← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 174

Sashe 148

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba musu ya taka ya ƙarasa, ya sunkuya, ta riƙo rigarsa a hankali ta ce "Iman babu lafiya, kar ku zata da wasa nake yi, kar wani abun ya sameta. Kuma, kuma daga yau ba zan sake baka ko ruwa ba, yau haka aka din ga azabtar da ni, wai sai an yi maka girki kuma ka ƙi ci, to daga yau babu ni babu kai, tun da duka zaka janyo mini, sarki mai koriyar alkyabba " ta ƙarasa maganar tana murmushi. Sai kuma ta cigaba da zabura.

Ya kalleta ya ce "To, na gode, ba za a dake ki ba, zan tafi da abincin"

Ta kuma cewa "Yauwwa, wannan matar, da ta bamu ruwa ni da Sabir, ka tuna ta?"

Adam ya ce "Eh, na tuna"

"To ka san ta ce wai akwai gwagwarmaya a gaba, hmmm ba ka san fa me nake gani ba ko? To in gaya maka, wani abu na gani rannan a gidanku, kuma ma, wani zai je ya É—ebi turarenka baka sani ba, yauwwa har da maganin ka ma da ake shafa maka, ana nema".

Gaba É—aya surutan da take yi babu ma'ana a wurinsu.

Mai sunan baba ya ce "Ya isa haka ki yi mana shiru"

Takawa kuwa ya ce "To, kin gama na tafi?"

"Eh ka tafi, amma fa kana tafe wannan matar tana binka, saboda tsabar taurin kanta, amma da kaina zan mayar da ita gurguwa"

Adam ya ce "Eh yakamata, yanzu dai ki cigaba da baccin, dama ammi ce ta aikoni, zan kira Aliyu a waya mu yi magana"
Ta ce "To" ta gyara kwanciyarta ta cigaba da barci.

Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai, Adam ya ce "To mama sai anjima, Allah ya ƙara afuwa"

Suka amsa da amin, ban da mai sunan baba.
Usman ya ce "Ka tafi da abincin nan, ka cika mata alƙawarin ta".

Adam yayi murmushi, Usman ya bi bayansa.

***
Ko da ya ƙarasa gida, sashin Ammi ya wuce, dan gaya mata abun da ya faru, amma ya tarar ba ta nan, ya fito ya tambayi baba uwani, ta ce "Ai suna tare da iman, tana can tana ta fizge-fizge kamar za ta haukace".

What! Ya faɗa cikin tashin hankali, da sauri ya nufi ɗakin iman, sai dai ya je ya tarar da ita, a kwance tana ta Addu'a, ammi na ta shafa mata ruwa a ka, tana yi mata Addu'a, Nusaiba kuma na riƙe da hannunta.

Da sauri ya ƙarasa yana faɗin "Iman, me yake faruwa?"

Ta miƙa hannu ta riƙe nasa ta ce "Yaya Adam mutuwa zan yi, dan Allah ku yafe mini, nikaɗai na san me nake ji a kaina, baku san me nake ji ba, kaina kamar ana kafa mini ƙusoshi.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya din ga maimaitawa, ya saka hannu ya janye piliown da take kai, ya kwantar da ita a kan gadon, ya din ga karanta mata duk addu'a da ta zo bakinsa, cikin ƙudirar Allah sai barci ya ɗauke ta.

Adam ya ce "Ammi, wai takamaimai me yake damun iman ne?"

"Takawa ina zan sani? Na ga na asibiti sam baya yi mata ma, na rasa in da zan saka kaina ma. To ya aka yi, kun tattauna ɗin, ya ka baro rumaisa? Ina son a satin nan idan iman ta warware a fara haɗa lefe, dan na turawa laila kuɗi, ta yi wasu sayayyar a can ƙasar"

"Babu lafiya" ya faÉ—a a hankali.

Ammi ta ce "Kamar yaya?" Nan ya kwashe komai ya gaya mata, ammi ta yi shiru ta ce "Ikon Allah, Adam akwai aiki ja a gabanmu, babban fatana yanzu shine in ga an yi auren nan, kuma bana fatan a É—aga ko da rana É—aya".

Adam ya jinjina kai Sannan ya ce "Bari na je na ga sabir, daga nan na wuce masallaci".

Tun da ya fita yake ta jujju
***
Rumaisa sai magariba sannan suka samu kanta, ta tashi daga wannan baccin, ba ta iya tuna komai ba, ta cigaba da sabgoginta.
Mama hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, saboda gani take rumaisa aljanu ne ke son su hanata aure. Babu wanda yayi yinƙurin gaya mata abun da ya faru, suka biye mata aka cigaba da harkokin gidan kamar yadda suka saba.

Washegari Ammi ce ta kira mama da kanta a waya, tana tambayarta jikin rumaisa.

Mama ta ce "Jiki da sauƙi hajiya, na ce ko ɗaga bikin nan za ayi, a nema mata magani, alamu sun nuna iskokai suna damunta, kar ayi aure da larura".

"A'a maman rumaisa, Allah zai bata lafiya, wataƙila da an yi auren ta samu lafiya, wallahi kin ganmu nima iman haryanzu jiki yaƙi daɗi, na rasa abun da yake yi mini daɗi, ciwon kai ko sauka ba ya yi".

Shiru mama ta É—an yi, kenan maganar rumaisa gaskiya ce?.

Mama ta ce "Allah ya basu lafiya baki É—aya, in anjima zamu zo mu sake duba jikin nata"

Ammi ta ce "Ba sai kun wahalar da kanku ba, ayi mata Addu'a kawai".

