← Book details Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 114

Sashe 104

Daurin Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asma'u dake tsaye can gefen wasu shukoki tana ganin abinda ke faruwa ta saki ajiyar zuciya,wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar tunkarar khaliphan,komai nashi yayi mata,dukkan wani abu da take bida ta ganshi tattare da shi,matuqar zai amince mata kashe aurenta ba wani abu bane mai wahala a wajenta,bare a yanzu da take jin auren tamkar ana dorata saman qaya ne,ko qawaye yanzu ta yanke alaqa da kowa,don kada ma wani ya rabeta ya fahimci halin da take ciki,kayan da daddy ya mata order tuni sun taru sunci uwar kayan da kudin ita da qawaye tun suna wancan gidan nasu,bata iya adani ba,bata iya tattali ba,batasan ta juya biyar ta koma goma ba,ta riga ta saba tun agida saidai ta bid'a a bata,takowa ta dinga yi har zuwa inda khalipha ke zaune cikin motar tayi knocking,ya tsammaci aysha ce saiya sauke gilashin yana murmushi,idanu biyu sukayi da asma'u,take yayi gaggawar gimtse fuskarshi yana dubanta
"Ranka ya dade yau kaine a gidan namu da kanka?"
"Eh...yaron oga ne da 'yar aikin gidan sukazo gaida mai gidan" saita danyi dum saboda tasan magana dai yake gaya mata,cikin barikanci tace
"Banda dai tuna baya,abinda ya wuce ya riga daya wuce,na baka haquri amma na fuskanci har yau baka haqura ba" tsaki yaja yana shirin daga gilasanshi saboda sauraton tama sam baida amfani saita dafe cikin karyewar zuciya
"Don Allah khalipha kayi haquri,ka taimaka ka karbeni kamar yadda ka amshi aysha,ba sonta kake ba tun asali nice wadda kakeso,qaddara ita takawo faruwar komai,kai kadai kai zaka cikamin burina"
"Burinki na kudi ko?,baki da matsala waisaita kudi ne?,a duniya babu wani abu mai daraja bayan kudi?,inasom in miki gargadi na qarshe kar bakinki ya sake kuskuren cewa bana son aysha na aureta,har abada aysha itace zabina,tun kafin nasanta nake qaunarta,tin kafin nasan zatazo cikin qaddarata nakesonta,kin fahimta?"
"Kamar yaya?" Ta yiwa kanta tambayar,saidai bai tsaya bata amsa ba yadaga gilasanshi yana jan tsaki ranshi yana baci,wato a rayuwa ma ka aikatawa mutum ba dai dai ba kazo daga bisani kana jin kunyarshi ka rahama ne?,wannan kenan na nuna zuciyarka akwai ragowar danshi,idanunka basu qarasa qeqashewa ba.

Kallo daya tayi masa tasan yauma baida lpy,hankalinta ya tashi sosai,tunda yayi wancan rashin lafiyar kullum saita kirashi amma ko sau daya bai taba nuna mata yana kwance ba,amma saboda qarfin hali irin na daddy nuna mata yake ba komai,ta sanar mishi tarr da khalipha suke,yace
"maza shigo dashi mana indo,yaron kirki dan albarka".

Tana juyawa daga wajen motar sukaci karo da aysha,kallon data jefa mata shi ya sanya jikin ayshan ya bata akwai wata a qasa,me take jikin motar khalipha?,tasan halin asma'u sarai shekarun da suka diba gida daya ba wasa bane,saita gifta ayshan ba tare data ce mata komai ba,itama ganin haka yasa ta kama kanta tunda tasan ba wani abu data yi mata.

