← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 96

Sashe 15

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rayuwa babu abin da yafi tashin hankali kamar a samu wani ya san sirri a kanka wanda baka so a sani. Kuma in anyi rashin sa'a ya dinga amfani da wannan damar wurin cusgunawa rayuwarka. A shekara shidan da Hamdi tayi a makarantar nan bata taɓa shiga matsanancin hali ba sai da Ummi ta fara blackmailing ɗinta. A jiya da abu ya fito fili waɗanda su ka sami ganin bidiyon nan su ka labartawa waɗanda basu gani ba, sai taji zuciyarta wasai. Abin ya matuƙar bata mamaki. Tayi zaton in an sani an tsokaneta za ta iya yin kuka. Sai gashi babu wanda ya tunkareta tunda aka ga abin da ta yiwa Ummi da kuma maganar da ta yaɓawa wata Metiron bayan ta dawo ɗaki.

Da yake wasu manyan hankalinsu a ƙwauri yake, matar a gaban mutane ta tambayeta.

"Hamdiyya da gaske ne babanki É—an daudu ne?"

A fusace ta amsa da "Eh, amma yafi uban wasu da yake zaman prison."

Matar tayi matuƙar mamaki domin kuwa ba kowa ne ma ya san cewa mijinta yana prison ba saboda sata. Laƙwas tayi don babu halin sake magana saboda ƴan kallo sun sami sabon abin tattaunawa.

Ƙarfe goma aka aiko kiransu. Tana zuwa ta sami Ummi tayi kneel down a gaban teburin Principal. Ga Baba Maje zaune akan kujera. Yana ganinta ya saki fuska sosai yana magana da Principal ɗin.

"Yauwa ita ce kuwa."

Principal ta dube shi da É—an sakin fuska don taga sam bai fahimci zancen ba ta ce "Nima ita nake nufi Alh. Maje. Wannan Hamdiyyan ce dai su ka yi faÉ—a da Ummi jiya su ka yi sanadin hargitsa makarantar nan."

"Na gane bayanin naki Hajiya. Dama abin da nake son fahimtar dake shi ne ina ganin ɗaya daga cikinsu ce ta shigar wa ƴar uwarta. Ba wai a junansu su ka yi faɗan ba." Ya yi mata bayani dalla dalla a ƙoƙarinsa na son ta gane.

Murmushi tayi masa don yanzu bata jin za su fahimci komai sai yaran sun yi magana.

"Ko me yasa ka yi wannan tunanin?"

Ƴar dariya ya yi gami da gyara hannun rigarsa "mahaifin Hamdiyya abokina ne tun kafin a haifesu kin gansu nan. Shi yasa nake tunanin ko karewa juna suka yi. Ba kuma wai goyon bayansu nake ba. In sun yiwa makaranta laifi zan bada goyon baya ɗari bisa ɗari a hukunta su."

Abin da ya fađa ya bawa Principal ɗin mamaki sai dai bata ce komai ba sakamakon sallamar sakatarenta da mutane biyu. Ɗaya wani ƙosasshen Alhaji ne ya sha babbar riga yana fama da kayan tumbi. Ɗayan kuwa Abban Hamdi ne. Su na shigowa VP da wasu manya cikin malaman su ka shigo su ma.

Abba na ganin Baba Maje ya ce "da na san za ka zo ai da nayi zamana a gida."

"Ko kuma da ni na zauna ba."

Dariya su ka yi sannan aka yi musabaha tsakanin duka mazan wajen.

Murya da yanayin mahaifin Hamdi kaɗai yasa malaman kallon kallo a junansu. Principal ta buƙaci a buɗe zaman da addu'a sannan ta ɗauko wayar Ummi ta miƙa mata.

"BuÉ—e min wayar nan don na sami labarin ita ta fara janyo rigimar."

Kai Alhaji mai É—an tumbi wato Uncle B da baka gane Baba Maje ba tunda Ummin bata kama dashi sai ya kama faÉ—an bogi.

