Sashe 68
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Leshi ne haɗaɗɗe mai laushi aka yi mata ɗinkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaɗai sun wadata ba sai an ɓata ɗinkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaɗan a jikin zare sai navy blue ɗin fulawoyi. Ta riƙo jar ƙaramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maɗauri. Ashokenta na ka da na kafaɗa navy blue da silver. Sai wata danƙareriyar sarƙa mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up ɗinta na hankali bata koma aljana a kwaba ba.
A tsakar gidan aka tsaya ana ta ɗauke ɗauken hotuna da ƴan uwa. Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo shi ɗauko musu amarya. Fitowar tasa ma sai da tayi da gaske. Anti Zahra tun safe ta bar gidan. Su na can gidan Alh. Lurwanu yayan Inna don a nan za ayi Kamun. Saboda ƙurewar lokaci basu iya samun event centre ba.
A waya ta faɗa masa cewa ana la'asar yaje ya ɗauko Hamdi. Hankalinsa a take ya tashi. Wato ƴan kwanakin nan da ya soma dawowa daidai babu abin da yake gudu kamar haɗuwa da amaryar tasa. Da wane baki zai bata haƙuri akan marin da ya yi mata? Inna bata ce masa komai akan asiri ba tunda Yaya Malam ya gargaɗeta da zargi. Gani yake girmansa ya gama zubewa a idanunta. Namiji mai dukan mata bashi da wata daraja a idonsa.
"Bari na faÉ—awa Happiness ya shirya mu tafi da wuri."
"Kai Happino. Nace happino" Amma tayi magana a fusace "É—auko matar auren naka ma sai da shi? Ince ko daren farkon ma tare za ku."
Da mamaki ya ce "Amma me ya yi zafi? Kamal nake nufi fa."
"Shi É—in fa! Ku yanzu sam baku iya lissafi da zurfin tunani. Dama me yasa ake haÉ—a angwaye da Æ´an rakiya? Ai saboda gudun fitinar zamani ne. Ku kuwa tunda an riga an É—aura aure me za ka yi da É—an rakiya?"
Dariya sosai ta bashi ya ce "to Allah Ya baki haƙuri. In kina so ma sai na ɗaukota na kai muku ita har kujerar da za ta zauna."
"Ɗan banza mai bakin tsiya. In baka yi wasa ba wallahi har wurin zaman sai in ce ka kawota mu ga ƙarshen rashin kunya."
"Cewa dai za ayi tarbiyarki ce." Ya ce da tsokana.
Ita ma da ta san hali bata san me ya sa ta biye masa ba. Rabuwa tayi da shi bayan ta tuna masa ƙarfe biyar daidai su ke son farawa.
Da ya faÉ—awa Kamal yadda su ka yi a wayar dariya su ka dinga yi son ransu. Kamal na cewa Happy ya girma shi kuma yana baya so.
"Ni wallahi kunyar haÉ—uwarmu ma nake ji."
"Hamdi fa bata da matsala. Kawai ka bata haƙuri a wuce wajen."
"Kaga last faÉ—anmu kuwa da na kai mata kati? Tana faÉ—a ina yi kamar wasu kaji. I am seriously ashamed og myself." Ya rufe fuska da tafukan hannayensa.
"Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau É—innan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu."
Taj ya gyaÉ—a kai "Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness."
Kamal murmushin yaƙe kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita.
"Wani sabon salon wulaƙanci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karɓo daga wajen tela?"
"Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?"
"Kaina ciwo yake Happy. Bani da ƙarfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita."
Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal É—in. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waÉ—ancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a'a. Gajiya ce.
Taj na fita ya kira Mubina ya faɗa mata jikinsa fa babu daɗi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ƙanwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ƙanwar ta ta tace mata patient gareta.
Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ƙarfi har ya dawo daidai.
"Ban faɗawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata. Idan bata faɗa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi."
Ranta a ɓace yake. Kamal ya yi mata murmushi.
"Wannan faÉ—an duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?"
Harara ya samu "Wasa ma ka mayar da abin?"
"Sorry Doc." Ya É—auko wayarsa dake gefen gadon "zo mu yi hoto."
Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ƙoƙarin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya ɗauketa wasu. Bai taɓa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa haƙuri ya yi ya ce da ita,
"A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?"
Abin control ɗin gudun ruwan da take ƙara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ƙarfen gabaɗaya saboda yadda zancen ya taɓa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi
"A'a."
"Ni? Ni?" Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya "nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daÉ—i."
"Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare alaƙar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree."
"Na nawa kuma? Ba kin faÉ—awa Yaya Kubra ba?"
"Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faÉ—a? Magani ta gani ta zo tayi tambaya."
Kallonta kawai yake yi yana jin inama ƙalau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita.
"To da ace ni É—in patient ne mai bada haÉ—in kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?"
Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa "Da gudu" sai kuma ta soma hawaye "please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka É—ora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah."
Tana gama faɗin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sauƙi. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati ɗaya da kan shi zai faɗawa iyayensa.
*
Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faÉ—a musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faÉ—uwa.
A hankali yake tuƙi cikin nutsuwa. Ƙamshin da take yi ya kwance duk wani notin arziƙi na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata haƙuri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa?
Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da ɗaga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ƙalau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa?
Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen Æ´an bori ta dire don murna.
Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir.
(Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ƙulle tamau kamar yarinya tana koyon ɗaurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ƙarshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.)
Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da ɓaro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. Ɗan duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ƙara volume. Can sai cewa yayi
"Nagode Allah ni dai ƙalau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu."
Shiru tayi tana ƙifta idanu. Gara yayi mata waƙoƙinsa akan wannan magana.
Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaÉ—i da nutsuwa yake ji a ransa.
"Ko kina da shi in saya miki..."
"Innalillahi..." ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluɓin.
Numfashi ya ja da ƙarfi da su ka haɗa ido. Tayi masa kyau ba kaɗan ba.
"Ni lafiyata ƙalau wallahi."
A daidai lokacin mai maganin ta zaɓi ɗora zancenta da dawowa kan mata.
(Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waÉ—anda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.)
Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya damƙe shi yana murzawa a hankali.
"Don Allah ka canja."
"Shhh...an zo wajen naku. Bari mu ji."
"A ji me?" Ta tambaye shi looking horrified.
(Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ƙaiƙayin...)
Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka.
"Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka."
"Allah Ya baki haƙuri. Daga taimako?"
"Ba na so." Ta turo baki.
Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ƙaramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faɗa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faɗa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus.