← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 96

Sashe 49

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallo Kamal ya yi masa. Taj is just selfless akan duk abin da ya shafi Kamal. Abubuwan da ya yi masa iyayensu basu sani ba ba za su ƙirgu ba. Ciki harda bashi jarin da ya gina boutique ɗinnan. Ya rufa masa asiri a lokacin da Alhaji ya bashi miliyan goma yaja jari. Allah Ya haɗa shi da ƴan damfara su ka wanke shi. Abu kamar rufa ido. Ya shiga ƙuncin rashin sanin yadda zai tunkari Alhajin. Kawai sai Taj ya ce ya sayar da filinsa da su ka saya tun da daɗewa. Filin da Mama take jira a fara gini. Filayen biyu su ka kama miliyan shabiyar. Ko ƙwandala Taj bai karɓa ba duk yadda ya so hakan. Ya kuma so ayi rubutu idan ya samu zai biya nan ma Taj ya ce kyauta ce. Baya fatan har abada a sake tada zancen.

"Tashi mana"

Muryar Taj ta dawo dashi daga duniyar tunani. Miƙewa ya yi cikin dauriya ya ce masa mura ke son kama shi. Shi yasa yake zazzaɓin.

"Ni kuwa sai nake ganin kamar kana ɓoye min wani abu Happiness. Kwanakin nan kamar fa baka nan. Komai ni kaɗai nake yi."

"You are married Happy. Ya kamata mu fara rage wasu abubuwan. Da banyi tunanin ba sai da Abba ya ankarar dani."

Taj ya taɓe baki "yanzu zancen Mal. Sule har wani abin ɗauka ne?"

"Ai kuwa dai ya fi mu gaskiya. Nan gaba kaɗan sai kaji ana Malama hide my ID. Brother ɗin mijina kullum suna tare. Ko unguwa zamu sai ya kira ɗan uwansa. Bamu da wani lokaci irin na mata da miji saboda ya kankane komai. Don Allah a bani shawarar yadda zan ɓullo musu ba tare da mijin nawa yaji haushi ba."

Dariya sosai Taj ya yi.
"Kamal mai malaman ig. Wato har salon tura saƙon ka iya. Daɗinta dai ba Hamdi bace za ta yi wannan. Daga ji Doctor ce ta fara ƙorafi. Tell her I'll make myself scarce in kun yi aure. Ayi soyayya lafiya."

Daga nan sai zolayat juna. Kamal ya dage va zai je asibiti ba wai yunwa ma yake ji. Cikin Happy Taj su ka koma. Kamal ya yi odar shinkafa da gasasshen kifi. Kamar yadda Taj ya koyo, yawancin abincim Asia duk da hannu ake ci. Masu zuwa ko sun so gayu suna fara ci sai kaga an yi yadda yake a hoto da bidiyo da suke a lungu da saƙon wajen ana ci da hannu hankali kwance.

"Kawo masa kaza" Taj ya ce da waiter É—in.

"Ban gane ba. Ka dai sanni da kifi ko?"

Wani article Taj ya nuna masa sannan ya tura masa a waya. A ciki anyi bayanin yawancin abincin dake kawo allergy. Akwai gyaɗa da dangoginta. Kifi, kayan da aka sarrafa daga madara, ƙwai, kantu da kayan fulawa.

"Za ka daina cin duka. A hankali sai mu dinga gwada É—aya muna gani. Wanda a kansa reaction É—inka ya dawo kaga mun san shi ne. Nima zan daina ci don ma kada ka ce mugunta na shirya maka."

Yawun bakin Kamal ɗaukewa yayi. Ya shiga damuwa amma dole ya mayar da ita dariya. Sam baya jindaɗin ɓoye ɓoyen nan. Amma yanzu da zarar sun sani ƙarshen duk wani farinciki na gidansu ya ƙare. Baya son ya zama silar daina walwalar kowa akan lafiyar da kuɗi kawai ba za su iya saya masa ba.

Abincin da yake masa É—anÉ—anobda magani saboda rashin jindaÉ—in abin da yake yi ya dinga tutturawa harma yafi Taj ci.

***

Office ɗin an rubuta Dr. Kubra Hayatu a jiki. Wani private asibiti ne mai tashe na mata da yara da su ka buɗe ita da ƙawayenta biyu. Wurin yana samon mutane fiye da zato saboda ƙwarewar aikinsu musamman akan mata. Zaune take tana harhaɗa wasu takardu kafin ta fita don ta gama shift ɗinta taji bugu a bakin ƙofar. Umarnin shigowa ta bayar inda wani matashi ya shigo ya gaisheta. Ƙaramin kwali da aka yi wrapping ya miƙa mata.

"Ban sayi komai ba. Bana tsammanin delivery." Ta ce masa.

"Ance na wani Kamaluddeen Hayatu ne amma ke ake so ki fara gani."

"Wa ya aiko ka?" Ta tashi tsaye.

