← Book details Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 114

Sashe 107

Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan gaba dayansu bai hanasu tashi sallar asuba ba,tare sukayi jam'i,ya waiwayo yana kallonta sanda suka idar cikin tausayawa da wata tarin qauna,saidai taqi yarda su hada idanu,wata kunyarsa mara misali take ji,murmushi ya saka a sirrance don yasan kunyar me take
"Khalipha zan mutu,ashe dama baka sona?" Ya fada a hankali,sarai ta jishi kuma tasan ita yake tsokana,saitayi banza dashi saidai bakinta data dan zumburo
"Ina sonki mana my uwaisha,Allah sai yanzu ma nake sake jin wani sabon shauqi game dake,uwaishaahhh zan iya mutuwa saboda ke..." Salon yadda yayi maganar cike da tsokana da shagwaba ya sanyata sakim dariyar dole,shima tayata yayi kafin daga bisani yayi nasarar sanyata cikin jikinta yana shafar gashin kanta,addu'a ya dinga jero mata godiya da fatan alkhairi tana amsawa can qasa kanta na saman qirjinta,a haka har bacci yayi awon gaba da ita,shimfideta yayi a wajen yana gyara mata kwanciya idanunshi a kanta,ya jima ahaka yana kallonta kafin ya miqe yana shawagi kadan kadan a dakin kamar mai gadinta,zuciyarsa fes qal,wani farinciki na musamman na ratsashi,ashe da can ba rayuwa yake ba gashinan ne dai kawai?,ya godewa Allah da tasahon shekarun ya tsareshi ya kuma kare ayshanshi,duk irin gwagwarmayar rayuwar da suka fuskanta hakan bai sanya sun fada gonar daba tasu ba.

Bai taisheta ba sai dayaga lokacin sallar azahar yayi,tana zaune inda tayi sallar yana aukin kallonta yace
"Ko zaki shirya na kaiki wajen ummi?" Kai ta girgiza alamun a'ah,don tana ganin kamar idan taje ummin zata gane wani abu daya faru.

Da la'asar ta sanke wanka da ruwa mai zafo don taji dadin jikinta,taji din kuwa,har ta dan samu tayi mishi kwalliya,tana daura dankwalin kanta taji hannunshi a wuyanta,sarqar gold din da suka siyo ce wadsa duk ciki tafi kowacce kyau da tsafa,bata ce komai ba itadai tana tsaye tana kallonshi,yasanya mata dan kunnenta sannan ya kama hannunta ya zira mata awarwarayen,baya ya danja yana kallonta
"Kamar yadda na zata kin haskasu sosai" ido ta zare tana daga gira alamun neman qarin bayani
"Eh,kin haskasu,don kinfi qarfin su haskaki aysha basu da wannan kyan saidai ke haskasu" tilas ya sanyata dariya,idan yana yabonta wani lokaci yakan sanyata dole taji kanta ya kumbura,taji duk duniya babu macen da tayi sa'ar miji kamar ita
"Wannan shine dan qaramin tukuicin da zan baki kan farincikin da kika sanyani daren jiya" ya rada mata wanda kunya ta sanyata saka tafin hannunta ta rufe fuskarta,kamar yadda ya saba ya hanata godiya yace amma wannan karon ta adana godiyarta sai haduwa ta biyu,murmushi ta saki kawai,khalipha na sata jin kunya shi kuma babu ruwanshi.

Haka sukayi zamansu yana jinyar abarsa yana lelenta,saida sukayi kwana biyu cur sannan suka fita,zuwa sannan ta samu sauqi bata jin komai a jikinta,don ya bata tazara bai sake neman komai daga gareta ba,ranar tare da ummi suka wuni a masallaci,don suna saka ran a satin zasu bar saudiyya.

