Sashe 98
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ruma ta zumɓura baki ta ce "Ni fa bana riƙe abubuwa, na manta komai, likita ya hana ayi mini zancensu"
"Ki yi haƙuri ki bamu haɗin kai, ba zancen su zamu yi miki ba, yaya aka yi aka sace ki? Yaya aka yi ki ka haɗu da aisha har ta baki jaririnta da ɗankwalinta?".
"Ni kawai sace ni aka yi, muka gamu da ita, ta bani yaron, na taho" yanayin yadda ta yi maganar zaka san ƙarya take yi.
Ɗan sandan ya sake nutsuwa ya ce "Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, a ina kuka haɗun da ita?"
Kawar da kanta gefe ta yi, irin idan ka gaji ka tashi É—in nan.
Duk yadda ya so lallaɓa rumaisa sai da ta fara hasala shi, rarrashin duniya amma fafur ta ce ba ta san komai ba.
Mama ta yi kanta da zagi, Abubakar yana lallaɓata amma ta yi mursisi tana hawaye, ta ce ba ta san komai ba ita ta manta.
Mai sunan baba da tun ɗazu yake jin su bai yi magana ba, sai yanzu ya tashi ya nufi gadonta, ya ture Abubakar shi ya zauna ya kalleta, ta sunkuyar da kai ƙasa, cikin muryarsa mai razanar da ita ya ce "Kalleni" ta ɗago da ƙyar ta kalleshi.
"Gaya musu abun da suka tambayeki" ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta mayar da idonta kansa ta shiga girgiza masa kai.
Idonta ne ya cika da hawaye, amma ta kasa magana.
Mama ta ce "Ruma ba kya ji ana yi miki magana ne?".
Ammi ta ce "Ku bita a hankali, kar ku tsoratata".
"Ba zaki faɗa ba sai na saka sun saka miki sarƙa sun tafi da ke, ana magana kina kallon mutane" yadda mai sunan baba yayi mata maganar cikin hargowa sai da ta tsorata, jikinta ya hau rawa, tana girgiza masa kai.
Ya sake kafeta da ido ya ce "FaÉ—i, komai É—acinsa da muninsa faÉ—i"
Cikin rauni idonta na zubar da hawaye ta ce "Bana son faɗa, bana son tunawa ne, labarin babu daɗin ji, kuma babu daɗin tunawa. Ta mutu!ta mutu! Ko sin ce sun kasheta? Ta mutu ne ba ta raye, kuma sun zo da mota sun ɗauke ta tun a can, bana son tunawa, mutuwar anty aisha abu ne da ba zan manta ba, ta mutu! Ta mutu!! Ta mutu ku rabu da ni dan Allah tun da na gaya muku" ta yi maganar cikin hargowa tare da watso piliown kan gadon tana wani irin kuka, da sai da mai sunan baba ya rungumeta jikinsa a matuƙar sanyaye.
Takawa ta gani a tsaye a ƙofar ɗakin, ya zuba mata ido da dukkanin nutsuwarsa, yana jin abun da take faɗa tamkar zubar dalma a tsakiyar zuciyarsa.
Ayshercool.
08081012143
*Littafin kuɗi ne, a bani hakkina kan a karanta, ₦500 ne via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143
Lumshe idonta ta yi, hawaye na tsiyaya daga idonta, mai sunan baba yana jin yadda zuciyarta ke bugawa da saurin gaske.
Duk wanda yake ɗakin sai da yayi sak, cikin ammi ya kaɗa yayi wani irin ƙugi, take ta fara fatan Allah ya sanya mafarki take ba gaske bane ba.
A hankali takawa ya tako cikin ɗakin, sai a lokacin suka lura da zuwansa, ya ƙarasa gaban gadon rumaisa, da take kwance a jikin mai sunan baba, hannunta ya kama ya yi wa wani irin mugun riƙo ya dubeta ya ce 'Ki ka ce matata ta mutu, ta yaya? Ya za ayi ki ce aisha ta mutu? Ke kin san mutuwa kuwa".
Ba riƙon da yayi mata ne ya sakata a cikin tashin hankali ba, abun da take gani a tattare da shi ne ya ɗaga mata hankali, sai dai alamu sun nuna babu wanda yake ganin abun da take gani sai ita kaɗai.
Mai sunan baba ne ya shiga ƙoƙarin ƙwace hannun rumaisa daga na Adam, amma ya kasa ruma kuwa ta ƙura masa ido tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Ammi tamkar an dasata, ta ji maganar a bazata, ba ta taɓa tunanin abubuwa zasu cigaba da rikicewa haka ba.
Bashir ma ƙoƙarin ƙwace hannun rumaisa suke yi, amma riƙon da ya yi mata ba na wasa bane ba.
"Ki ka ce matata ta mutu? Ta mutu fa ki ka ce, ki tashi daga baccin da ki ke yi ki gaya mini gaskiya, ba Aisha ce ta mutu ba".
Cikin kuka ta ce "Ka cikani kar ka ɓalla mini hannu, tun da na gaya maka abun da ka ke son ji" tayi maganar cikin kuka.
Bai iya cewa komai ba, sai ganinsa suka yi ya silale a ƙasa ya suma.
Sai a lokacin ammi ta samu hawayen idonta suka gangaro, mama da sauran mutanen wurin suka yi kan adam, sai dai ba ya motsi sam.
Da gudu Abubakar ya fita, sai gashi da likitoci sun biyo shi, suka yi umarni a kawo stretcher a É—au adam a kai shi emmrgency.
