Sashe 107
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon rumaisa kawai yake yana murmushi, yarinya ce ƙarama, ita a yanzu babu abun da yake damunta, sai dai ta yi ciye-ciyenta ta faɗi abun da take ji a ƙwaƙwalwarta shi ne dai-dai, sai dai yanayin yarinyar ya nuna ba za ta yi ƙarya ko ha'inci ba, kuma tana da ɗan karen wayo.
Hajiya Sauda ce ta shigo, sai dai ta yi turus, ganin yarinya zaune a gaban turaki tana cin abinci a kwanonsa, duk da ta bawa ƙofa baya, ba ta iya sanin kowacece ba.
"Mai girma turaki wannan kuma wacece? Meyasa take cin abinci a kwaonka, kwanon da ko 'ya'yan cikinka ba su da wannan damar".
Ɗan turus rumaisa ta yi, amma ba ta waiwayo ba, ta kuma miƙa hannu, ta ɗauko alkaki, tana taunawa tana jin zaƙin sugan har cikin kunnuwanta.
Turaki ya ɗaga kai ya kalli mama ya ce "Baƙuwata ce?".
"Baƙuwarka kuma kamar yaya kenan?"
Ya kalli rumaisa ya ce "Yarinyar kirki, je ki ki kirawo mini takawa"
Rumaisa ta miƙe ta ce "To baba".
Sai a lokacin ta juyo suka yi ido huÉ—u da mama.
Rumaisa ta wani lumshe ido, ta ce "Ina wuni". Kallon banza ta yi wa rumaisa, ta ji gaba É—aya yarinyar ba ta yi mata ba, idonta kawai zaka kalla ka gane tattacciyar mara kunya ce.
Rashin amsawar ta ta bai ɗaɗa ruma da ƙasa ba ta fita falon.
Usman na ganinta ya harareta, sai dai bai tsinke da lamarin rumaisa ba sai da ya ga tana lashe hannu tare da gutsurar wani abu a hannunta.
"Kar dai yarinyar nan ciye-ciye ta je ta zauna ta na yi? Ya tambayi kansa.
"Wai ka zo in ji baba mai rawani" ta yi maganar tana kallon adam ba tare da ta kama sunansa ba.
Bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da danna wayarsa.
"Magana nake maka, ana kiranka"
Still bai amsa mata.
"Takalmawa ake ce maka ko me?, sunanka dai Adamu ba wani Adam ba to ka zo in ji baba mai farin rawani"
Wata irin tsawa aka bugawa rumaisa, wadda sai da ta tsorata, ta kusa faÉ—uwa!
AYSHERCOOL
paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*
A razane ta waiwaya tana kallon in da aka yi mata tsawar, wasu dogarai ne su biyu suka shigo suna baza riga, shigowar ta su yayi dai-dai da lokacin da rumaisa ke gatsali da sunan takawa.
"Hattara dai yarinya, hattara 'yar talakawa, ba a furta wannan sunan hakan babu girmamawa"
ÆŠayan ya juya ya kalli Adam ya ce
"gaba salamun baya salamun, takawarka lafiya magajin saraki, basarake É—an basarake jikan basarake, mai babban suna, takawa magajin takawa, motsawarka lafiya É—an gidan giwar galadima jikar fulanin gombe, ayi mana izinin bata horon yadda ake girmama wannan suna".
Adam ya girgiza kai, tare da É—aga musu hannu, É—an risuna masa suka yi, sannan suka nufi sashin turaki, dan neman iznin shiga wurinsa.
Rumaisa ta ce "Yau na ga masifa, to naga annabawa ma ana faɗar sunansu, sai sunan wani mutum gama gari ace ba za'a faɗa ba, taɓ kun haɗu da wahala, wai wani ƴar talakawa sai ka ce su masu kuɗi ne".
Usman ya ce "Dan Allah maiyasa ba ka saka sun ɗagata sun zaneta da bulala ba? Wataƙila a samu hankali ya shigeta".
"Yaya usy ai ni yanzu na wuce duka yasin, sai dukan ruwa bari na je na gaya wa baba mai rawani ka ce ba zaka zo ba" ta wuce ta koma wurin turakar turaki.
Dogaran nan ta tarar a tsaye, suna jiran iso, amma ta zo ta saka kai zata shige.
"Ke! Ke hattara dai, tsaya a nan ina zaki ba ayi miki iso ba?" Ai ba ta ko tsaya ba, ta daka tsalle ta shige da gudu, ta tsaya tana jiran ko zasu biyota.
"Wallahi tura ta kai bango, abubuwan da ka ke aikatawa sun isa haka, kai ko kunya ma ba ka ji? Ka mayar da 'ya'yanka ba komai ba, sai guda ɗaya shiyasa Allah ya kasheta a wulaƙance, saboda zaluntar 'ya'yanka da kake yi, kuma idan ba ka yi wasa ba, kuma ba ka nemi afuwar yaranka ba, kaima a yadda ta mutu haka za ka mutu.
Ka binne wa mutane gaskiya, kun haɗa kai da giwa da ɗanta sai rainawa mutane hankali ku ke yi, tayaya za ace wannan yar yarinyar ce ta dawo da jariri, ta yaya aka tabattar ɗan aisha ne, wataƙila ma wani abun suka ƙulla, ya haihu da wata aka kashe aisha aka kawo yaron a matsayin nata, ba abun da ba zai iya faruwa ba, tun da dai 'yar ka ce ba tawa ba, matsalar ku ce"
Turus rumaisa ta yi tana bin Hajiya saudat da ido, ta gama zubarta, ta nufo hanyar fita, cikin tsawa ta cewa rumaisa "Ke kuma ban hanya ko na yi gaba da ke" maimakon rumaisa ta matsa, sai ta tsaya tana ƙarewa ƙwayar idon mama kallo, ba tare da tsoro ko shakka ba.