Cikin satin kuwa khalipha ya dinga daukarta suna zuwa siyayya,har gajiya tayi da siyayya,ya dinga sanyata tana diban kaya kamar banza,batasan cewa ba nijeria zasu wuce ba sai ana ya gobe zasu tafi,ya shaida mata suma zasu suga ruqayya ne,langabe masa tayi tana kallonsa
"Nayi missing din anni pls ya khalipha...."
"Na sani nima haka,amma inaso muje mata ne da babbar tsaraba" sam bata gane ne yake nufi ba sai tace
"Akwai tsarabar dana siya mata,kuma abinda tafiso shi na siya mata,nasan zataji dadinta" bakinsa ya tabe yana kada kai
"Duk tsarabar da zaki kai mata bata kai wanna ba,so nake ki samar mata jika....." Ai bai qarasa ba ta saki ihu tana rufe fuskarta,yayin daya bita ya danneta yana qoqarin saita bude fuskar ya qarasa gaya mata ita kuma ta qiya,daga qarshe shi yayi nasara dole sai rintse idanunta tayi tana saurarenshi a haka.

Karon farko da suka soma haduwa da ruqayya tayi aysha ta kwanta mata sosai,kamar yadda itama anty ruqayya ta kwanta mata,ta rasa inda zata saka ayshan,ta lura akwai sabo da qaunar juna sosai tsakaninta da khalipha,yaranta kamar aysha ta qwacesu,yara masu kyau da tarbiyya.

Tun anty ruqayya na mata hira kan dabarun zama da miji tana jin kunya har daga qarshe ta haqura,a nan ta samu sirrika masu tarin yawa a wajenta,dauka mata wannan tasha,dauko mata wancan ta lasa duk wasu hadin na larabawa ne,sai data tsima ayshan da kyau cikin dabara,donta lura da take taken khalipha wanda ta fuskanci ayshan sam batasan me yake nufi ba,ana sallar magariba ta sanya ayshan tayi wanka da kyau cikin ruwan turaruka,ta bata wata rigat bacci mai kyau saidai tana da dan kauri wadda tasha turaruka kala kala,bayan ta gama shiryawa suna gefan gadon anty ruqayyan ayshan na sauyawa qaramin yaron anty ruqayyan pampers khalipha ya shigo dakin wanda dakin spare ne na baqi mata dake cikin gidan,dubanshi anty ruqayya tayi samda yake tsaye ya tokare bango da qafarsa guda daya daya yana tsaye a kanta,hannunsa harde a qirji ya dan shagala da kallon aysha wadda antyn ta gyara mata kanta yayi kyai qwarai
"Ya ne alhj halifa?" Saiya saki ajiyar zuciya a boye ya maida kanshi gunta
"Zuwa nayi ki bani matata,tunda na fuskanci so ake a qureni ana zaton bazan iya magana ba" dariya ta saki
"Allah ya baka haquri,aysha tashi ki bishi tun bao daukeki da kanshi ba" sauke qafarshi yayi yana tattare hannun rigarshi
"Kamar kuwa kinsan abinda nake nufi kenan ba?"kafin suce meye su duka ya daga ayshan cak yana fadin
"Allah ya bamu alkhairi saida safe anty" kunya kamar aysha tayi me?,sauqin abun daya duka yaran antyn na dakinsu suna assigment,tun daga hanya qamshinta ya soma rikitashi,suna zuwa daki ya qarasa birkice mata,ranar ya more angoncinsa qwarai,taso tayi dauriya amma daga qarshe saidata nuna raki,duk da akwai sauqi akan karon farko,shikam ji yayi kamar ma ranar yake ango.

Washegari qememe ya hanata fita sai daya sake morewa,kunya tasa ma ta kasa fita gaba daya,'yar halak anty ruqayyan saiga aiken breakfast ta turo babban danta ya kawo musu,koda yamma da suka fito zai zaga da ita gari antyn fuskewa tayi kamar ba'ayi komai ba,wanda hakan ya sanya aysha itama ta sake.

Kwanansu bakwai a dubai suna amarci sosai,randa suka dawo daga wani mall tana fitowa daga wanka saiga kiran wayar hanan,ta tsaya da tsane ruwan kanta da take ta amsa wayar,ta gaya mata an dawo daga yajin aiki,suka dan taba hira sannan sukayi sallama ta aje wayar tana duban khalipha dake ninke kayan da suka cire shi da ita,haka yake baida qyuyar aiki,wani lokaci har mamaki yake bata,baida girman kai ko kadan,baya jin yiwa iyalinshi aiki ko wata hidima,wani abunma kafin tayi musu shi yayi
"Komawa gida yazo kenan,kaga hanan ce ta kirani tacemin an koma strike" kanshi kawai ya daga ya kalleta,saiya maida yaci gaba da abinda yake ba tare daya ce mata uffan ba kamar ma baiji abinda tace ba,dubanshi kawai take,ta tabbatar yaji din,amma batasan me yasa yayi banza da zancan ba,saitaja bakinta itama tayi shuru taci gaba da sabgarta,saidai jikinta gaba daya a sanyaye yake.