Mai sunan baba kuwa bai motsa ba, sai ma rungume rumaisa da yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, saboda kukan da take yi, ruma kuwa da ta ga an kawo stretcher an ɗora adam a rikice ta ce "Wai shi ma mutuwa ya yi? Haka anty aisha fa ta yi ta daina motsi bayan ta yi ta fitsarin jini, jininta ya ƙare"
Mai sunan baba ya sanya hannunsa ya rufe mata ido ya ce "Bai mutu ba in sha Allah, ki yi ta Addu'a".
Gaba daya ta kasa nutsuwa, mutuwar aisha ce ta dawo mata sabuwa fil a idonta, duk masifar mai sunan baba, tausayin rumaisa ya mamaye shi, yarinya ƙarama tana ta gamuwa da iftila'in ƙaddara.
Ammi kuwa kuka ta din ga yi, kamar babu gobe ta yi iya ƙoƙarin ta amma ta kasa tawakalli ta jure, abu ka da mata abu na 'ya'ya, mama na son ta rarrasheta amma ita ma ta ɓuge da kukan, daga baya suka bi bayan su Bashir, domin jin halin da Adam yake ciki, Yaya Abubakar ya tare su a hanya ya ce "Mama, ku je ku zauna in sha Allah babu wani abu, ga likitoci can sun rufu a kansa, ba za su bari ma ku shiga ba, ku yi haƙuri ku je ku zauna, ayi masa addu'a.
Yadda ammi take kuka zai tabattar maka da ba iya mutuwar ce ta dake ta ba, akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, la'ila ha illa la Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam" sune abubuwan da ammi ke ta nanatawa.
Mai sunan baba ya numfasa ya ce "A duk lokacin da muka rasa abu mai muhimmanci a rayuwarmu, sai mu tuna Allah ne ya bamu, kuma Allahn da ya bamu yafi mu son abun, kuma ya fi mu sanin muna son abun, dan haka addu'a zaki yi ki daina kuka" da ruma yake maganar, amma a zahiri ba iya ruma yake yi wa nasihar ba, har da ammi.
"Mai sunan baba" ruma ta kira sunansa.
"Na'am"
"Ka ga laifina da naƙi faɗa tun da farko? Ka ga shi ma zai mutu ya bar jaririn ko?"
"Ke da ki ka ce ba shi ne babansa ba, Meyasa ba kya so ya mutu?"
"Mai sunan baba" ta kuma kiran sunansa.
"Na'am" ya amsa mata.
"Idan sabir ya girma sai ya ji duk a gabana iyayensa suka mutu, idan ya tsane ni fa? bana son tunawa da mutuwar anty aisha, idan na tuna ji nake kamar na kashe kaina, da tsohon cikin nan fa dukanta suke yi, idan zasu dakeni ta hanasu, tun da suka taka mata cikinta take rashin lafiya, idan barde ya kawo mini abinci, tare muke ci, wataran ta ce in cinye ni 'yar baby ce ita ta ci girma. Mai sunan baba na yi ta yi musu magiya su kai ta asibiti suka ƙi, kuma sun san ba ta da lafiya, na yi ta kuka ina roƙonsu ita kuma tana musu magiyar su karɓi kuɗin fansata a wurin mijinta su sakeni ni yarinya ce. A hannuna ta mutu bayan na bata ruwa, babu wani ɗan sanda da ya zo kuɓutar da mu, kuma sai yanzu zasu zo su dameni wai sai na gaya musu tana ina? Me za su yi a kai bayan ta bar duniyar, na tsani duk wani jami'in tsaro tunda har anty aisha ta mutu ba wanda ya kawo mana agaji, sai wasu 'yan ta'addan ne suka ƙwace mu, wallahi duk wanda ya kuma tambayata wani abu ba zan faɗa ba, dan babu abun da za su iya yi a kai" tayi maganar cikin ƙunar zuciya tana rirriƙe hannun mai sunan baba.
A hankali ya kwantar da ita, ya toshe mata bakinta, saboda kamar nema take ta fita hayyacinta, adduoi ya din ga yi mata, har ya samu ta yi shiru, amma maganganunta sun É—aga masa hankalin, shi daga nesa ma masu ciki tausayi suke bashi, saboda dakon cikin ma kawai ya ishe su, balle ace a taka mace da tsohon ciki, abun da ban tausayi.
Daga mama har ammi kowa sai goge hawaye take yi, sabir ne ya motsa ya fara kuka, mai sunan baba ya sanya hannu ya É—auke shi ya fita da shi waje.
Ya ƙurawa yaron ido, sunan mahaifinsu rumaisa ta saka masa, ya tuna irin faɗi tashi da sadaukarwa da mama take yi a kansu, tun suna yara har zuwa yanzu da suka zama mutane ba ta daina ba, amma shi wannan ɗan bai san wannan ba, hasali ma tasa uwar tana kawo shi duniya ta mutu ta bar shi a dokar daji a hannun yarinyar da ita kanta ba ta san ciwon kanta ba, ta yi kwanaki tana gararanba da shi a daji babu ko wando a jikinsa ga ƙazantar haihuwa.
Wani irin tausayin yaron ya kama shi, ya rungume shi a ƙirjinsa yana shafa bayansa, wata irin ƙwallar tausayin yaron ta cika masa ido.
Abubakar kuwa tamkar wani daga cikin 'yan uwansa ne suka suma aka kwantar da su, sai kai wa yake yi yana komowa, sai da ya ga lokaci na neman ƙure masa sannan ya ɗau jakarsa ya tafi.