Sashe 50
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa cikin ɗinkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar ɗaurin aure. Riga da siket ne mai adon ja da shuɗi mara turowa ne a jiki sai baƙi. Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin wannan. Light make up. Komai cikin tsari babu hayaniya. Tayi ɗaurinta a karkace kaɗan ta ɗora shuɗin mayafi daga rabin ɗanƙwalin. Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a ɗaya. Ɗayan kuma agogo ne na silver.
"Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?" Yaya ta ce da taga kallon yaƙi ƙarewa. Taj ya ma manta inda yake da alama. Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take.
Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu. Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfalaƙi. Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai. A idonta dai jeep ce tunda tana da tudu. Fara ƙal da tambarin BMW a jiki.
Buɗe mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai. Gilasan masu duhu ta kalla ta ƙara jin wannan tsoron. Ƙamshin daɗin da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake. Taj na zama a mazaunin direba ta kama kanta. Ɗan waigen ƙauyancin ya ƙare. Ya tada motar ya kunna AC sannan ya fara ribas.
"ÆŠan tsaya."
Hamdi ta faɗi tana ɗora hannu a ƙirji.
Burki ya taka da hanzari "Me ya same ki?"
Idanunta har sun tara ƙwalla ta ce "Gabana ke faɗuwa wallahi."
"Saboda me? HaÉ—uwa da Æ´an gidanmu?"
Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi.
Yana son honesty É—inta. Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce
"Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?"
Tana jindaÉ—in yadda yake girmama mahaifinta sosai. Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi "na sani ko ka fara yau. Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje."
"Ƴar ƙauye zan ce miki ko matsoraciya? Amfanin wannan tint ɗin ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji ya kamata..." ɗauke ido ya yi daga titi su ka kalli juna.
"Ya kamata me?"
"Will you let me kiss you idan mun dawo? Ko yanzu in sami wurin parking?"
"Ya Taj???" Idanunta su ka firfito.
"Na'am. Ashe kin san suna na. Na zata Salman Khan za ki ce. Har na tanadi waƙarsa da zan miki." Ya yi maganar yana dariya.
Bakin tsiwa ya mutu murus. Ya É—an kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo. Shi da ya tsammaci ta bashi amsa.
"Hamdi? Yaya? Zazzaɓin ne yau ma?"
"Uhmm" ta gyaÉ—a kai harda shafa wuya da goshi.
"Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai."
"Allah da gaske nake. Jikina babu ƙwari ma." Ta ɗaga hannu ta sake shi yaraf.
"Kinga mun kusa zuwa gidan. Ki rufa min asiri yanzu don za ki haÉ—u da Æ´an jarida masu tambayar tsiya. Akwai Æ´an bugun ciki ma waÉ—anda za ki iya faÉ—a musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba."
A tsorace ta ce "da gaske?"
"Da wasa" ya furta a hankali yana yi mata murmushi.
A bakin gate ɗin wani ƙaton gida taga sun tsaya. Ya ɗaga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso.
Tsoron nan bai barta ba ta ce "ba za ka shiga ba?"
"Alhaji bai yi min izini ba." Ya amsa mata da murya mai rauni.
Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka.
"Kada ki ɓata min kwalliyar nan tun kafin na biya kuɗinta don Allah."
"Ni ba don kai nayi ba" ta ce da tsiwar nan.
"Mala'iku suna jin ki dai."
Da sauri ta ce "Astagfirullah."
Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi. Hannunta mafi kusa dashi ya kama ya sarƙe yatsun ya lanƙwashe su.
"Wa ki ka yiwa kwalliyar? Suna ji dai kada ki manta."
Tsuke baki tayi tana jin yadda É—umin hannunsa ke shigarta. Ita kam ta shiga uku. Wannan aure ta son ya É—ore....Allah na tuba ta faÉ—i a zuci.
"Hamdi?" Ya É—an matsa hannun.
"Kai na yiwa" murmushi ya soma yi ta ƙara da cewa "amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi."
"Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki..."
Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki.
"Kaga fa Ya Kamal ya fito." Ta kalli gate É—in a firgice.
Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya riƙe shi da ɗaya hannun.
"Idan ya ƙaraso sai na ce ya tayani roƙonki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long."
Kamal har ya ƙaraso. Ƙwanƙwasa gilas ya yi ta ɓangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas ɗin ƙasa.
"Happiness taƙi yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita."
Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake riƙewa.
Kamal dariya yayi kawai "Mrs Happy haka za mu yi dake?"
"Shi za ka zaɓa?"
"Da me kike tunani? Ya zaɓeki a kaina?"
"Naga wai ni ce ƙarama" tayi kicin kicin da fuska.
A take Kamal ya canja sheƙa.
"Happy buÉ—e mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can."
"To wallahi tayi alƙawari a gabanka" Taj ya sha kunu da ya yi maganar.
"Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira."
"Nayi." Ta faÉ—a don idanun Æ´an uwan su biyu sun hanata sakat.
Sama Taj ya yi da gilas É—in ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya.
"Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan an ɓata miki rai ki fara faɗa min kafin su Abba. Zan baki haƙuri a madadin ko waye. Kin ji?"
Murmushi tayi har zuci. Ta É—an matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita.
Kamal na buÉ—e gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana.
"Ya Kamal basu iso bane?"
Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata amarya.
"Salwa? Saukar yaushe?" Ya ce babu wani jindaÉ—i a tare da tambayar.
"ÆŠazun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo gaishe da su Hajiya."
"Gata ku gaisa." Ya faɗi yana kallon yadda shigarta gabaɗaya ta saɓawa sanin da ya yi mata a baya.
"Sannu amarya." Ta ce tana yin gaba "bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito."
Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ta fita. Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta.
RAYUWA DA GIÆI 22
Batul Mamman💖
This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409.
Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu.
Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai ga Firdaus. Ƴar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi.
"Anti Hamdiyya Habib Umar" ta kirata da ƙarfi cikin murna.
Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ƙarya. Ƙaruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta.
"Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki É—ebo ba. Uncle Taj is my favourite."
Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri.
"Ke matsa min. Ƙanwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita."
"To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me..." wata ƙanwarsu ta janyeta "sannu da zuwa Sis"
"Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?" Umma tayi magana daga ƙofar ɗakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa "Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?"
Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ƙasa. Akayi akayi sam taƙi komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri'ar Abba Habibu ta ɓace ɓat.