"Idan kin duba ciki za ki gane. A tashi lafiya"

Fita ya yi kafin ta sake yin magana. Ta É—auki kwalin taji babu nauyi sai É—an girma. Ta jijjiga taji abu kamar magani. BuÉ—ewa tayi da sauri sauri. Sunayen magungunan da hotunan dake jiki su ka sa ta kusa yanke jiki ta faÉ—i.

"Kamal? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

Waya ta ɗauka za ta kira Alhaji. Har ta shiga sai tayi saurin katse kiran. Duk yadda aka yi likitarsa ce ta turo saƙon. Kuma da alama hakan yana nufin tana son ganawa da ita domin tayi mata bayanin da ya dace. Kiran Alhajin ne ya biyo bayan nata. Ta ɗaga wayar a firgice.

"Doctor yaya? Haihuwar Nabila (ƙanwarta mai ciki) ce ta tashi?"

"A'a Alhaji. Kira nayi mu gaisa kuma sai network ya katse kiran."

Kwantar da hankali ya yi su ka taɓa hira sannan ta tashi. Kao tsaye asibitin da Kamal ya kwanta ta nufa. Aka sanar da ita Dr. Mubina sai litinin za ta zo. Nambar wayarta ta nema a reception ɗin aka sanar da ita bata ƙasar ne. Ta tafi Ghana amma ranar lahadi za ta dawo. Haka nan ta tafi cike da zulumi da fatan gaggawar zuwan litinin ɗin.

***

Wato ƴan gidan Alh. Hayatu gwanaye ne wajen son shagali. Duk abin da zai sa su taru a gida komai ƙanƙantarsa basa raina shi. Daga su har ƴaƴansu. To iyayen ma dai ba a barsu a baya ba.

Akan maganar zuwan Hamdi sai ka rantse bikin ne ya taso. Mama ce ta kira Yaya ta nemi izini tunda har yanzu a gida take. Bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta.

"Suna na Haj. A'i kuma Mama a gida."

"Allah Sarki Hajiya. Da fatan kuna lafiya."

Da jindaÉ—in yadda Yaya ta tarbeta Mama ta ce "Alhamdulillahi. Allah Yasa Taj ya yi muku É—an bayanin gidan namu."

"Sosai. Ya ce Hamdi surukarki ce ke da É—ayar maman tashi ta Abuja."

"Ƙwarai kuwa. To muna bada haƙuri tunda mace ita ya kamata a bi. Yanayin gidan namu ne Masha Allah. Muna da yawan da in muka zo za sai ƴan unguwa sun fara tunanin ko biki ake baki gayyace su ba."

Yaya ta kama dariya. Da alama barkwancinsu Taj ba a ƙasa su ka ɗauka ba.

"Allah da gaske. Shi yasa mu ka ce gara ta zo. Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba. Ai kin san wacce ce Inna a cikinmu ko?"

Yaya tayi murmushi "na gane."

Mama ma dariyar tayi "tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne. Ina fatan zuwan nata babu takura."

"Wace irin takura kuma ku da abar ikonku? In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu'a."

Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana. Taj zai É—aukota bayan azahar.

***

Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta taƙarƙare tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan Sajida.

"Allah ƙadiran ala mayyasha'u. Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin? Lallai Sajida rakiya tayo a gidan nan ga ƴar so nan kin saka a gaba" ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi "kema ƴar rakiyar ce ko za ayi miki?"

Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo. Hamdi da Zee su ka yi ta dariya. Da ƙyar Hamdi ta yarda ake yi mata. Wai cikin mutane za ta je. Bata son a rainata ta. Zee ma nata kwaɓin yana gefe. Ita kuma sai yau Baballe zai zo. Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren. Yaya ta ce gara a ga ƴaƴan nata a yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci. Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu.

Falon ya bita "dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira."

"Kankara kuma don Allah kamar wata faso?" Ta faÉ—i tana Æ´ar harararsa cikin wasa.

Ƴaƴan da irin wannan abu ba baƙonsu bane su ka tattara su ka barsu a falon. Zee ce taƙarasa mata ita kuma ta yiwa Zee ɗin.

"Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?" Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lulluɓin ƙaton zani kowacce ta zauna akan kujera.

"Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba. In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida gobe."

"Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce? Ni fa na rasa ma me zan ce. Haka kawai yanzu shige ds fice na sai in bin wani bayan a gidanmu nake" cewar Zee.

"Na ma manta da tambayar. Zan dai gwada. In na kasa in rubuta a text." Shawarar ta yiwa Zee. Ita ma a text É—in za ta rubuta.

Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya. Jinkirin fita na ɗaya daga cikin abubuwan dake saurin kawo saɓani tsakanin ma'aurata. Ita dai nata to ne. Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida. Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana son ji daga babbar yaya.

*

Biyu da kwata Taj ya iso. Ƙememe Kamal yaƙi rako shi. Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda shi a waje zai tsaya. Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi. Haka nan ya tafi yana mita. Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka.

Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama. Ya juya a hankali su ka yi sa'ar haɗa ido. Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa ɗinki irin na matasan zamani. Ruwan toka ne kamar kullum an ƙaranta adon. Very classy and elegant. Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi.
Chapter 49 · 0% Book details