akan rigar baccin da ta saka mai santsi wadda ta tsaya mata a gwiwa.

Taj ma nutsuwa ya yi ya gama shirin bacci sannan ya taho É—akinta. Wani abu ne ya bashi mamaki da yana shiryawar har ya kashe masa dukkan karsashi da É—okinsa.

Da ya saka kaya ya fesa turaruka da body spray sosai amma sam bai ji ƙamshin ko guda ba. Ya ɗauki turaren ya kara a hancinsa amma har lokacin babu. Ya koma toilet ya đaga sabulunsa wanda yanzu da yana wanka yake sake yaba ƙamshinsa sai yaji yanzu baya jin komai.

Zuciyarsa wani irin harbawa tayi. Yaje ya buÉ—e fridge nan ma babu komai. Hankalinsa a tashe ya É—auki kwalin juice ya kafa kai don yana son jin sanyi a zuciyarsa. Sai dai me??? Harshensa kwata-kwata babu É—anÉ—ano.

Afuwan 🙏🙏🙏
Its late, I know.
RAYUWA DA GIƁI 32

Batul Mamman💖

This page is sponsored by NAFS-BEDDINGS (Nafisa Tofa 08034581454). A trusted and reliable plug for bedsheets and duvets. A trial is all it takes to get conviced. Ƴar uwa a yar da ɗan yagwalgwalin zanin gadon nan da ya gama tashi daga wanki ɗaya a sayi garanti!

*

Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daÉ—i. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daÉ—i ba? Idan sun haÉ—a ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaÉ—ai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun É—azu shi ne a ransa?

Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taɓa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a maƙera sai aka sameta a masaƙa. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu.

Muryarta a tausashe ta ce "Wani abu ne ya faru?"

"Me ki ka gani?" Taj ya faɗi yana miƙe ƙafafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaɗarta ya dawo da ita jikinsa.

"Babu komai tunda baka son faÉ—a min."

"Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai."

"Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sauƙi in sha Allah." Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faɗa ya san bata yarda ba ɗin.

Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ƙaƙƙarfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah.

Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ƙamshin ɗakin da na jikin Hamdi sun cika ƙofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah.

Shi dai tunda yaji wannan ƙamshin ya tashi da ƙarfinsa ya sungumi Hamdi yana faɗin Alhamdulillah.

"Wai don Allah me ya faru?"

Hancinsa ya É—ora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce "its nothing" ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaÉ—ai.

***

Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faÉ—awa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text É—insa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta

(Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.)

Bacci ɓarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faɗawa komai a hali na tashin hankali.

"Wallahi ba ya son ɓoye ɓoye. Goben nan ban san me zai yi min ba."

"Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faÉ—a da wuri."

Wannan magana ƙara dagula mata lissafi tayi. Washegari a daddafe ta jira ƙarfe bakwai da rabi tayi ta kama hanya ta tafi gida. Waya ta ɗauka ta kira Alhaji. Yayi mamakin sammakonta.

"Idan kina da aikin safe ne ki wuce Kubra sai na same ki a office idan na shirya."

"A'a Alhaji. Na san akan abin da kake nemana. Babu aikin da zan iya idan baka fahimceni ba."

Katseta yayi da ya gane me take nufi.
"Jira ni a É—akin Kamal."

"To Alhaji. Kayi haƙuri don Allah." Ta faɗi da rawar murya.

Ko amsata bai yi ba ya kashe wayarsa. Yaƙi jinin ƙumbiya ƙumbiya. Shi yasa yake jan su a jiki tun basu da wayo. Ko fensir wannan bai yarda wani ya zo ya ce wane na buƙata ba. Ya fi son ka je da kanka ka faɗa.

"Ban faÉ—a masa komai ba."
Kamal ya tabbatar mata da ta shiga É—akin.

"Nafi tunanin gaya min zai yi. Gara da na faÉ—a masa gaskiya a waya don ban san yadda zanyi na fidda kaina a gabansa ba."

