← Book details Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 114

Sashe 71

Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse take fitowa daga kitchen din zuwa falon,shi ta soma hangowa a gefan anni wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba wadda bata taba jin irinta ba,bata sani ba ko hakan yana da nasaba da abinda ya faru dazun?,fuskarshi fes,kyansa ya sake fitowa sosai,ganin yana niyyar juyowa ya sanyata dauke kai da sauri ta maida kan anni,dubanta yake sanda take tahowa din,sai yaga kamar an canza ta gaba daya,shidai yasan ba wannan ayshan ya tafi ya bari ba wata ce daban,abinda tayi dazun ya dawo mishi,sai yace da anni sanda ta iso wajen tana aje kwanukan
"Yaushe humaira ta koma haka?" Yayi subutar bakin fada ba tare daya shirya ba,sam anni bata fahimci tambayar tashi ba,tayi tunanin kyau da gogewar data qara yake nufi,saita saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,miqewa tayi tana cewa
"Sannu takwara,ki kai masa saman teburi,fita zanyi nima dubiya,drivan ma har ya iso" ta qarasa maganar tana miqewa,sai ya dubeta
"Ba hira kenan anni,kamar ma baki kewata ba?"
"Ni bance haka ba saikai khalipha?,watanka nawa?" Ya gane qorafi takeson yi masa,mafi a'ala kuma yayi shuru kar allura ta tono garma
"A dawo lafiya"
"Allah yasa,ya kamata idan ka huta kaima kaje ka dubashi,don yanzun ma tare dasu haidar zamu je"shuru kawai yayi yadan sadda kanshi,da alama baison zuwa wajen amma bazai iya musa mata ba,miqewa aysha tayi ta amshi jakar hannunta ta bita da ita a baya,suna zuwa qofar falon ta amsa
"bar aikin da ba lada kije kiyi na lada,ki kula da mijinki" kunya kaman zata nutse,kalmar saita mata banbarakwai,ba wanda ya fado mata a ranta a lokacin sai maman hunaifa da baban hunaifa,saita dinga jin girma da wani alfahari na shigarta kadan kadan,wai itama fa matar wani ce akwai igiya a kanta,hakanan taji tana son ta gwada yanda matan aure keyi,juyawa tayi zuwa cikin falon,har ta isa kanshi na qasa da alama tunani ma yake,bata tankashi ba ta kwashe kwanukan zuwa saman tebur wanda motsinta yasanyashi daga kai,saiya tsinci kanshi da binta da kallo,qamshinta daya buso zuwa hancinsa yaji ya burgeshi,ci gaba yayi da kallonta ba tare data sani ba yana jin qimarta na qaruwa cikin ranshi,zaman da sukayi da anni kafin fitowarta labarinta kaf duka kan ayshanne,irin kulawar data samu daga gunta ya tabbata ko shine iyakar abinda zai mata kenan,sai yaji tausayinta ya kamashi,lallai mahaifiyarta batasan baiwar da Allah yayi ma rayuwarta ba na samun nutsatstsiyar diya.

Sai data shirya komai sannan ta daga kai da niyyar duban me yake,sai suka hada ido,murmushi ya sakar mata saboda harga Allah bazai iya boye jin dadin kulawa da anni data yi ba,tamkar an dorawa zuciyarta wani abu haka taji,bugun zuciyarta ya sake yawa,idanunta ta lumshe tana qoqarin maida masa martanin murmushin nasa,sai kuma taji kunya ta mata dabaibayi,yanayin daya ganta da abinda ta masa dazu suka fado mata,ji take kaman qasa ta tsage mata ta shige ciki,a nutse ya taso har zuwa inda take tsaye,yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna,saita motsa kadan ta matsa daga kusa dashi.

