← Book details Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 106

Sashe 36

Mijin Malama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana" Ita ka
ai take magana ita ka
ai kuma take fahimtar me take cewa.

Ya shafa la
anta da suke jajir ya ce "Mami ni ma irin naki"
Ta yi murmushi tana
aukar shi tare ta
ora a cinyarta ta ce "Until you grow up" Ya shiga buga
afa da yarfe hannu shi a dole sai la
ansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce
"Ok Shafi ka
an, da safe sai koma red" Ya yi murmushi yana tsalle ya
ora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta
auke shi tana dungure masa kai,
ara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya.

Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki.

Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani.

Wani irin kuka take da dukkan
arfinta wanda yake tasowa tun daga
asan zuciyarta.

Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai.

Da
yar ta rarrashe shi suka kwanta bacci.

Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son ta
a jikinsa ta ji ko da zafi.

Wayam!

Ta bu
e idanu taga babu Little a kan gadon ta mi
e da sauri idanunta ya sauka akan
ofar
akinta dake bu
e bayan har rufewa ta yi.

Da sauri ta ce "My Son, Little?....

Paid book
MIJIN MALAMA
08119237616
Sosai Majeederh ke kuka kamar ranta zai fita har da shasshe
a Mami dake tsaye ta ri
e ha
a ta dubi Majeederh ta ce "Yanzu ke kina Ina yaron ya zare sakata ya yi nasa waje" Ta kasa cewa komai sai kuka gaba
aya hankalinta ya ta shi ta zama kamar
aramar yarinya.

Mami ta
ara tafa hannu ta ce "Yaro ne mai shegen karambanin tsiya, ko gidan uwar wa ya sani wanne hannu zai fa
a ohho, ga yadda
an mafiya da
an kidnaping su ka yi yawa a gari" Majeederh ta
ara rushewa da kuka ta ce "Little ba zai ta
a bu
ofa ya fita ba, ina yaga tsayin?" Aaliyyah ta ce
"Kuma ko ya iya bu
ofar
akin ki Anti Jeederh ai ba zai iya bu
ofar waje ba" Abbu wanda ya fito da shirin fita Masallaci ya gyara muryar kowa ya shiga hankalinsa kamar sun ga mala'ika ya dube su
aya bayan
aya kafin ya ce "Lafiya?" Ruma ce ta ce "Abbu wai Little ne ba a gani ba" Ya yi jim alamar tunani kana ya kalli Majeederh dake fuskarta ta yi jajur a cikin wutar lantarkin dake gidan.

"Hawwa'u garin ya ya?" Jikinta na rawa ta ce "Abbu wallahi ban sani ba, tare muka kwanta sai da ya yi bacci na yi, yanzu na farka nayi raka'atul fjr na ga babu shi" Ta goge hawayen fuskarta wasu na sake zubuwa ta ce "Na rufe
ofa, amma na ganta a bu
e" Ya dubeta sosai yana nufar waje ya ce "Allah ya bayyana shi, akwai ban mmki?

Wani ya shigo?

Wani ya bu
e masa
ofar?

Ko fita ya yi da kansa?" Ruma ta
aga kafa
a tare da shigewa
akin da suke kwana su uku, ita, Raihana, Aaliyyah.

"Abbu zan je duba shi?" Da sauri ya ce
"Ina?" Kanta a
asa tana shasshe
a ta ce "Waje, maybe yana waje ko police please Abbu"
....

Bada yawona ba
Cewar Abbu.

Ta marairaice fuska ta ce "Ka tausaya mini, bashi da kowa" Cikin tsawa ya ce "Ki fita daga idanuna Hawwa'u, ke bakya tausayin kan ki sai yaron da baki san waye ba?

Kin san wanne kallo ake miki a unguwa?

Wasu tunaninsu
anki ne kawai kike
oyewa, to wahainiyarki ta kiyaye ramata, nan da waje kika fita dalilin neman yaron nan ban yafe ba, ina akan shi kika
i zuwa kar
o form wato kin girma kin manta wahalar dana sha akan ki, har ki ka yi growing zuwa yanzu?

Idan kika je Misira yanzu kin san irin matsayin da zaki taka?

Ni za Hawwa'u ni mahaifinki?" Ya
are maganar yana nuna kansa da yardarshi.

Majeederh ta zube gaban Abbu akan gwiwoyinta hawayenta ya tsaya zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ta kasa tantance wanne kalar yanayi take ciki.

Ta ri
afafuwan Abbu ta ce"Na tuba Abbu, na tuba na bi Allah na bika Mahaifina ka yafe mini zan zama yadda ka ke so, zan yi karatu zan je matakin da kake bu
ata ka yafe mini Abbu don Allah?" Aaliyyah kukan tausayin yayarta Majeederh ya kamata ta dur
oshe a wajan tana kuka sosai.

Abbu ya
an sassauta murya ya ce "Ki je anjima zan kira ki, amma ki cire maganar yaron nan a ranki" A karon farko a iyakacin rayuwarta da za ta yi wa Abbu magiya ta ce "Abbu please...

Little.,"
"This is noises!"
"Ka yi ha
uri" Jikinta duk rawa yake kamar ba babbar
ar daya haifa ba ta yi cikin
akinta.

Sosai Raihana ta ji tausayin Anti Jeederh amma babu yadda ta iya, ta ja bakinta ta yi shiru.