Tare suka jero har cikin parlour din,a sannan mummy na zaune tana hada magunganan daddy daya gama sha,idanunta kan khalipha sanda yake gaisheta,banbanci muraran ta ganshi,qyashi ya cika ranta,saita kasa zama tabar musu falon ta koma sashenta,wanda hakan ya basu damar hira sosai duka su ukun harda khalipha,irin hirar da zata ce ma bata tabayinta da daddy ba,har tayi mamakin dadewarsu sanda suka tashi zasu tafi suna mishi sallama kan gobe zasu wuce umara,dai dai sanda asma'u ta shigo falon,sai ta samu waje ta zauna tana jinsu,cikin farinciki daddy yayiwa ayshan murna,saboda yasa yunqurin kaita sai mummy ta sako wasu qorafe qorafe da zai sanya a dage zuwan da ita koda daddyn bai shiryawa hakan ba
"Uhmmm,ba sabanba,su umara manya,kai bawa da baka taba zuwa ba daka shiga uku" asma'u ta fada qasa qasa yadda ayshan zata jiyota,murmushi tayi sannan itama ta mayar matan ta yadda zata jita da kyau
"Mun godewa Allah da bai banbanta saudiyyan masu kudi da talakawa ba,duka dai gurin daya ne inda kaje nima can zani,Allah ya kirani babu damar dakatarwa" saita miqe ta isa gaban daddy tana masa sallama bayan fitar khalipha wanda yadan basu waje ne suyi sallama
"Allah ya qara maka lafiya daddy,bansan wanne irin abu zan saka maka dashi ba a rayuwarta,don Allah daddy ka tambayi koda abu daya ne a wajena wanda kake buqata daga gareni" murmushi ya saki
"Aysha indo har kullum kedin ta dabance,haka Allah yake tsarinsa cikin halittunsa saiya fifita wani kan wani,dukkan abinda nayi miki nayi miki ne Saboda Allah,na miki saboda a lokacin kina cancanci kuma kina da buqatar ayi mikin,abu guda daya da zan nema a gareki shine,ko bayan raina karki manta dani kici gaba da yimin addu'a"zuciyarta ce taji ta karye da kalamanshi,wani rauni ya kamata,take hawaye ya balle mata,asma'u dake zaune gefe ta tabe baki
"Kalen dangin masifa,kamar ta fimu sonshi,sai kace ita ya haifa bamu ba" ta fada a zuciyarta
"Indai xan manta dakai daddy to lallai zan manta da kaina,baka cikin jerin mutanen da zan iya mancewa dasu har numfashina yabar gangar jikina,ubangiji yayi maka jagora a dukka lamuranka duniya da lahira"
"Amin ya Allah ayshatu,idan na taba yi miki wani abu naba daidai ba tsahon zamanki a gidan nan ina neman afuwarki" kuka ta saki sosai harda sheshsheqa
"Daddy niya cancanci na nema afuwarka da zanyi tafiya,ba zaka taba laifi ba awajena daddy koda naman jikina kake yanka kullum"
"Daina kuka ayshatu,ubangiji yayi miki albarka duniya da lahira,idan kinje kimin dawafi na musamman kiyimin addu'a sosai"
"Zan maka addu'a daddy in sha Allahu fiye da yadda zan yiwa kaina"da haka sukayi sallama,haka kawai taji zuciyarta ta karye qwarai,hakanan taji kamar karta tafi,kukan da take yaqi tsayawa har a cikin mota,tun khalipa na daurewa har ya gaza
"uwaishah,ki taimakeni kiyi shuru,har cikin qirjina nakejin ciwon kukan da kikeyi" bata son bata masa rai ko qanqani,hakan ya sanya dole tayi shuru gami da yin luf a qirjinsa,kusan ranar wuni tayi a sanyaye,tunanin daddy fal zuciyarta.

🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶🧶

Washegarin ranar jirginsu ya daga sai saudiyya,a garin makka suma soma sauka,suna sauka a masaukinsu dukkansu sukayi wanka suka dauki harama,saboda tsabar murna da zumudi ma ta rigashi kammalawa,ji take kaman tayi tsuntsuwa ta ganta bakin ka'aba,tana da abubuwa da yawa da zata roqa,tana da mutanen da takeso ta yiwa addu'a sosai,idanunta a kanshi sanda ya kammala daura hiraminshi,idanu suka hada sai suka sakarwa juna murmushi a kusan tare,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi.