"Ban hanaki zuwa da waya makaranta ba? Ke kenan kullum rigima ta tashi sunanki ne a sahun gaba."

Baba Maje buÉ—e baki yayi don maganar ba tsoro ta bashi ba illa ruÉ—a masa tunani. VP na ganin haka sai ya taso har inda yake ya ja shi waje.

"Duk abin da za ka ji ko ka gani kada kace komai don Allah har ka gama fahimtar inda zancen ya dosa."

"To amma..."

"Mu koma ciki. Komai zai warware kansa."

Haƙuri ya bawa Principal na katse su sannan su ka jira Ummi ta buɗe wayar da rawar hannu. Jikinta babu inda baya ɓari. So take tayi aljanun ƙaryan tun yanzu amma bata da ƙwarin gwiwar pretending. Hamdi da bata san badaƙalar dake kwance ba kuwa ko a jikinta. Jikin kujerar da Abba ke zaune ta raɓa tayi kneel down abinta.

"Kunna min abin da ki ka kunnawa É—alibai a jiya."

Nan fa É—aya. Kasa kunnawa tayi. Displine master ya daka mata tsawa amma ko gezau.

"Kin cika umarnin da aka baki ko sai na tashi?"

Muryar Baba Maje ta fito da kaushi. Uncle B duk ya zata malami ne da ake tsoro shi yasa bai ji komai ba da yaga ta cika umarni da rawar jiki.

Ofishin karaÉ—ewa yayi da muryar Abba. Kunya tayi masifar kama shi. Idanunsa su ka yi jawur lokaci guda. Hamdi taji wani irin tausayinsa wanda yasa ta kuka. Baba Maje ya rasa me yake yi masa daÉ—i.

Principal ta miƙawa kowa wayar ya gani da idonsa sannan ta umarci Hamdi da tayi magana. Ba tare da coge ba ta faɗi abin da ya faru tun ranar da su Baba Maje su ka zo gidansu har abin da ya faru jiyan. Irin cin zarafin da Ummi ke yi mata da takura kawai don ta mallaki sirrin mahaifinta. Kallon takaici kala kala ya dinga sauka akan Ummin bayan ra gama magana.

"Ummi haka aka yi? A ina ki ka sami bidiyon?" Uncle B ya tambayeta har yana kai hannu zai ɗaga haɓarta domin kanta a ƙasa yake tana zubar da zafafan ƙwallar tsanar Hamdi.

"Wai kai ɗin uban waye a makarantar nan da za ka taɓa baligar mace?" Baba Maje ya tambaye shi a harzuƙe bayan ya doke masa hannu.

"Kai zan yi wa wannan tambayar." Ya kalli Principal É—in "ya kamata malamanki su san aikinsu in ba haka ba zan cireta daga makarantar nan."

Baba Maje ya ce "Kai a wa?"

"Ni a mariƙinta" Uncle B ya bada amsa kai tsaye.

VP gaban kujera ya dawo don yaga an zo inda yake jira. Cikin zafin rai kuwa Baba Maje ya É—ago Ummi tsaye ya dubeta.

"Kalli ƙwayar idona ki faɗa min waye wannan."

Numfashi ta fara ja tana shirin yin suman ƙarya taji Baban nata ya yi mata wata irin wawiyar jijjiga. Muryarsa tana rawa har wajen office ɗin kuma ana ji ya ce,

"Idan ki ka ce za ki yi min ƙaryarku ta ɗalibai zan sabauta miki halitta a wajen nan. Ki faɗa min waye shi."

"Saurayi na ne."

Tasss, tass, tas ya É—auketa da wasu gigitattun maruka. Abba ya yi saurin finciketa daga hannunsa ya tsaya a tsakani.

"Haba Maje..."

"Matsa min Habibu." Ya furta yana huci.

Uncle B na ganin haka ya tashi zai sulale ya gudu sai dai babu dama. VP ya sanya securities ɗin makaranta a bakin ƙofa. Hasashen haka zai iya faruwa tun a jiya yasa ya ɗauki matakin da ya dace.

