← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 174

Sashe 32

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma aka ce ki je ke da wani babba, anya ruma ke fa ba gaskiya ki ka cika ba"

Ruma ta ce "Ni dai wallahi na san babu abin da na yi"
Mama ya gyaÉ—a kai ta ce "Ai shikenan, zamu gani".

Ta ƙarasa ƙofar ɗakin 'yan mazan, ta ce "Waye ba zai fita ba yau a cikin ku? Wani ya zo ya je mini makarantar su yarinyar nan, an kira ni an ce ta je ita da wani"

Yaya Aliyu ya ce "Mai sunan Baba dai ya tafi makaranta, ni ma ina da lectures ƙarfe goma sha biyu, amma bari na zo mu je na ji menene"

Ita kanta ruma tunani take Meyasa ake neman wani a gidansu a makaranta?

Suna tafe a hanya da Aliyu yana mita "Ke, kawai kin sa an katse mini bacci na, Allah ya sa na ji wani rashin jin ki ka yi, na samu abin duka na zane ki"

Ta tura baki ta ce "Ni dai na san ban yi komai ba, wataƙila ma wani abun arzikin na yi ake nemanku, amma kowa ba ya kyautata mini zato"

"Ruma ai ke abin arziki  bai karɓe ki ba, sanin halinki ne ya sanya ake tsoron lamarinki"

Suna tafe a hanya, yara da manya mata da maza kusan kowa ya san ruma, suna tafe ana kiranta ta na É—aga wa mutane hannu, har suka isa makarantar.
Ofishin Headmaster suka je, ruma sai rarraba ido take tana 'yan ciye-ciyen ta.
Aliyu suka gaisa da Headmaster, ruma ma ta gaida Headmaster ta koma gefen Aliyu ta tsaya.

Headmaster ya kalli ruma ya ce "Waye ya sallameki jiya ki ka tafi?"

Ruma ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba.

Headmaster ya dubi Aliyu ya ce "To, a gaskiya ƙanwarka ce ko 'yar ka ba ta jin magana, sun samu saɓani da abokiyar karatunta, an yi musu sulhu amma ba ta ji ba, sun kuma faɗa jiya, ta karyata a hannu, kuma ta bita hanya ta din ga jifanta da dutse wai jifan shaiɗaniya. To uwar yarinyar nan ta ce ba zata yadda ba, yanzu haka tana division ta kai ƙara, suna jiran mu, ka san ƙabilu wasu lokutan basu da tawakalli ba su san ƙaddara ba".

Aliyu ya ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke dan ubanki a garin yaya ki ka karya 'yar mutane, kuma baki faÉ—a ba?"

Ruma ta zare ido ta ce "Kaii Innalillahi, wannan É—an dukan da na yi mata ne ta karye, zagina fa tayi ta zagi mama, ta dakeni shekaranjiya waccan, amma aka bani rashin......."

Cikin tsawa Aliyu ya ce"Rufe wa mutane baki, sai ki tashi mu tafi idan kulle ki za su yi ke ki ka jiyo, tashi mu tafi"
Ai ruma ko a jikinta, ta turɓune fuska.

Haka suka tasa ruma a gaba, zuwa police station. Mama sai kiran waya take ta na tambayar meyafaru, Aliyu ya na ce mata babu komai.

Ko da suka je police station, suka tarar da Asiya, an naÉ—e hannu, ga fuskarta duk a kumbure. Ruma ta kalli babar Asiya, kujera ba ta É—auketa ba, sai wani benci aka saka mata ta zauna, fuskarta ta sha uban tsagu kwaya-kwaya.
Ruma ta sunkuyar da kai ta na so ta yi dariya.

Suka nemi wuri suka zauna, wani É—an sanda ya kalli ruma ya ce "Yanzu wannan ce ta karya ta?"

