← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 96

Sashe 4

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Inna Batulu ta dawo ta sanar da ita sai da tayi kuka. Shi yasa ba a son zama unguwa É—aya da wanda ake ganin zai iya jan ra'ayin yaran unguwa. Daga yawan aikensa siyan abinci a wurin wasu Æ´an daudu dake bakin titi ita dai bata san yadda aka yi ya dinga rikiÉ—ewa ya koma wannan Habibun na gabansu ba.

Ranar anyi masa faÉ—a sosai. Baba ya zage ya yi masa dukan mutuwa. Garin Allah na wayewa aka neme shi aka rasa. Wurin wata uku ana nema kafin daga bisani su sami labarin ya tafi Saudiya da wani ubangidansa. Sana'ar abinci su ke yi a can É—in.

Akwai abubuwa da kan sami bawa ya rasa silarsu. Ka haifi ɗa kayi masa duk iyakar ƙoƙari amma idan ƙaddara ta faɗa masa kana ji kana gani zai zaɓi hanyar ta bata ɓullewa. Irin haka ta sami Habibun Inna Batulu. Dangi su ka sanyo su a gaba da yawan magana da famin ciwo. Wasu in sun sami zuwa ƙasa mai tsarki a unguwar su yi ta kawo labaran yadda aka ganshi ya ɗashe saboda shafe shafe. Zantuka barkatai harda wanda ya ce wai an faɗa masa ya yi aure da wani ɗan daudu irinsa.

Zancen da ya tayar da hankalin Baba fiye da kowanne kenan. Ya sayar da gonarsa da wani gidan haya ya haÉ—a kuÉ—i a shekarar ya tafi Hajji. Bai wani sha wahala ba aka sada shi da gidan da Simagade yake haya da abokan sana'arsa. Lokacin shekararsa tara baya gida. Jinjin ta gama sakandire har ta fara sana'ar kitso a gida tunda aure ya gagara. Ta kai matakin da kowane iri tana son samu saboda yadda mahaifinta ke jifanta da maganganu idan taje gida.

Baba fashewa yayi da kuka da yaga ɗan nasa sanye da jallabiya ya ɗora zani da ɗankwali. Ga haƙoran Makka har biyu. Tamkar ba a Jidda ba suna ta ƙazaman zage zage shi da wani da suke faɗa. Ganin mahaifinsa ne ya sagar masa da gwiwa ya yi shiru. Sai hankalin kowa ya kai kan tsohon dake zubar da hawaye.

"Shiga ka sako kaya ka zo ka rakani masallaci."

Ba Habibu ba hatta abokan zamansa duk jikkuna sun yi sanyi. Ya shiga ciki ya samo aron wasu pakistan na maza ya saka. Ya fito tafiyar nan babu dama ne. Masallaci mafi kusa Baba ya shiga dashi. Ya umarce shi da yin sallah raka'a biyu sannan ya fuskance shi bayan sun idar.

"Saboda ka taka dokar Allah Habibu yau alwala da sallarka ma in ni nake karɓa ba za su bar rufin masallacin nan ba zan jeho maka kayarka."

Kai ya sunkuyar cike da kunyar kansa.

"Daga wannan rana ba zan sake yi maka faɗa ko nasiha ba. Zan kuma roƙi Batulu da kada mu sake zubar da hawaye a kanka. Na barka da duniyar da ka zaɓa wadda nan da kwanaki kaɗan za ta daina yayinka. Idan tayi maka rawar ƴan mata ina jin za ka yi hankali har ma kayi tunanin dawowa gida. In na mutu tun yanzu ka sani na yafe maka. In kana da rabon shiriya ka zo gida kafin baƙincikinka yayi ajalin mahaifiyarka."

