← Book details Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 114

Sashe 49

Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Qarfe takwas na safiya suka gama shirin komawa gidan daddy wanda haka su inna yelwa suka zartar a cewarsu a gidan mutumin daya riqeta kamar diyarsa za'a dauketa a miqata gidan mijinta,itakam bata da wani tsari sai yadda suka tsara,wannan karon ma ce musu kawai akayi su fito ga mota,wannan karon bata musa ba bata ce komai ba suka fito,motocin guda biyu ne wannan zuwan,guda daya ita da aliya ne da mero sai larai da bahijja yayan baba auwalu,daya motar kuwa gimbiya inna yelwa ce da inna kulu ga mamakin aysha inna yelwan bata ce komai ba ko tayi wani abu na tada hankali kan an hadasu muhalli daya da inna kulun ba,sai kuma lanti matar baba sadisu da kuma qannen ummi mata su biyar jimillar wajen su goma suka nufo gidan daddyn.

Kamar wancan karon wannan ma tafiyar bata wani wahal dasu ko sunga nisanta ba,cikin mintoci zuwa awa guda suka isa gidan,suma gidan a cike yake da 'yan yinin biki,hakanan suka ratsa zuwa cikin gidan ayshan na musu jagora,bata wuce dakinta ba sai da suka soma zuwa wajen mummy don su gaisa,sama sama ta karbesu kafin daga bisani su wuce zuwa dakin ayshan su yada zango.

Qarfe biyu na rana ya shiga bangaren annin,ya kasa daurewa duk da yawan jama'ar dake gidan da sunan 'yan biki da kuma ciwon kanshi da yakeson ya dawo,ciwo ne daya sameshi kusan shekara goma baya bisa wani dalili,tun jiya rabonshi daya ganta abinda bai saba yi ba indai yana gari ko yana qasar,a kasalance yake takowa zuwa bangaren nata sanye da farar shadda riga iya gwiwa mai dogon hannu da wando da alama masu hade babbar riga ne,wanda ya barwa mahmoud ajiyarta a guest house dinshi da suka sauka shi da sauran abokanshi da suka halarci bikin,duk da ba yadda baiyi dasu suyi zamansu ba amma kowanne sai dayazo mishi,kanshi babu hula hannunsa daya saye cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun yake riqe da hular da bai saka din ba,duk inda ya gifta ido ake binsa dashi kaman yadda akasan amarya da ango da farinjini haka aka dinga tsokanarsa,murmushi kawai yake wanda kusan na yaqe ne saboda ciwo da kanshi keyi,yakan tsaya wani wajen su gaisa wani wajen kuma ya wuce abinsa,da yake yasan kowa yasan kuma dalilin da yasa mafi yawancinsu suke tarayya da su,a haka ya cimma anni a falon ta zaune ita da sauran 'yan uwa kowa na sabgar gabansa,falon ya cika da hayaniya da surutu dalili kenan da yasa yaji bazai iya zaman falon ba bayan sun gama gaisawa ya miqe,inda wasu mata dake zaune su uku kowacce idonta ke kasa taba qissima abinda zata fada wanda zahiri abinda kecin zuciyar kowannensu ne,inna maryam wadda kusan tafisu rashin haquri kuma mahaufiya ga zeenart tace
"Kadaiqi 'yan uwanka khalipha qarfi da yaji...duk dadin bare ai dan uwa ya fishi ko?,da cikin 'yan uwanka ka auri daya kai kanka kasan yanzu farinciki da ake yafi haka...." Murmushin gefen baki yayi wanda yafi kama daya motsa fuskarsa ne kawai,baisan me yasa wasu mutanen sam Allah bai halicci kunya aqwayar idanunsu ba,baisan me yasa wasu suke da saurin manta bara ba,bai cancanta idan ka aikata sharri ka mance da kayi ba,domin shi din dan aike ne,duk daren dadewa watarana zai dawowa mai shi,ta manta lokacin da 'yan uwan suka kasa tabuka komai ga rayuwarsu?,ta manta sanda suke gudunsu kowa ke qyamar hada muhalli da su?,ta manta cewa bare...baren da basu san daga ina ya fito ba shi ya tallafi rayuwarsu?,ya musu abinda kaf dinsu suka kasa yi musu?zaiso ya jefa mata dukka wadan nan tambayoyin saidai kuma a yanzu baijin yana da lokacinta,sai kawai ya saka kai ya shige dakin gadon anni.

Saman gadonta ya xube plat yana tallafe da qeyarsa da tafukan hannunsa daya hada guda biyu waje daya idanunsa a lumshe,kunnuwansa na masa tariyar kururwar maroqa dake faman kiransa da angon aysha a wancan awannin da suka shude,yana tariyo yawan jama'ar da suka halacci wajen,manyan mutane a qasar nan da wajenta,mutanen da bai taba tsammatar a rayuwarsa zaiyi tarayya da wasunsu ba.