Mami ma
akinta ta yi tana
aukan hijabi domin daman da alwala a tare da ita.

Aaliyah ta mi
e bayan ta ci kuka ta
oshi sosai ta nifi
akin Majeederh.

A zaune ta sameta bakin gado ta sanya hannunta a tsakanin cinyoyinta tana ka
awa a hankali kanta sunkuye.

Jiki ba
wari cikin muryar kuka sosai Aaliyyah ta ce "Anti Jeederh mene haka?

Me yake shirin faruwa?

Me ya sa sai ke kawai?Anya Abbu shi ne Ubanmu?

Wannan abun it's too much, this is not fair zuciyata ta fara raya mini bashi ne Ubanmu ba ko Uncle.....," Kau!

Majeederh ta
auke Aaliyyah da wani kyakkyawan mari har sai da ta yi baya daga tsugunen take.

Ta fashe da kuka sosai ta ce "Anti Jeederh ki dakeni son ranki, beat me amma ba zai iya sauya tunanin da zuciyata ta fara wanzar mini da shi ba, na bu
e idanu da soyayyar da kike mini Anti Jeederh, na fahimci kece madadin uwa a gareni ko da baki shaida mini Mami ba ita ta haifemu ba, Innati ta fa
a mini komai, amma kullum kina nuna mini hanzar tsira hanzar da zan kare kai na a matsayina na
iya mace, na tashi naga yadda Abbu ke son ki ya fifita ki da kowa, komai Hawwa'u musamman
angaren karatu, Anti Jeederh baki da lokacin kan ki kullum karatu kullum karatu, mene nufin Abbu?

Imran ya zo neman aurenki ya ce ba aure zai miki yanzu ba, ya yi masa korar kare, yanzu kuma ya amshi ku
in auren Ruma bayan kece babba kece ya kamata ki fara yin aure kafin ita..." Kuka ya ci
arfin Aaliyyah ta ce "Soyayyar kenan?

Za a ci karatu ne?

Idan bai barki kin yi aure ba yanzu sai yaushe, Anti Jeederh tun kina jss 3 na ji kina fa
awa Yaya Latifa aure kike so, idan ya tilasta miki yin karatu ya hanaki aure shin ya miki adalci?

Mufa
a ajjiye ce, amana ce a wajan iyayenmu za a tambaye su yadda suka kula damu, Malaminmu ya fa
a mini duk
iya macen da ta ce ayi mata aure bata son karatu mafi alheri shi ne a aurar da ita, domin ita tasan me take ji,mene ya sanya ta ce tana son auren, idan ba a aurar da ita ba komai yana iya faruwa da ita kuma...." Majeederh ta yi saurin toshe bakin Aaliyyah tare da rungume yarinyar a jikinta ta ce "Enough, enough is a enough, ok"
Kukan zuci take wanda ya fi komai cin rai da sanya damuwa da ciwo a zuciya, bata son hawayenta ya zuba gudun
arawa Aaliyyah nata kukan da damuwa.

Sun jima a haka tana jin Aaliyyah na kuka tana bubbuga bayanta a hankali har ta fara sauke ajjiyar zuciya kafin ta
agota tana ri
e fuskarta murmushin dole bayyane a fuskarta ta ce "Stop crying my dear, hannunka baya ta
a ru
ewa ka yanke ka yar, Abbu yana so na, soyayya ce ta sanya ya yi haka, kuma yana da iko kaina, yana ganin kuma karatu ya dace dani ba aure ba, shi ne mahaifinmu our own father, biological father ok ba a ta
a sauya tuwo suna, kuma idan na yi karatu zan samu aiki Abbu zai ji da
i i most be proud, zai alfahari da ni, zan gyara mana gida, na siya masa mota, na kaisa Makka na bu
e masa wajan aiki ya fita daga halin talaucin da yake ciki" Da sauri Aaliyyah ta ce "Aure fa?"
"Zan yi, idan da rabo" Ganin zata sake magana Majeederh ta ha
e fuska sosai ta ce "Je sallah, kiyiwa Fulani addu'ar samun rahama a kabarinta, kiyiwa Abbu addu'a da su Ruma da Mami" Ta ce "Anti Jeederh ke ma zan miki addu'ar Allah ya kawo miki mijin aure ko gobe ne" Majeederh bata ce komai ba, a ranta tana jin cewa karatu zata aura shine zai zame mata miji da zuri'a.

Bayan fitar Aaliyyah kuka taci ta
oshi son ranta, kukan ya dace da ita
ilan hakan zai sanyaya mata zuciyarta daga yadda take ji, idan ta tuna babu Little bata san kuma inda zata same shi ba, bata san wanne hannu zai fa
a ba zai samu kula ko ba zai samu ba sai zuciyarta ta karaya damuwarta ta
aro fiye da ko yaushe.

Ga Abbu ya yi mata katangar
arfe tsakaninta da nemo Little
inta.

Tunaninta ya tsaya ta rasa me za ta yi, rashin Little tamkar rasa wani gefe ne na rayuwarta.

Ganin lokaci na tafiya ya sa ta mi
e tare da shiga ban
aki yau ko wankan da take da asuba domin kiyaye jikinta daga mafarkan da take yi bata samu zarafin yi ba, ta
aura alwala tare da shimfi
a ladduma ta yi sallah raka'a biyu.
Chapter 36 · 0% Book details