Ganin shuru batayi niyyar zuba komai.ba bayan shi kuma yunwa yakeji sai ya sanya hannunshi da niyyar bude flask din dake gabanshi,tare hannunsu yaje kai saboda arashin tunanin budewar da akayi yazo daya a qwaqwalensu,da sauri kowanne ya janye hannunshi,khalipha ya dunqule nasa hannun yana jin wani irin abu na masa tafiyar tsutsa a jikinsa
"Uhmmm,a sanmin naci" ya fada qasa qasa ganin taqi ta sake motsawa,sai da tayi qoqarin controlling hannunta dake rawa sannan ta iya zuba masa komai ta miqa masa
"Ka dawo lafiya ya hanya?" Ta fada cikin amfani da irin salon maman hunaifa,wanda ba qaramin kyau yayi mata ba fiye da tunaninta
"Alhamdulillah" ya amsa yana sauke ajiyar zuciya,sai tayi niyyar wucewa,ba haka yakeso ba,hakanan yaji bai gaji da ganinta ba awajen,kwalliyarta ta tsaru,sosai adon yabi jikinta
"Zama zakiyi naji me kika bayan bani nan" ya fada yana kai lomar farko bakinsa,saiya kasa ci gaba da maganar da yayi niyya,dadin abincin na kai masa ko ina,hakanan ta zauna a kujerar da ya nuna mata wadda itake facing dinsa,kanta na qasa shi kuma yaci gaba da cin abincinsa
"A ina kika koyi girki haka?"
"A gida" ta amsa masa a ataqaice
"Tun yaushe?"
"Can da dewa" daga haka bai sake cewa komai ba,yayin da sautin muryarsa daya tambayeta da ita taci gaba da amsa kuwwa a kunnenta,sai take jin kamar ba muryarsa ba,komai nashi ya sauya.

Shiru ne ya ratsa wajen,baka jin komai sai qarar cokalinsa da kuma hayaniyar masu aiki dake can cikin kitchen,daga wata kusurwa ta falon kuma amal ce rakabe tana duban abinda ke faruwa ta bayan labule,agogo yayi niyyar kalla sai ya hangi gefan skert dinta da batasan ya fito ba,qaramin murmushi ya saki cikin ransa yake cewa
"Barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba,lallai hali jini yake bi" a hankali ya sauke idanunsa kan hannunta da take wasa da farcan hannunta da yasha jan lallenta ya koma marroon,tafin hannunsa ya dora a hankali samansu ya damqesu kadan yadda ba zataji zafi ba,da hanzari ta daga kai ta dubeshi don sanin dalilin faruwar hakan,murmushin dake shimfide saman fuskarshi saiya qarasa narkar da ita,qwayar idanunta kawai ya kalla yasan tambaya takesoyi
"Amal" ya furta kamar mai rada ta yadda idan ba ita din dake wajen ba bawanda zai iya jiyo me yake cewa
"Amal kuma?" Ta tambayeshi cikin mamaki,kai ya gyada
"Banason ki dinga nuna rashin sabo ko baqunta tsakanina dake" maganarshi ta dawo mata randa take da kwana guda a gidan,kai ta gyada masa alamun ta fahimta,qoqarin dai daita kanta tayi ya dubeta
"Bani labari dame dame ya faru bayan bani nan" ya qarashe maganar yana miqewa a nutse tare da nufar inda ya hangi amal,aysha ta bishi da kallo a sace tana ganin kaman ya qaro salo da yanga,kominshi shima ya sake sauyawa.
39
Tamkar mai neman wani abu yaje wajen,yayi kaman zai juyo ya take qafarta,wata iriyar azaba ta ziyarceta,sai ta saka hannu ta rufe bakinta dashi tana tunanin zata iya jurewa,sake taketa yayi wannan karon kasa daurewa tayi sai data qwalla qara,baya yaja ya dage labulen yana dubanta
"Me kikeyi a nan?" Tsabar azaba ya hanata magana,sai daya maimaita maganarsa cikin tsawa sannan ta iya amsashi
"Babu komai,abu nake nema...." Tsai yayi ya zuba mata rikitattun idanunta dake sake tsumata cikin soyayyarshi koda yaushe,nauyi sukai mata ta gaza daukarsu,saita sadda kai gabanta na faduwa,kunyar abinda tayi na mamayarta,da kanta ta tona kanta ta hanyar cewa
"Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba"
"Daga yau duk sanda muke zaune a falon nan mu biyu kacal ko gilmawarki kar na sake gani,bacemin a gun" ba shiri ta wuce tana dingisa qafarta.