Babu tsammani, rumaisa ta ji an ja ta gefe, an bar hanyar da mama zata wuce.
Hajiya sauda ta yi wa adam wani mugun kallo, ta fice. Rumaisa ta ƙwace hannunta, ta ƙarasa gaban turaki ta ce "Baba, mai ya sa ka tsaya matar nan take maka masifa, kai ba sarki bane ba? Ai ba a ɗagawa sarki murya in ji mama, haka ta ce mini kan mu zo nan"
Turaki ya ce "Yarinyar kirki, sarki a waje yake sarki, amma wani sarkin a gida bawa ya fishi power, kar ki damu zaki gane me nake nufi " ya kalli Adam ya ce "Takawa, Biliyaminu nan sun kawo saƙon 'ya ta, ba sai sun ganni ba, na ta ne a kai mini ita har gida, Allah ya yi miki albarka".
Rumaisa ta ce "To baba dan Allah ka saka baki ya bani ɗana sabir, kaga na gaya maka anty aisha ta bar mini shi wallahi, amma ya ƙwace mini shi, kar na kai shi kotu ne a ga kamar ban kyauta ba, kuma ina ganin girmanku kai da mamansa, amma da wallahi nima kotu zan kai shi wurin alƙali, wata a unguwarmu ta taɓa bawa mama labari wai a kotu an ƙwato mata ɗan ta daga wurin mijinta an bata"
Turaki ya girgiza kai tare da murmushi ya ce "Subhanallah, ba za ayi haka ba, ai mu yanzu mun zama 'yan uwa, za a duba lamarin in sha Allah, saƙonki yana mota Allah ya tsare".
Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce "To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi Allah ya sa ka zama sarki, ka zama shugaban ƙasa baba"
Sunkuyar da kai turaki yayi, yana rife fuskarsa da rawani, dan sha'anin na rumaisa ba ya ƙarewa.
"Wuce mu tafi ina da wurin zuwa" Adam yayi maganar a kausashe.
"Ai ko ba ka ce ba zan tafi, ba sai ka kaÉ—ani kamar wata akuya ba" ta yi maganar tana ficewa waje.
Tun da ta fito usman ke cigaba da aika mata harara ko ta ina, amma ta yi kamar ba ta gani ba, haka suka fita suka hau motar takawa.
Suna tafe a hanya, babu wanda ya kula rumaisa a cikinsu, usman ya ce wa Adam "Ina ga idan muka ƙarasa titi ka ajiyemu, sai mu samu abun hawa mu ƙarasa gida".
Adam ya girgiza kai ya ce "A'a zan kai ku gida, akwai kaya ma, ba zai yiwu in ajiyeku a hanya ba" daga haka suka ɗan shiga taɓa hira suka cigaba da tafiya.
Tafiyar su takawa babu daÉ—ewa, Samha ta dawo, har ta shiga É—akinta ta canza kaya ta fito, ba ta ga gilmawar mama ba, dan haka ta bita É—aki.
Ta iske mama na ta ƙananun maganu, da mita.
"Mama, wai baki san na dawo ba? Ke da waye ki ke ta mita haka ne?".
"Ba dole na yi mita ba, ubanku na nema ta ƙarfin tuwo ya mayar da ni mahaukaciya".
"Ohh mama, kullum cikin case da Alhaji, yakamata ku daina zuwa yanzu".
"Ke dalla rufe mini baki, mai za a fasa? Ai yanzu aka fara ma ba ayi komai ba, na rasa abun da yake shiryawa da shi da adam, sai ɓoye-ɓoye suke yi, da rainin hankali wata shu'umar 'ya ya kawo masa, wai ita ta dawo ɗan wurin aisha daga hannun 'yan bindiga"
Cikin rashin fahimta samha ta ce "Yan bindiga kuma, wasu 'yan bindigar kenan kuma? Ba a can in da take karatun aka ce ta haihu ba? To meya kawo Æ´an bindiga ban gane ba".
Hajiya Sauda ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ke, adam wani abun yake shiryawa, aisha ba wani a ƙasar da taje karatu da ta mutu, a hannun'yan bindiga, da suka yi garkuwa da ita, ta haihu ta mutu a wulaƙance ko gawarta ba wanda ya gani, waya sani ko shi ya cinyeta ko ya kashe ta yayi tsafi da gangar jikinta".
Cikin rashin fahimta samha ta ce "Mama kin yi wa kwanyata dabaibayi da zantukkanki, na gaza fuskantar ko da guda daga ciki, ki yi mini bayani gwari-gwari. Ƴan bindiga ne suka bi ta can suka sace ko kuwa?".
Nam mama ta fayyacewa samha komai, duk da gargaÉ—in da turaki yayi mata a kan hakan.
Salati samha ta yi, tare da tafa hannuwa cike da tsananin mamakin sarƙaƙiya da ruɗanin lamarin, a fili ta ce "Oho musu, ko ma dai yaya ne, a wannan karon nasan babu abun da zai hanani mallakar takawa".
Sheƙeƙe mama ta kalleta ta ce "Wai ke samha wace irin mara zuciya ce ne?, Au ke yanzu duk abun da ya faru da ke a baya, da irin cin kashin da yayi miki baki haƙura da batunsa ba?"
"Dan Allah mama karki ce komai, wallahi ina son sa haryanzu kuma abun da ya faru, ya riga ya wuce, dan Allah kiyi haƙuri ki bani goyon baya a wannan karon na auri adam dan Allah"
"Kin ga tashi ki je, ina da abun yi yanzu".
Samha ta haÉ—a hannayenta biyu cikin magiya ta ce "Please mama".