Yana gama faÉ—in haka ya tashi. Habibu zai bi shi ya ce baya so. Haka ya koma ya gama kwanakin da su ka rage ya dawo gida. Habibu kuwa komai ya daina yi masa daÉ—i. Nadama mai raÉ—aÉ—i ta shiga É—awainiya dashi. Ana gama kwaso mahajjata ya tattara komatsansa ya dawo gida.

Bai fi wata biyu ba Baba ya kama cuta har ya cika. Yayi kuka kuwa kamar ba gobe. A gefe guda yana godiya ga Allah da Ys bashi damar dawowa. Tun daga lokacin ya soma neman gyara rayuwarsa. Sai dai kuma jama'a da dama suna gagarar yiwa mai laifi uzuri ko ya tuba. Da yake har yanzu in ba jallabiyar nan ya saka ba sai yaji kamar yayi tsirara, amma yana bakin ƙoƙarinsa wurin yin abin maza. Matsalar dai an bar kari tun ran tubani. Murya ta gama shaƙewa. Karairaya ta zame masa jiki duk da ya rage. Ya yi ta neman aikin yi ya rasa. In ya kasa kayan sayarwa irinsu kayan miya babu mai saye. Har wurin Hayatu yaje amma yaƙi taimaka masa ya zama yaron shago kamar yadda ya nema. Allah Ya ɗora masa ƙyamar ƴan daudu sosai.

Da ya rasa yadda zai yi ne ya roƙi Inna Batulu ta yarje masa tafiya Lagos sayar da abinci. Ya tabbata a can da babu wanda ya san shi kuma girki ba a ɗauke shi sana'ar mata kaɗai ba zai sami sauƙi.

"Idan ka tafi Habibu ina jin tsoron kada ka koma ruwa. Gashi nayi imanin babu mai baka mata ka aura a halin da kake ciki." Ta goge hawaye.

"Ki yafe min Inna. Na san na cuci kaina amma nayi miki alƙawarin ba zan komawa waccan rayuwa ba."

Duk zancensu a kunnen Jinjin. Kafin tafiyarsu ta sake jin maganar ana yi tsakaninsa da ƴan uwansu. Ta kula Inna tana cikin damuwa. Barinsa babu abin yi matsala ne. Sannan zuwansa shi kaɗai akwai haɗari. Bayan dogon nazari irin na yarinta ta nemi izinin zuwa gida ta shawarta da mahaifiyarta. Luba ƴar halak ko mijinta bata bi ta kansa ba ta sako ƴarta a gaba su ka taho Kano. A gaban ƴaƴan gidan da mahaifiyarsu ta ce ga amana ta sake damƙa musu.

"Jinjin miskiniya ce na sani. Ban sani ba ko bawa Habibu ita zai zama gwaninta ko abin ɓacin rai a gareku."

"Allah Ya kiyaye Gwaggo Luba" cewar yayar Habibu tana taya Inna Batulu kuka don ta kasa magana.

Sun yiwa uwa da ƴar godiya kamar su ari baki. A wata guda aka yi komai aka gama su ka koma Lagos da zama. Rayuwar ta fara daɗi Allah Ya karɓi ran Innarsa. Shi ne dalilin dawowarsu kuma ya kasa komawa.

Habibu yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Yafi kowa sanin akwai lokutan da basa son nuna shi. Shiyasa ya kan kame daga zaƙe musu don kada ya ɓata rawarsa da tsalle. Matarsa Jinjin kuwa duk duniya baya haɗata da komai. Shi ya sani cewa tayi masa alfarmar da da ace ana auren ƙanwa ko ya nasa ba za su taɓa aurensa yana ɗan daudu ba.

**

Alh. Hayatu Sule Maitakalmi mashahurin ɗan kasuwa ne a Kantin Kwari. Takalma dai na mata da maza daga shagunansa an gama magana. Karansa ya kai tsaiko a kasuwanci. Sunansa ya zaga duk inda ya dace a dama da shi. Mutumin cikin ƙwaryar Kano ne daga unguwar Soron ɗinki. Yana da kirki da ƙoƙarin cicciɓa na ƙasa da shi sai dai akwai tsatstsauran ra'ayi kuma baya tanƙwaruwa. Duk wanda ya san shi ya san kaifi ɗaya ne kamar bakin wuƙa.