Dariya ce sosai ta zowa aysha,ta kifa kanta a saman tebur tana qunsheta,a nutse ya tako wajen,sai yaja ya tsaya yana dubanta,sam batasan ya dawo ba sai dataji yace
"You,me kike ma dariya?" Ya dage girarshi daya,kai ta girgiza tana qoqarin hade fuskarta daga dariyar da take sadai ta gagara hakan,ci gaba yayi da kallonta yadda take son tsuke fuskarta ya taimaka wajen fito da beauty point din dake kumatunta,wanda ko sau daya bai taba kula dashi ba sai yau,qarar wayarshi ita ta dawo dashi daga duniyar kallon daya tafi,saiya fara laluba aljihunsa cikin basarwa,sai daga bisani yaga a saman tebur ya ar wayar,hannunshi ya miqa ya dauko wanda sauran kadan jikinsu ya gogi juna,hanyar waje yayi yana amsa wayar da alama mai muhimmanci ce.

A hankali ya tura qofar falon ya shiga sanyin ac da qamshin nan na musamman da tun zuwanshi yaji sashen nasa nayi ya daki hancinsa,ba wadataccen haske a falon sosai sai daya sanya hannu ya kunna makunnin qwan falon sannan hasken ya gauraye ko ina,daga can bangare daya na falon ya hangota akwance,sanye da kayan bacci ruwan hoda mai turuwa riga mai dogon da wando mai kauri,sai farin hijabi da take sanye da shi wanda bai wuce qugunta ba,gabanta takardu ne a baje da litattafai,sai torch din wayarta dake kunne da alama karatu take baccin ya sureta,sannu a hankali kamar mai sanda ya isa gabanta yana dubanta fuskarta da tayi fes kamar ba bacci take ba,quruciyarta ta fito sosai,baccin ya mata kyau,murmushi ya saki sanda ya tuna abinda ya faru dazu yana zarar daya daga cikin takaddun gabanta wanda take rubutu akai ya soma karanta rubutun dake jiki daya bayan daya

Dauke idanunshi yayi ya maida kanta yana yaba tarin basirar daya gano sanda take gyara kwanciyarta cikin baccin da alama ta gaji da kwanciyar daya bangaren ne,iya yanda take bayanin aikin da aka bata kawai ya isa ya gaya maka cikin sahun daliban da take,jinjina kanshi yayi yana yaba mata kafin ya durqusa ya maida takardar cikin 'yan uwanta sannan ya tsugunna yana tattare mata takardun waje daya.

Motsin takardun shi ya farkar da ita,zumbur tayi ta miqe ta zauna tana dan matsawa baya,da sauri ya dora yatsanshi akan lebansa yana fadin
"Shshshsh....in kika sake kikamin ihu irin na dazu saina cinye bakin" kunya ce ta kamata daya tuno mata da kuma lafazinsa na yanzu,saita sadda kai tana gyara zamanta a fakaice saboda yadd wandon jikinta ya tattare qaurinta ya fito,maimakon daya gama hada takardun taga ya miqe sai ya koma ya zauna sosai,yana soke yatsunshi cikin na juna idanunshi a kanta
"Uhmmm,bani labarin abinda ya faru da bana nan" yatsunta ta lanqwasa suka bada sauti,cikin muryar wanda ya tashi daga barci wanda ta cakudu da yanayin sanyinta tace
"Ba abinda ya faru" lumshe idonsa yayi saboda yadda tsigar jikinsa ta zuba
"Me yasa baki nemi ni ba tunda na tafi?,haka ake yaya da qanwar?" Idanunta da suka sake haske saboda baccin da tayi ta daga ta zuba mishi su
"Ya salam" ya furta can qasan maqoshinsa ta yadda shi kadai zai iya ji
"Wai me yake damunka khalipha?" Ya tambayi kansa da kansa,baisan me yasa yake jin baqon yanayi tattare da ita ba,komai tayi sai ya bada wani reaction a jikinsa da zuciyarsa
Chapter 71 · 0% Book details