← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 96

Sashe 82

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ƙwalawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta ɗauko a buɗe musu su gani.

"Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buɗe. Ƙamshin ne ya yi min daɗi na kasa barwa cikina" Amma ta faɗi da sauri.

"Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama É—aya" cewar Yaya tana kama guda É—aya "in sun je gidan yanzu ma buÉ—ewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran."

Da ƙyar su Hajiya su ka hanata buɗe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ƙal don daɗi. Duk da ana ta yaba ƙamshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waɗanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa.

Matar Halliru maƙobcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ƴar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru taƙi haƙura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karɓi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karɓi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka.

Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai ɓoyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faɗa sai ta kunna. Soyayyarta da ƙamshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam ɗinta kuwa abar duƙan ƙirji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wađanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane.

Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya.

***

Banɗaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini saƙo cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata.

Da ta É—auka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daÉ—in ji.

Da jindaɗi ya ce "Ƙarshen wannan ɗan daudun ya zo."

"A'a fa, ba É—an daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi É—an daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau.

"Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?"

"Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda.

Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaÉ—ai ya isheta dalilin mayar da kwaÉ—ayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan.

"Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na Æ´an kwanakin nan. Kin san na faÉ—a miki aikinsa a hankali yake ci."

"Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani."

"Sai ki san yadda za ki yi." Ya É—aga mata murya kamar wata Æ´arsa.

Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce "Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj É—in ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww"

Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki.
"Aikin banza. Ni za ka É—agawa mur..."

Haɗiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haɗa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama ɗaɗɗaga ƙafa.

"Fitsari, fito don Allah."

Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa.

Gaba na faɗuwa Siyama ta dakata a bakin ƙofa ta nemi mafita don kaɗan daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji.
"Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi yaƙi tafiya ba? Kada na shiga nayi gamo."

Ba kunya Ummi ta saki fuska harda ƴar dariya "shiga ki ganewa kanki" ta turata ciki. Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi ƙarfinta. Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji. Tabbas akwai manaƙisar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu. Hankalinta ya tashi. Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi.

Da zuwansu babu daɗewa ta nemi keɓewa da Iyaa. Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu laɓe. Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen. Wata maganar daban ta ɗauko har Iyaa za ta fara yi mata faɗan me yasa ta janyota akan shirme, sai ta ƙifta mata ido. Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta faɗi sunan Ummi iya leɓe. Wannan yasa ta fahimta.

"Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo? Ni fa ban taɓa zuwa ba."

"To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don É—auko Zee."

Murna ta kama yi harda rungume Iyaa. Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji.

"Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi."

Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gabaɗaya jikinta ya mutu. Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna. Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa. Haƙiƙa kowane ɗa da halinsa yake zuwa. Tarbiya bakin gwargwado sun bawa ƴaƴansu. Amma tun ƙananun shekaru tanƙwara Ummi ke wahalar dasu. Bata da bakin ɗorawa ƙawaye alhakin ɓata mata ƴa domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar waɗanda take mu'amala dasu. Ita ce boss mai sawa da hanawa. Ko dai kawo ƙara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu ƙarar ƴaƴansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta? Duk inda Ummi ta zauna sai tayi faɗa kuma ana bincike ita ce mara gaskiya. Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jindaɗi da Ummi bata taɓuwa. Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro. Kana cewa kule take ce maka asss. Wata maƙociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce

"Iyaan Baballe ki daina murna. Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu'ar kada su taɓa ɗan kowa. Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko wani naka bai zama silar ƙunci ko zubar hawaye ko jinin wani ba. Sannan kaima kada ɗan kowa ya yiwa naka. Ko babu komai akwai baki da ido kuma su ɗin gaskiya ne. Allah Ya kyauta."

Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba. Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai ƙara da a kai ƙararka. Za ta koyawa yaranta su ƙwaci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri. Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu.

Hawaye ya zubowa Iyaa. Ta É—auki laifin ta É—orawa kanta. Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin. To amma É—an wannan guntun sakacin da kuma halayyar fiÉ—rar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri.

"Allah na tuba. Allah Ka duba min."

Wata walwala da jindaÉ—inta duk sai su ka kau a lokacin. Ciwon kai ta É—orawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita.

*
"Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?"

A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga É—akin Kamal.

Son faɗawa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa faɗa a yau ba ƙaramin rashin adalci bane. Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau. In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi.

"Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba? Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari. Kifi na ci last kafin mu tafi."

"Subhanallahi. Kuma Alhamdulillah tunda an gano. We'll just avoid it don a zauna lafiya."

"We? Kai kuma me zai sa ka daina ci?" Kamal ya tambaye shi.

"Ai ka sanni da kirki. Ba zan so na dinga ci a gabanka ba."

Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda.

"Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida É—aya da Hamdi ba?"

"Akwai ƙura fa Happiness. Alhaji ya ɓallo min ruwa jiya." Ya faɗa masa abin da ya faru.

"TabÉ—ijam ake cewa ko cabÉ—ijan...yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?"

Bugu Taj ya kai masa ya goce "ta Allah ba taka ba. In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci."

"Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane." Kamal ya faÉ—i yana yi masa dariya.
Chapter 82 · 0% Book details