Har sukazo kwanciya jikinta a mace yake,yayin da shi kuma har a sannan baice da ita komai ba,sai daya gama addu'at kwanciya ya shafa itama ya shafa mata sannan ya janyota jikinsa,a hankali can qasa yace da ita
"Karki wani zafafa da yawa,kar ki saka buri da yawa,Allah ya sani ni kadai nasan me nakeji a zuciyata a kanki,kici gaba kawai da addu'a kan ci gaba da karatunki a wudil,idan babu alkhairi Allah ya zaba miki abinda yafishi alkhairi"sosai gabanta ya fadi tana tsoro da fargabar fa yace ba zata koma ba,amma duk da haka saita danne kawai,tunda shine sila na komai hatta da karatun nata ma.

Cikin dare ta tashi a firgice sakamakon mafarkin da tayi,gidan daddy ya cika anata kuka,shi kuma yana zaune yana ta bin mutane yana basu haquri,ita kuma waisai ta shigo ta fadi tana kuka,saiya dagata yana cewa ta fada kan maciji,sai macijin ya sareshi shima ya fadi anan sai kuma akayo kanshi anata jijjigashi amma ya daina motsi,tana cikin bawa khalipha labarin kawai saita saki kuka,harga Allah zuciyarta tayi gida a sannan,da qyar ya lallabata ya nuna mata sharrin mafarki ne,shi ya sanyata tayi alwala shima yayi suka dasa sallar nafila har asuba,bayan tayi sallar ne bacci ya dauketa.

Tana farkawa kuwa layin daddyn ta soma kira,babu jimawa ya daga,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta soma gaidashi,a sake yake amsawa ta tambayeshi jiki yace jiki da sauqi sosai,don bai taba jin dadin jikin nasa irin yau ba,hira sukayi mai tsaho sannan sukayi sallama tace ya gaida mutanen gidan,yace zasuji don safiyya ma mutuniyarta nakan hanya tace saitazo ta kawo masa wani dahuwar nama,tana dariya tace idan tazo daddy kace ta ragemin,yayi dariya yana fadin
"shikenan kuwa zata ji,sai wani lokacin kuma"
"Zan sake kira daddy anjima in sha Allahu"
"Allah ya bamu aron rai"
"Amin" da haka suka rabu,khalipha na tsaye saman kanta yana kallonta yana dariya
"Yar daddy,kin kirashi dai kinji dadi ko,kuma kinji lpy lau yake sharrin mafarki ne,haka kawai jiya kika wani birkice,ina shirin da asuba adan sanmin na d'ana duka aka hanai" juya qwayar idonta tayi cikin kunya tana murmushi
"Hankalina ya tashi ya khalipha,ina son daddy" gefanta ya samu ya zauna
"Mutum ne na qwarai sosai" daga haka hirar daddyn ta balle a tsakaminsu,kowannensu na tuna alkhairinsa gareshi.

A ranar da yamma tana tare da anty ruqayya suna hira khalipha ya shigo yana shaida.mata ta shirya nan da wa daya zasu wuce nigeria,cikin mamaki anty ruqayya kanta take kallonshi bama ita ayshan ba
"Lafiya daiko?" Ta tambayeshi
"Lafiya,aikime kawai ya taso min a kamfani kiran gaggawane ya samu"
"Auto,har naji dadi" ta fada tana sakin ajiyar zuciya,itakam.aysha ba wani zumudi dataji wanda ta tsammaci zataji duk randa zasu koma gida,saita miqe zuwa dakinsu da zummar hada musu kayansu.
[16/03, 11:11 PM] +234 806 544 7089: 58
Chapter 107 · 0% Book details