Sai bayan kimanin minti sha biyar Alhaji ya shigo tare da Bishir da Abba. Kana ganinsu ka san basu san me yake faruwa ba. Sun dai kama bakinsu tunda sun san koma mene ne yanza za su ji. Ita dai Yaya Kubra tana haÉ—a ido da Alhaji ta sunkuyar da kai. Daga daren shekaranjiya zuwa yau ya faÉ—a. Dakakkiyar shadda ce a jikin shi ruwan toka. Babbar rigar a ninke Abba ya rataya a hannunsa. Kwarjini iya kwarjini sai Alh. Hayatu.

Da kakkausar murya ya ce mata "Kin kyauta."

"Alhaji don Allah..." ta fara cewa tana zamowa daga kan gado.

"Ya isa." Ya zauna a inda ta tashi. Yaran nasa su ka zagaye shi a ƙasa banda Kamal da ya hana motsawa daga kan kujera.

"Wace gudunmawa shirunki ya sama min?"

Iya bincikenta na ƴan uwansu na kurkusa (gidansu Alhaji da Hajiya) ta sanar dashi. Abin al'ajabi cikinsu babu mai blood group AB(-). Ana bikin Taj ta tura musu survey link na google form inda ta buƙaci su cike da cewar research (bincike) ne take yi da ya shafi aikinta. A ciki tayi tambayar da mutum sai ya saka sunan dangin da ya fito. Ta haka ta rarrabe kowa.

"An sami masu rhesus negative mutum huÉ—u."

Alhaji ranƙwafowa yayi kamar da haka ne zai ji me za ta ce sosai.

"Biyu ba za su iya yi masa amfani ba domin É—aya A ne, É—ayar kuma B."

"Ina jin ki Kubra."

"Masu O negative biyu da za su iya taimaka masa, ɗaya ɗiyar ƙanwar Hajiya ce."

"Mata suna iya bayarwa ne?" Alhaji ya tambayeta hankalinsa a tashe. Bishir da Abba su ka sake shiga duhu.

"Eh, amma...amma da wuya a samu nata. Widad ce. Yaranta biyu tana da cikin na uku" Yaya Kubra ta faÉ—i, ita ma kanta tana cikin jin ciwon hakan.

Kamal ya dube su. Irin wannan abin yake gudu.
"Alhaji don Allah..."

"Ka rufe bakinka Kamal" ya tsawatar masa. Ya juya ga Yaya Kubra "Sai wa kuma?"

"Ɗan Widad ɗin na farko mai shekara biyar. Yayi ƙanƙanta."

"Wai me ake buƙata ne Yaya Kubra?" Abba ya gaji da jin maganar da bai fahimta ba kuma yana ganin masu yinta cikin rashin nutsuwa.

"Ƙoda ce Abba. Duka ƙodojin Kamal ciwo ya cinye su." Alhaji ya bashi amsa da kansa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Abba da Bishir kuka su ka fashe dashi. Alhaji ko hanasu bai yi ba. Kowanne yana cewa a cire tashi. Da su ka ji ba da ka za a É—auka ba nan ma sun sake shiga tashin hankali. Kamal mai ciwon shi ya koma rarrashinsu.

"Amma fa ni ban gane ba. Me yasa masu A da B ba za su iya bashi ba, bayan kuma su ma É—in negative ne? Jiya fa nayi ta bincike Kubra. A da B duka donors ne." Cewar Alhaji da sanyin jiki.

"Haka ne Alhaji. Mai B É—in sickler ce."

Alhaji ya ce "Ita ma mace? Bana ma son a kai ga É—aukar na mace. A É—in fa?"

"Ɗan Kawu Sayyadi ne (ƙanin Hajiya). Shi kaɗai ne bayan mu nan wanda ya san da ciwon Kamal. Naje na same shi. Ban ko roƙa ba ya ce a shirye yake da aje a cire tasa. Shekaranjiya kafin naje wajen bikin test muka fara zuwa aka yi masa." Ta ja numfashi sannan ta ce "yana da Hepatitis."

"A taƙaice dai ...Ya Rabbi....Allah na" Alhaji ya danne ƙirjinsa da ya kama wani irin ciwo.
Chapter 85 · 0% Book details