Sashe 27
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lahhhh" Yaya ta faÉ—i tana jifanta da maficin hannunta "ni kike faÉ—awa haka ko mara kunya"
Hamdi ta fice da gudu suna dariya ita da Zee. ÆŠakinsu su ka koma su ka sami Sajida tana farinciki.
"Me ya faru?"
Rungume ƙannen nata tayi a tare "Safwan zai turo ranar asabar."
HaÉ—uwa su ka yi su uku suna tsallen murna. Yayinda Yaya take waya da Taj wanda yake cike da nishaÉ—in jin muryar Hamdi.
RAYUWA DA GIÆI 14
Batul Mamman💖
***
Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba kullum. Har ta haƙura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata ɗanɗanonsa idan ta haɗa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa'a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai.
"Yaya zan kai masa da kaina."
Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s
Sau ɗaya ta taɓa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huɗu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi taƙi jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler ɗin da ta sako meatpie ɗin mai hannu biyu ta kinkima ta ƙarasa.
Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ƙofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.
"Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi ɗiyarmu ce don ga kama nan. Ƴan mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da baƙi."
Gaban Hamdi ya yanke ya faɗi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caɓalɓala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da ɗaurin ƙirji. Kansa kuma ya yi ɗaurin ture ka ga tsiya da ɗankwali irin zanin.
'Me ya kawo ɗan daudu wajen nan?' Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ƙuncin rai.
Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ƙafafunta wani irin baƙinciki ya turnuƙeta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ƴan daudu sama da huɗu ne su ke ta karakaina wajen ɗaukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da taƙi jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna shaƙiyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.
*
Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. Ƴar Ficika ake kiransa saboda ƙanƙanta da ƙwarewa a iya shege. Duk wani mai ji da hayaƙinsa idan ya gamu da Ƴar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haɗawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ƙwarai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuɗi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haɗa abinci. Ƙaryar mutum ya ce ya taɓa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. Ƴar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo Ƴar Ficika ne ya biya masa rabin kuɗin jirgi.
Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haɗa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ƙarƙashinsa kaf babu ɗan daudu. Maza ne kawai masu ra'ayin girki a dalilin rashin wata sana'ar. To yau kwana uku kenan da Ƴar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ƙafa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haɗu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.
Abba bai ɓoye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. Ƴar Ficika yaji ya kwaɗaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ƙyama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buɗe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa.
"Ɗan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ƙoƙarina."
"Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran ɗin sai na karɓi wurin nan."
Abba bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin taƙaitaccen tarihin Ƴar Ficika da tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince.
"Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau."
Taj ya ce "haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya take."
Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaɗi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daɗi domin yau kasuwar ta buɗe fiye da kullum. Ya alaƙanta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wulaƙancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman wurin kafa sana'a da ya rasa wancan.
*
"Kai, kai, kai...Tabarakallah."
Hamdi ta waiga baya ta haɗa ido da wani ƙarmasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. Ƴar Ficika ya cigaba da murmushi yana kallonta.
"Wannan ma taka ce?"
Yaronsa da ta haÉ—u dashi a waje ne ya bada amsa.
"Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ƙamshi." Ya faɗi yana lanƙwaya hannu da juya idanu.
Wani irin ɗaci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ƙyar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da ya gabatar a matsayin abokan sana'arsa a Saudiyya.
"Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama É—aya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba."
"To" ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje.
Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta É—auka Abba girki da abubuwa na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu'amalanci mutane irin waÉ—annan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin É—an daudu.
"Hamdi"
Sarai taji kiran da yake mata amma ta ƙara sauri. Kafin ta ƙarasa titi ta dire coolar a gabanta ta ɗagawa wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faɗa ciki su ka yi gaba.
Abba ya kalleta ya juya ya kalli Ƴar Ficika da ya biyo shi.
"Ba dai ganinmu bane ya ɓata mata rai ba?"
Murmushi ya ƙaƙalo "ahh haba dai. Sauri take yi."
Ƴar Ficika ya murmusa "ko kai a gabana ka ƙarasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na saba gani?"
Cike da jin nauyi Abba ya faÉ—a masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da nasaba da tunaninta na komawarsa ga É—abi'ar baya.
"To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan É—in sai mu dawo?"
Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su Ƴar Ficika sai ya ce a'a. Yau kaɗai da ya haɗu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta aikin abin da su ka fi ƙwarewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau.
***
Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ƙyar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a ɓace.
"Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne. Yanzu duk wanda ya ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu."
Da laluma ya dubeta "Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe muka sami wannan rayuwar bayan haÉ—uwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so."
"Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ƙimarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi ɗa mai ido ba."
Ta sake faɗi cikin fushi. Duk yadda ya so ɓullo mata taƙi amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma. Yau dai ɗaya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba.
"A bar maganar nan. Indai Ƴar Ficika ne, ba zan kore shi ba."
"To ai shikenan. Allah Ya kyauta ɓacin rana."
***
Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi. Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba.