Sashe 43
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai ba ke ki ka ce kina son sa ba tun farko balle haƙuri ko rashinsa ya zama a hannunki." Hajja ta faɗi cikin fushi tana duban Anisa "har ni Jamila za ta yiwa haka? Maza kirawo min ita."
Cin mutumci babu irin wanda Hajja bata yiwa Amma ba. Da Daddy ya shigar mata shi ma ta haɗa dashi ta ƙare musu tas. Yau har gorin haihuwa biyu kacal sai da aka yi mata.
"Saboda shegen son kuɗi da koyi da rayuwar nasara ki ka tsayar da ƙwayayen haihuwarki. Gashi nan wanda ki ka ɗauko a dangin ya nuna miki shi ba ɗan goyo bane. Don na tabbata da sahalewar ubansa ya yi auren."
Allah Yasa ita ɗin ma ba ƙyalle bace. Da maganganun su ka isheta fita tayi daga ɗakin. Hajja ta ce dama ta rainasu daga ita har mijin. Banda haka bai kamata tana yi mata magana ta fita ba.
A wannan halin dai aka kwana ranar. Gidan duka babu daɗi. Anisa kanta ta sha kuka saboda ta dogara da cewa ko don alkunyar abin da gidansu su ka yiwa Taj, ba zai taɓa tsallake aurenta ba. Shi yasa da baya yi mata zancen soyayya bata wani damu ba. Aure ne dai za ayi kamar yadda Hajja ta alƙawarta mata.
Da safe ma gidan babu wata walwala. Kowa kai kawo yake kamar ana tura shi. Ga tafiya Kanon da Amma ta so yi Hajja ta hana Daddy yi mata izini.
*
Taxi Taj ya shiga har gidan. Maigadi ya riga ya san shi saboda haka ba a tsaya sanar da mutanen ciki ba ya buɗe masa gate. Agogo ya kalla da ya isa ƙofar shiga gidan. Goma da rabi ta ɗan wuce. Sanin ba Amma bace kaɗai a ciki dole ya sanar da zuwansa don ayi masa izinin shiga. Wayarta ya kira tana gani ta taɓe baki, ɓacin ranta ya dawo sabo. Har kiran ya katse bata ɗauka ba. Ya kira yafi sau shida kafin ta daure ta amsa.
"Ina jin ka." Ta ce a kausashe duk da wani ɓangare na zuciyarta yaji daɗi. Ta tabbata tana ransa tunda ya yi asubancin zuwa gareta.
Ya san za a rina. Ya kwantar da kai ya faɗa mata yana bakin ƙofa.
"Yau kuma gidan sirikinka ne da ba za ka shigo ba?"
"A'a, dama saboda naga safiya ce..."
"Bana son gulma. Shigo ina falona."
"Tuba nake Amma." Ya faɗi yana buɗe ƙofar.
Abin da ya guda ne ya faru. Anisa da ƙannenta duka ya samu a falon suna breakfast kowacce da kayan bacci. Ba abin ya koma ba ya riga ya sako kai. Ɗauke ido ya yi daga kallonsu ya yi musu sallama. Aka rasa mai amsawa don kishi su ke taya yayarsu, sai ita Anisan. Mai binta ta banka mata harara. Ƙaramar kuma ta ja dogon tsaki.
"Aikin banza."
Ko kallonsu bai yi ba ya wuce falon Amma. Uzurin ƙuruciya ya yi musu kawai. Kuma dai abin kunya ne ya biye musu. Yana ji suna ta tsaki. Ita kuma Anisa tana yi musu faɗan basu kyauta ba. Yana wucewa su ka yi rige rigen sanarwa Hajja da Anti zuwansa.
A zaune ya tarar da Amma. Ita ma ko wanka bata yi ba. Komai nata a hargitse saboda rashin kwanciyar hankali.
Jikinsa a sanyaye ya ajiye jakarsa a ƙasa ya zauna a gaban ƙafafunta.