"Lafiya dai khalipha?" Yaji muryar anni na ratsa dodon kunnensa,idanunsa da suka dan kada ya bude ya kalleta da su,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon
"Ba komai....kaina ne yake dan ciwo kadan..."
"Hayaniya ko?....dama nayi xaton faruwar hakan..kasha magani?"kai ya gyada
"nasha...."
"To Allah ya sawwaqe"
"Amin"
"Batun dauko amarya...." Anni ta fada tana dubansa,baisan sanda murmushi ya subuce masa ba mai sauti,shi shaf ya manta da agender ta gaba ma ta dauko amarya
"Anni....kina son yarinyar nan da yawa...Allah yasa itama haka ne" murmushi tayi
"Khalipha yarinyar ta wahala da yawa...ya kamata zuwa yanzu tasan akwai soyayya qauna da tausayi a ban qasa....ya kamata taji yadda sauran mutane suke ji idan suka samu mai nuna musu qauna....kasa a ranka amana ce zaka riqe saboda Allah,kar ka sanya cutarwa ko matsantawa a tsakaninku,ka bata 'yancinta wanda bai sabawa addini da shari'a ba" hakanan yaji zuciyarsa na bugawa da kalaman anni...yanajin kaman ta dora masa wani qaton dutse saman kanshi,sai kawai ya miqe
"Qarfe nawa zasu je tahowa da itan"
"Kaman biyar ko shida"
"Ba damuwa......" Tare suka fito da annin ya fice daga sashen nata ya koma nashi bangaren don yana buqatar kadaicewa baya son hayaniya ko zai damu ciwon kan nashi ya sauka,bai jima da shiga ba bacci yayi awon gaba dashi mai nauyi,bai tashi farkawa ba sai qarfe hudu da rabi,subhanallahi ya ambata ganin lokacin sallah ya qwace masa,da sauri ya dira daga gadon ya wuce toilet ya kama ruwa yayi alwala ya fito ya tada sallah.

Yana tsaka da azkar din yammaci biyar saura mahmoud ya kirashi
"Wai ina ka shiga ne?"a kasalance yace
"Ina cikin gida"
"Anya kuwa?....irin wannan murya kodai amarya ce...." Tsaki khalipha yaja,mahmoud yana magana kaman baisan komai kan auren ba
"Me yake faruwa?" Ya jeho masa wata tambayar daban
"Maganar dauko amarya fa?....sai yaushe?"
"Biyar zuwa shida anni tace"
"Toh ba damuwa...ciwon kan fa?"
"Da sauqi dai...baikai na dazu ba"
"Allah ya qara afuwa...zan sake nemanka"
"Okey" ya fada yana katse wayar yaci gaba da azkar dinsa kafin daga bisani ya lula duniyar tunani.

Qarfe biyar da rabi yana shirin shiga wanka ko zaiji qarfin jikinsa kiran mahmoud ya sake shigowa
"Mun fito da dukka motocin nan fa yau ne yafi cancanta ayi amfani da su,dasu xamu tafi daukota" idanuwa ya zaro yana mamakin mahmoud
"What....mahomud dukka sababbi ne...kasan me zanyi da su,wai kana nufin duk yawansu dasu zaku tafi kaman zaku taron president?"
"Tafi president ma" ya fadi yana katse kiran,sauke wayar khalipha yayi yana binta da kallo cike da mamaki,kada kai kawai yayi ya shiga toilet din ba tare daya sake bi ta kan mahmoud ba.

Gaba daya layin ya dinke tsaf da jama'a,koda bakasan wajen ba idan kazo wucewa zaka san cewa biki ake,daga cikin gida kuwa bangaren asma'u amarya an gama shiryawa tsaf,ko irin kunyar nan tsoro da fargaba na amare babu ita tattare da ita,kwalliya ta tsara sosai kamar ranar ne ma ake dinner din tata,qawayenta 'yan bana bakwai kewaye da ita suna sake tunzurta tare da hirarrakinsu,lubna qawarta wadda itace ta biyu baya ga mai sunanta husa ta shigo tana cewa
"Guy din nan ya gama fitowa dake asma...ke kinga sabbin motocin da suka jere a layin nan kar da su,da alamu ma ba'a taba hawansu ba,iya ganinka sune kala daya yadda kikasan za'a rakiyar shugaban qasa?,wata boyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan a fili tayi far da ido,dukkan fargabarta na tafiya,ta boye dukkan wani gata da aysha ta fita tsoronta kar a barota ranar da za'a kaisu,ta toshe duk wata kafa da zata fidda labarin aljannar duniyar da aysga ta samu,tana tsoron kar a daukan amarya suyi shirin da zai rusa nata,wanda kallo zai koma sama,maimakon a kalleta ya zama ayshan itace abar kallo,ashe da wasa hamid yake mata daya gaya mata cewa mota biyu xai kawo shi baya son hayaniya azo a cika masa gida a bata masa waje,tunda ya fada ta kasa challanging dinsa don kar yayi fushi,amma kuma a farga take na kada ya aiwatar da abinda ya fada din,ashe ma wasa ne
"kice yau muma ranarmu ce...idan da rabo muma sai kiga mun dace da wani don din fa" inji nusaiba wanda maganarta ta farantawa da yawa a wajen rai,shewa suka saka sannan suka shiga tafawa cikin walwala da nishadi,asma'u kam ji take kaman ta shide don dadi,kanta ya sake fasuwa,taji ba komai bane don aysha ta fita da gida tundaya kankarota a nan,kuma zata ci gaba da toshe duk wata hanya da qawayenta zasu san mijinta sama yake da nata mijin.
Chapter 49 · 0% Book details