Cikin gurɓatacciyar hausa, babar Asiya ta ce "shi ne ya karya ɗana wannan, ke ni ki ka zana a allo, ban fi babarka kyau ba? Ka zana katuwar mace wai ni ne, kuma ka karya mini ɗa, wallahi ba zan yarda ba, yaro ba tarbiyya"

Ruma ta ce "Ni fa mace ce ba namiji ba, kuma ita ta cewa babata tsohuwa, kuma wallahi mama ta fi kyau"

ÆŠan sandan ya dakawa ruma tsawa, amma ko gezau ta tsatstsare shi da ido.
Ta tsuke baki, tana cigaba da zazzago madara a hannunta tana sha.

Aliyu ya yi ajiyar zuciya ya yi ƙasa da murya ya ce "Wallahi idan ba ki nutsu ba, sai na bar ki a wurin nan, su yi miki duk abin da suka ga dama, kuma wallahi matar nan ta zauna a kan ki sai dai buzunki"

Ta waro ido ta ce "Kai dan Allah ka bata haƙuri, ai sai na mutu idan ta zauna a kaina"

Aliyu ya gyara murya, ya dubi ɗan sandan ya ce "Dan Allah Yallaɓai, a yi maganar nan a kasheta a yanzu".

ÆŠan sandan ya ce "A'a, case É—in a hannun DPO yake, sai kun jira ya zo"

Aliyu  da Headmaster sai bada haƙuri suke, Headmaster sai  cewa yake a samu a rufa maganar nan, a rufe case ɗin tun da abu ne na yara. Amma babar Asiya ta ce ba ta san zancen ba, sai an biwa 'yar ta hakkinta.

Aliyu suka ɗan fara hira da ɗan sandan da yake wurin, ruma kuwa da sun haɗa ido da Asiya, sai ruma ta zare mata ido. Aikuwa suka haɗa ido da babar ruma, tana zarewa Asiya ido. Aikuwa ta taso tana tafe da ƙyar tana bala'i, ta yo kan ruma.
Ruma ta zabura ta miƙe, ta haye bayan Aliyu ta na ihu.

"Wanna yaron ba shi da mutunci, ba shi da tarbiyya wallahi sai na yi shari'a da baban shi, ya karya mini É—a kuma yana zare masa ido"

Aliyu ya janyo ruma daga bayansa, ya tankaÉ—ata gaban babar Asiya, ya ce "Ga ta nan ci ubanta tun da ba ta da kan gado"

Ruma ta din ga kurma ihu tana "Na shiga uku, dan girman Allah kiyi haƙuri, ki yi mini rai babarmu" babu kunya babar Asiya ta taso tana ƙoƙarin make ruma.

Ganin rashin dacewar abin da babar Asiya ke shirin yi ne ya sanya, ɗan sandan shiga tsakani yana bawa babar Asiya haƙuri.
Ta hau ta din ga bala'i a kan ko sisi ba zata yafe ba, sai an biya kuÉ—in maganin da suka kashe.

Aliyu cewa yake "Dan Allah Yallaɓai ka bari ta jibgeta, yadda gobe ba zata ƙara ba"

"A'a gara dai a bata haƙurin, kar karyayyun su zama biyu"

Ihu ruma take yi tana faɗin "Dan Allah babarmu ki yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara ba"

DPO ne ya yi sallama, gaba É—aya hankalinsu ya koma kan sa.

Nan ɗan sandan ya ƙame tare da sarawa DPO.

DPO ya ƙare musu kallo, sannan ya ce "Sannunku"

Aliyu ya ce "Yauwwa Yallaɓai sannu da zuwa"

Ruma ta durƙusa har ƙasa ta ce "Ina kwana"

"Lafiya lau Baby girl, me ki ke yi a nan ba ki tafi school ba, na ganki da uniform?"

Ƙarasowa babar Asiya ta yi, tinkis-tinkis "Yallaɓai, shi ne yaro da ya gaya maka jiya, ya karya mini yaro a school"

BuÉ—e baki ya yi, ya na kallon ruma ya ce "Ke, ke ki ka karya musu 'ya Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ku shigo daga ciki mu yi magana ".