"Don Girman Allah Amma ki yi haƙuri. Wallahi ba da gangan nayi ba."
Rai na ƙuna ta ce "Kayi ne saboda ka nuna min irin nawa matsayin a wajenka?"
"Ban isa ba wallahi. A gaggauce komai ya faru."
"Bayan ya faru É—in kuma sai ka manta sunan da ka sanya min a wayarka balle ka kira ko? Haba Taj. Aure fa kayi. Nayi zaton ina sahun gaba cikin waÉ—anda ya kamata su sani ko da wacce irin gaggawa ya zo maka."
Shi ma ya san bai kyauta ba. A daren da Alhaji ya yi masa izinin auren ya dace ya gaggauta kiranta. Sai gargaɗin Alhajin ya tsaya masa a rai. Shi ya hana shi faɗawa su Inna. Idan ya kira Amma ya tabbata sai ta faɗawa su Inna. Ita ɗin sam bata tsoron Alhaji. Akan Taj ma sai ta ƙure take yi masa magana. Gudun kada ta ɓallo masa ruwa yasa shi kama bakin nasa. Bai ƙara tunawa ba kuma sai bayan sun kama hanyar gida da Kamal. Duka wannan bayanin babu lallai ita ko wani ya đauke shi a matsayin uzuri. Kawai ya yarda bai kyauta ba, ya bata haƙuri shi ne mafi a'ala.
"Don Allah ki yafe min. Ki kuma saurari bayani na ko da ba zai gamsar dake ba."
"Baka da abin da za ka faɗa min Taj. Ka koma gaban iyayenka tunda dama na san burinka kenan. A nawa tunanin dai ko me zai faru ba za ka manta dani ba." Tayi maganar da ƙwalla a idanunta.
"Har yanzu Alhaji bai sakko ba. Su Hajiya ma basu san da auren ba sai bayan an ɗaura. Ke kuma gani nayi bai dace ba ace ta waya na fađa miki."
"Ban yi fushi ba. Ka dai koma Kanon tunda ka zama mijin aure. Allah Ya baku zaman lafiya." Ta miƙe.
"Amma ki yafe min mana don Allah."
"Ai nace raina bai ɓaci ba. In an tashi bikin ka daure dai ka faɗawa ƴan uwanka su Ihsan."
Da yaga dai rarrashin ba zai yiwu ba sai ya marairaice mata.
"Amma na baki haƙuri kin ƙi. Ina son yi miki bayanin yadda auren ya zo ma ba ki son ji. So ki ke dole ki nuna min ni ba ɗanki bane. Banda haka ai ko gudun kada auren yaƙi albarka za ki sassauta min." Hawaye yaga ta goge, ta kalle shi a raunane ya cigaba da magana "haihuwata ce fa kawai baki yi ba amma ina ji a jikina ko tsine min ki ka yi sai ta bi ni."
"Tsinuwar lafiya Taj? Kada na kuma jin wannan kalmar a bakinka."
Ya sake kwantar da murya "To ya kike so nayi? Fushinki ba zai barni naga hasken rayuwa ba."
"Allah Ya tsareka Taj. Zauna mu yi magana" ta ce a rikice. Bata son ganinsa a yanayi irin wannan ko kaÉ—an.
Daga bayansu su ka ji muryar Hajja da basu san tun yaushe take tsaye a bakin ƙofar ba tana cewa.
"Shegen baki kamar rainon cikin gari. Na rasa me yasa ba a taɓa cin galabarka a magana." Ta nuna Amma "ke kuma da ya soma kalallameki sai ki bada kai bori ya hau. Da ɗan cikinki ne ya yi min haka wallahi ba zan masa da sauƙi ba. Ɗan riƙo dama ai ba ɗan goyo ba. Kayan aro bai taɓa rufe katara."
Bayan Hajja ashe harda Anti da su Anisa. Daddy ne kaÉ—ai basu iya zuwa kai wa rahoton zuwan Taj ba.