Matansa huɗu kuma duk a gida ɗaya suke. Ƙaton gini ne na masu kuɗin da wanda yake yawan shan gyara domin ya tadda zamani. Ainihin gidan akwai ƙaton falo wanda in an shiga da ƙofofi huɗu a jere a ɓangaren dama. Kowacce in ka shiga falo ne babba da banɗaki da kuma ɗakuna biyu. Nan me ɗakunan matansa. Bangon dake kallon ɗakunan kuwa kitchen ne makeke da store sai ɗakin masu aiki dake haɗe da banɗaki. A jikin bangon tsakiya ne da matattakalar bene inda ɗakin maigidan yake da falonsa. Sai kuma ɗakuna biyu na ƴan mata suma kowanne da banɗaki duk a saman. Sai an fita daga bayan ainihin ginin ne kuma za a tarar da ɓangaren samari. Ta gaba kuma aka jona ginin falo da banɗaki inda yake ganawa da baƙinsa. Duka gidan ƴaƴa ashirin da takwas ne kuma a ciki biyar ne kaɗai maza. Sai ƴaƴan ƴan uwa da yake riƙo da ƙannensa. Shi yasa kullum gidan yake a cike.

Uwargidansa ta lalle Haj. Gambo da ake kira Hajiya kaɗai tana da goma. Ta biyun Mama A'i tana da uku. Sai Umma Jamila mai takwas. Sannan amarya Inna Abu mai shida. Ya taɓa sakin mace ɗaya wadda ta kasance ta uku a jerin aurensa. Ɗa ɗaya ta haifa kuma shi ne babban namiji a gidan mai suna Ahmad. Da fitina ta zo shi kuma ba zai lamunta ba. Tun yana lallaɓawa da yaga za ta wargaza masa tsari ya sallameta ya bawa Mama ɗan. Tun daga lokacin babu wadda ta sake gigin tayar masa da hankali. Zaman lafiya ake da ƙullewar zumunci. Har ta kai idan mace ta haihu wani zubin ɗan cikinta ma sai ya yi mata ƙyuya saboda kulawar da yake samu a wajen yayyensa da sauran matan. Irin rayuwar nan ta daga ni sai ƴaƴana bata da muhalli kwatakwata a gidan Alh. Hayatu.

Bayan Ahmad an ɗauki lokaci kafin a sake samun ɗa namiji. Don a haihuwa ta tara Hajiya ta haifi Kamaluddin. Yana da wata biyar Inna ta haifi Tajuddin. Bayansa tayi mata biyu sannan ta ƙara da maza biyu Sulaiman (Abba) da Bishir sai ta rufe da mace kuma autar gidan. Wannan yasa mazan su ka tashi a ƙarƙashin yayunsu mata tunda sun zo a sahun ƙarshe ƙarshe.

Kamal da Taj sun tashi tamkar ƴan biyu sakamakon rashin tazarar haihuwarsu. Wasu har basa gane su don hatta pant duk mai sayawa ɗaya za ta sai wa ɗayan. Bambancinsu da aka fi ganewa shi ne doguwar fuskar Taj da gashin fulanin Kamal wanda su ka gado daga uwayensu. Da yake jinin Alhajin akwai ƙarfi duk inda ƴaƴansa su ke basa ɓoyuwa. Musamman da cikakkiyar girarsu da ta zama wani sirri na ƙarin kyawunsu. Mama uwar riƙon Ahmad ita ce maman mazan gidan. Duk abin da ya shafesu ita ce a kai tun ana goyonsu. Ita take yayesu shikenan yaro ya koma ɗakinta.
Chapter 4 · 0% Book details