Suka shiga ofishin DPO, ruma sai maƙalewa Aliyu take yi, tana sunkuyar da kai kar su haɗa ido, da babar Asiya.

Tun da suka shiga babar Asiya take mayar da yadda aka yi tana masifa, DPO mamaki yake yadda aka yi ruma ta iya karya wata, ba da abin duka ba da hannunta. Sai da ta gama banbamin bala'inta, sannan ya dubi ruma ya ce "Yarinyar kirki, zo nan"

"Dan Allah ka yi haƙuri kar ka kai ni prison" Ruma tayi maganar tana tauna kwakwa a bakinta.

Yayi murmushi ya ce "Ai ba prison zan kai ki ba, magana za mu yi"

"To rantse" kallon ruma suka yi gaba É—aya, wai DPO take cewa ya rantse.

Aliyu ya ce"Yallaɓai, dan Allah ka yi haƙuri yarinyar ba ta da cikakken hankali, magani ake nema mata"

Ta yi farat ta ce "Wallahi lafiyata ƙalau"

Aliyu ya kai mata duka ya ce "Ni ne nake yi miki ƙaryar?"

DPO Ya ce "Na fuskanta, zo ki ji kin ji baby girl, magana za mu yi" Ruma ta ɗan matsa gaban teburinsa, amma taƙi ƙarasawa in da yake.

"Garin yaya ki ka iya karya mata hannu?"

Ruma ta ce "Ka na kallon wrestling?"

Ya ce "Sosai makuwa"

"To a nan na koyi ƙarfi, kuma yayyena fa maza ne, su bakwai ne ni ce 'yar auta a gidanmu, ina da ƙarfi sosai, irin yadda shemaus yake yi a wrestling na gwada ban zaci ana karyewa ba wallahi "

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kun ga kaÉ—an daga rashin fa'idar kallon irin wannan abubuwan ga yara kenan. to meya haÉ—aki da ita ki ka karya mata hannu?"

"Zane ta yi mini a littafina, na yi mata magana ta yaga min  littafi, na rama, shi ne ta din ga zagina, tana yi mini ashar ni kuma bana zagi, ta ce wai babata tsohuwa, shi ne ni kuma na zana babarsu a allo, ta dakeni kuma aka bani rashin gaskiya, ni kuma washegari na rama, ina ga aljanuna ne suka tashi, na yi mata irin na 'yan wrestling, amma wallahi ban san za ta karye ba, raina ne ya ɓaci sosai"

Headmaster da tun da aka zo bai ce komai ba, sai girgiza kai kawai da yake yi, dan ya rasa me ma zai ce, bai taɓa zaton haka rumaisa take ba.

Headmaster ya numfasa ya ce "Yanzu dai tun da sabga ce ta yara, ayi ƙoƙari a sulhunta kowa ya yi haƙuri"

Babar Asiya kuwa kallon ruma kawai take, yadda take bayani da confidence, tana ciye-ciye kuma aka rasa mai tsawatar mata, sai ma nema ake a goyi bayan ruman.

DPO ya kuma kallon ruma ya ce "Matso nan kusa da ni 'ya ta, magana za mu yi"

"A'a, ba na zama a kusa da maza, Huzaifa ya ce idan ina zama a kusa da maza haihuwa zan yi, kuma korata za ayi daga gidanmu, idan aka koreni kuma ban san in da zani ba, rannan ma Allah ne ya taimakeni, da malam Habibu ya taɓa mini hannu ban haihu ba, mama ta ce lafiyata ƙalau ba ni da ciki".

ba ƙaramin dariya ruma ta basu ba, Aliyu ya dafe kai ya sunkuyar ƙasa, ita ruma ba ta san rufi ba, ko zaka kasheta za ta faɗi gaskiya ne".

Duk yadda aka so yin sulhu, babar Asiya taƙi yarda.
Chapter 32 · 0% Book details