'Duk zan iya da ku' Taj ya faɗi a ransa. Ya je bakin ƙofar ya riƙo hannun Hajja ya zo ya zaunar da ita.
"Na ɗauka ko me zai same ni a waje idan na shigo gidan nan Hajja zan sami kwanciyar hankali. A wurin ɗanki na sami baban da bai taɓa ƙyamar sana'ata ko goranta min don mahaifina ya kore ni ba."
"Shi ne ka kasa yi masa alfarmar auren Æ´arsa ba. Ko don ba Jamila ta haifeta ba?"
Taj ya girgiza kai "kinga inda matsalar take ko? Komai nayi sai kun fassara saboda baku É—aukeni É—a ba. Da ace Daddy ne ya haifeni hukunci kawai za ku yi min da faÉ—a akan laifina na. Ba sai anyi ta zancen asalina ba."
Duk fushin Hajja bata san lokacin da tayi murmushi ba "Tajo kenan. Wannan baki dai ba na ubanka bane. Shi banda haÉ—e rai bai iya komai."
"Baki taɓa zuwa bayan magariba bane. Da har dariyar Alhajinmu sai kin ji."
"Wa yaga tarangahoma. Dariyar Hayatu ai tsorata mutane za ta yi."
Taj ya yi murmushi "wallahi Hajja ke kaɗai za ki taɓa min tsohona in share saboda kin isa. Kaka na ɗauke ki ba surukar Amma ba."
Kwashewa tayi da dariya. Ta bar Anti da Amma da mamaki.
"Ɗan duniya. To ka gama kalallame mu. Sai ka faɗa min inda maganar ƙanwarka ta kwana tunda naji ance mahaifin amaryar ɗan daudu ne."
A take fuskarsa ta canja da furucin Hajja. Ta kalli Amma da mamakinta ya fi na Anti.
"Kada ku ce min baku san É—an daudu bane baban nata?"
Amma ta kalli Taj tana neman ƙarin bayani a tsorace.
Æoye É“oye dama can ba halinsa bane. Balle kuma yanzu da ya riga ya yi aure. In ya rufe yau anjima ko gobe magana za ta fito. Saboda haka a taÆ™aice ya labarta musu yana aiki da Abba da kuma abin da ya faru lokacin auren Sajida har zuwa jiyan.
"A taƙaice dai ba auren soyayya bane. Yarinya mai asali girɓatacce irin wannan dama sai dai auren alfarma." Cewar Anti.
Hajja kuwa cewa tayi "kakarta ce kawai ta yanke saƙa. Wannan kishi da ita ma ɓata lokaci ne Anisa. Kawai ki sa a ranki ke kaɗai ce."
"A'a fa Hajja" Taj ya katse musu hanzari kafin a kai matakin da zai faɗi baƙa.
"A'a me?"
"Ina sonta."
"Taj" Amma ta kira shi don ta san hali.
"Am serious Amma. Ina roƙonku don Allah kada a sake tada zancen mahaifinta ko yanayin auren. Nema nayi ba bani aka yi ba. Please" ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.
For once sai jikin Hajja ya yi sanyi. Magiya Taj yake amma irin wadda mai yinta yake fata da tsananin burin samun biyan buƙata.
Tashi Hajja tayi ba tare da tayi magana ba. Ta dai ƙarewa Taj kallo sai taji babu adalci idan ta cigaba da sanya shi a kwana.
"Ina É—an uwanka Kamalu"
Taj ya dubeta girarsa a cure "yana gida."
"Idan ka koma ka ce ina nemansa. Shi sai ya zo su daidaita da Anisa idan bashi da wata."
"Hajja!!!"
Anisa, Taj da Anti su ka kirata lokaci guda. Ta taɓe baki.
"Ku bar Hayatu da halinsa. Ban taɓa ganin wanda Allah Ya azurta da iyali masu kyakkyawar mu'amala da ɗabi'a kamar nasa ba. Shi yasa nake kwaɗayin haɗa zuri'a dashi ba wani abu ba."