Da ƙyar da suɗin goshi aka samu Baba Maje ya zauna. Abba ya dubi Principal ɗin ya yi magana.

"Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓarnar da yaran nan su ka janyo muku. Ummi tayi kuskure sannan ita ma Hamdi tayi na ɗaukar doka a hannunta. Amma fa duka abin da ya faru laifina ne..." ya sunkuyar da kansa.

Principal ta kalle shi da tausayawa "bari na ɗan ce wani abu a nan." Ta kalli Hamdi "mu iyayenku da ku ke gani muma haifarmu aka yi ba da wayo muka zo duniya ba. Shekarunmu na hawa ne muna daɗa hankali. Duk wani kuskure da kuke yi a yanzu muma mun yi ƙila ma fiye da haka a lokacin tamu ƙuruciyar. Yanzu mun girma mun san illar abin shi ne dalilin da yake sa muke muku faɗa ma idan kun yi. Abin nufi a nan shi ne ƙuruciya da raunin hankali a baya yasa mahaifinki yin kuskuren bin rayuwar da kowa yake ƙyama. Gashi ita aba ce da ko ka daina da wahala đabi'unta su barka ɗari bisa ɗari. Amma tunda Allah Ya baki shi a uba ki rungume kayanki da godiya. Da baki ji kunya kin ɓoye shi ba, babu wanda ya isa ya ɗaga miki hankali akan shi. Ki nuna godiyarki ga Allah ta hanyar appreciating ɗin duk abin da Ya baki."

GyaÉ—a kai tayi tana goge hawaye "Abba don Allah ka yafe min."

Da ƴar muryarsa ya ce "Allah Ya yi miki albarka Hamdiyya. Ki bawa iyayenki na makaranta haƙuri su ma."

Ta kuwa bi umarninsa ta bawa kowa haƙurin abin da su ka yi jiya. Cike da kunya da jin nauyi Baba Maje ya bawa Abba haƙuri.

Abba ya yi murmushi "Don Allah ka bar wannan zance."

"Ta yaya zan bari? Bayan shekara sama da ashirin da rabuwarmu ace Æ´ar cikina ce tayi maka irin wannan tozarcin?"

"Magana ni dai ta wuce don Allah." Abba ya sake maimaitawa.

VP ya ce "yallaɓai ina ganin sanin alaƙar Ummi da mutumin nan shi ne abu mafi mahimmanci yanzu tunda an kashe wancan case ɗin."

A lokacin aka fito da file na fitinannun makaranta inda sunan Ummi ya bayyana a kowanne term tun zuwanta a JS3. Bata fara laifin da ta cancanci a kira iyaye ba sai a SS2 da ta zama cikakkiyar senior. Kuma a lokacin ne duk sanda aka buƙaci iyayenta sai wannan mutumi dake zazzare idanu ya zo a matsayin kawunta. Ita ma aka bata dama ta faɗi yadda suke biyan maigadi su haura katanga ita da wasu. Samarinsu su kai su gari a shaƙata a sha ice cream da su shawarma a dawo. A rantsuwarta dai ta ce babu abin da ya taɓa haɗasu na fasiƙanci. Baba Maje kasa jurar jin maganganun ya yi ya finciki bulalar hannun wani malami ya shiga lafta mata. Da taron dangi aka raba shi da bulalar

"Kanki ki ka cuta Ummi. Nan duka ɗaliban da ki ka zalinta in basu yafe ba sai kin gani a ƙwaryarki."

Fuskarta yaɓe yaɓe da majina da hawaye ta ce "Baba ka yafe min."

"Ba dole na ba? Idan nayi miki baki rayuwarki ai sai tafi haka lalacewa. Ki tashi ki haÉ—o kayanki don kin gama karatu kenan."

"Alhaji ba ayi haka ba." Principal ta sa baki "ka bari mu É—auki matakin da ya dace."

"Maje kada ka É—auki hukunci cikin fushi."

"Kun san Allah ɗaya ne ko? To wallahi yarinyar nan ta gama karatu a ƙarƙashin ikona."
Chapter 15 · 0% Book details