Sati guda sukayi a garin makka,iya ibada kam sunyita saidai fatansu Allah ya amsa,bata taba sanin khaliphan ta fannin ibada jarumi bane sai a wannan karon,duk nacinta da son ibada sai taga ashe ya kere mata,sau tari idan ta gaji tayi kaman zata huta sai taga shi a sannan ya saka qaimi,sai ya sake zaburar da ita,tabbas ta yarda ta kuma amince cewa kowacce mace halayenta idan zama yayi zama na kamanceceniya dana mijinta,kota debi wasu dabi'u nashi koshi ya debi nata,idan akayi katari na gari ne sai nagartarta ta ninku,idan kuma akasin haka ne walau ya rinjayeta ta ko ta koyi kaso mafi yawa daga cikin halayensa,shi yasa akeson ko aboki zakayi ka aboci na qwarai,don annabi ya kwantata aboki na qwarai da misalin mai saida turare ne ko.baka siya ba idan ka zauna dashi dole wataran zai san maka,kaima zakayi qamshi,hakanan nara gurbin aboki tamkar abota da maqeri ne,kana zaune feshin wutar zai dinga sauka atufafinka yana bata maka sutura,hakan shike nuna auren miji na gari shine babbar sa'a hakanan abu mafi muhimmanci da gata da mace zata yiwa kanta da zuriyar da zata samu a nan gaba.

Randa suka cika sati guda a garin makka suka wuce madina don suyi ziyara,musamman ya samu motar da zata zagaya dasu duk wani wajen da tarihi yazo dashi a addinin musulunci,farincikin data dinga ji ya zarce wanda taji a garin makka,jinta take fes,zuciyarta qal,kamar babu wani abu daya taba samunta a rayuwa na bacin rai,kullum tana maqale da masallacin ma'aiki tana yiwa kanta khalipha daddy da anni addu'a,dama duk wanda ya ratsa rayuwarta,idan na neman shiriya ne ta nema masa,idan na fatan alkhairi ne tayi masa.

Randa suka cika kwanaki hudu a garin madinan,da wata safiya sun fito zuwa masallaci ita da khalipha,irin wannan yanayin yana mata dadi qwarai,takan jita wata ta daban ta musamman,zuciyarta da ruhinta kan cika da farinciki,tabbas garin madina dabanne,hatta da yanayinsa ma daban yake,tayo bangaren mata shi yayi bangaren maza taji sabuwar wayarta daya siya mata tana ruri,tana dubawa taga sunanshi ne,cikin mamaki ta kara a kunnenta
"Ta wacce qofa zaki shiga?" Ya tambayeta,gaya mishi tayi sai yace ta sauya ta shiga ta daya qofar,bata kawo komai ranta ba ta amsa mishi ta kashe wayar sannan taci gaba da takawa donta wuce zuwa cikin masallacin.

A hankali take takawa cikin zuciyarta tana ta istigfari kamar yadda ta saba tunda suka zo,bata minti daya cikakke bakinta babu ambaton Allah,tana son ta ribaci lokacinta da dimbin falalar da garin yake dashi,dukkan aikin da kayi cikin garin walau na alkhairi kona sharri kana da ninkin lada ko zunubi.

Kamar a mafarki kamar wasa sukayi kacibus da umminta tana shirin fita daga masallacin itama,kallon kallo suka fara yuwa junansu tamkar wasu baqin juna,dukkan wani tashin hankali da fargaba da aysha takeji a sanda suka hadu a yanzu fes take jinta,zuciyarta a taaye take kyam,idanunta cikin na umminta
"Assalamu alaikum"aysha ta furtawa ummin tana dubanta
"wa'alaikumussalam"ta amsa mata itama tana dubanta,idan batayi kuskure ba qwalla take gani cikin idanuwan ummin fal,saitadan gotata kamar zata shige,da sauri aysha ta riqe tsintsiyar hannunta,tsahon minti daya suna a haka kowa ya kasa motsawa,sai ta jiyo sheshsheqar kukan ummin nata,abinda yayi masifar tayar mata da hankali,da hanzari ta sakar mata hannu tasha gabanta,batayi auneba taji ummin ta rungumeta tsam tana sakin kuka sosai
"bazan iya ba,bazan iya ci gana ba"
"Kiyi shuru ummi don Allah" saiga ayshan dake bata bakin tayi shuru itama ta saki kukan,duk yadda taso daurewa ta kasa,kuka suke sosai,ganin masu wucewa zuwa cikin masallacin na kallonsu ya sanya ayshan janye ummi gefe.
Chapter 104 · 0% Book details