Mama ta ce "Haba, ai babu wannan a tsakanin mu, bari ayi sallar magariba, rumaisa ta dawo daga islamiyya sai mu zo"

Ammi ta ce "To shikenan, ta samu ta ga É—anta ma".

Bayan sun gama wayar, mama tayi ta Addu'a Allah ya sa ba aljanu ne suka buÉ—ewa rumaisa ido ba, take gane-gane.

Da magaribar, tare da mai sunan baba suka je gidan su takawa, rumaisa na ta murna za ta ga Sabir.

Har É—akin iman, aka yi musu izinin shiga, suka tarar da ita kamar mai shirin zarewa saboda surutai, duk suna kanta ciki har da Jabir.

Rumaisa ta ƙarewa ɗakin kallo, ta ce "Mama, ɗakin nan na yi mafarki fa jiya, ku cirewa iman pillown nan, mafarki na yi wata ƴar tsana tana soka mata allurai a kanta, yauwwa ba na ce muku iman ba ta da lafiya ba jiya?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin tuna abun da ya faru jiyan.

Ammi ta ce "Rumaisa a ina ki ka ga Æ´ar tsanar?"

"Mafarki fa na yi, ki dafa pillown, ki karanta mata bisimillah da fatiha, amma dai wata Æ´ar tsana na gani a mafarki"

Abun sai da ya É—aurewa kowa kai, Mai sunan baba kuwa tuni ya bar É—akin, saboda yadda iman take, zaka san tana jin jiki ba kaÉ—an ba.

Ammi ta dafa pillown, ta karanto adduoi, Rumaisa ta riƙe hannun iman tana yi mata sannu.

Jabir ya tashi ya ce "Ammi, bari na je gida, Allah ya bata lafiya"

Suka amsa da Amin ya tafi.

Tattaunawa ammi da mama suka cigaba da yi, ammi tayi ta bawa mama ƙwarin gwiwa, a kan kar a fasa wannan auren.

Bacci iman ta samu, mama ta kalli Adam ta ce "Takawa, kai rumaisa part ɗina, ta ga Sabir, sai ka tambayeta abun da take buƙata na bikin"

Adam bai fiye yin jayayya da ammi ba, balle kuma yanzu da yake a gaban mutane ne, bai ce uffan ba, ya tashi ya fita, rumaisa ta bi bayansa tana murna, jin an ce za ta ga Sabir.

A hanyar sashin ammai, suka haɗu da baba uwani, cikin girmamawa ta risuna ta ce "Takarwarka lafiya magajin galadima, baƙuwa muka yi ne?"

"Eh" ya amsa a taƙaice yana fatan kar rumaisa ta yi wani shirmen, amma ga mamakinsa, ko kallon baba uwani ba ta yi ba balle ta gaishe ta.

Sai da suka yi gaba sannan ya kalleta ya ce "Baki iya gaisuwa bane?"

"Wa zan gaisar?"

"Matar da muka wuce, meyasa baki gaisheta ba? Gidan sarauta ba wuri ne da zaki gwada rashin É—a'a ba, akwai girmamawa da karamci, ko da kuwa kai ne kake gaba da mutum"

Ba kunya ba tsoro ta ce "A hakan? Sau nawa na gaisheka a rayuwar nan baka amsawa, gidan sarautar da watarn wanda kake gaisarwa daban masu amsawa daban, ana ce maka an gaisheka ɗan talakawa, wannan ba wulaƙanci bane ba, ban kula kowa ba balle ayi mini wulaƙanci na ji haushi, ammi da wanda suke amsawa kawai zan din ga gaisarwa"

Wato ya fuskanci ita dai wannan yarinyar, defeating ɗin ta, ba abu ne mai sauƙi ba.

Sai da suka shiga ɗakin ammi, in da babu idon mutane, sannan ya dubeta ya ce "Idan ki ka cigaba da wannan taurin kan, ina gaya miki abu kina mayar mini da martani, zaki yi dana sanin aure a gidan sarauta, dan zai zame miki tamkar kurkuku mafi azaba, kowa zai yi ƙoƙarin yin amfani da ke wurin cimma burinsa, dole ki kiyaye".

Rumaisa ta ce "Na sani, gidan sarauta ba irin normal gida bane, ina gani a film, na indiya da sauransu, daga tsafi sai munafunci, abun ban tsoro, kowa ba abun yadda bane ba, da an ga baka da wayo, sai a cuceka, da ka yadda da wani, sai ya nemi ganin bayanka. Ai ni a duniyar nan kurku mafi azaba ita ce zamana a hannun 'yan bindiga, abu mafi razani kuma ganin mutuwar matar da ta bani kulawa kamar ƴar ta a lokacin da ake yi mini ƙamshin mutuwa. Abu mafi tsayawa a rai shi ne tunanin idan har gawarta tana da muhimmancin da za a kasheta a ɗau gawarta a mota a bar wurin da ita, saɓanin sauran mutanen da ake kashewa wurin, to waye ya saka ayi garkuwa da ita a kasheta, kuma ayi umarnin kashe ɗan ta? Abu mafi ban tausayi shi ne haihuwar jaririn da bai san komai ba, na din ga wahalar da shi da sunan kulawa, har koko na bashi, ya shafe kwanaki da ƙazantar haihuwa a jikinsa, bayan mun kuɓuta a ka yi yinƙunrin rabani da shi.
A tunaninka akwai wani abu mai wahalar mantawa kamar wannan? Ko wani irin ƙalubale ne, zan jure shi na rayu da sabir, kamar yadda na yi wa anty aisha alƙawari, amma ka ƙyaleni a yadda nake, ni ba ƴar sarauta bace ba, lokaci ɗaya ba zan iya zama irin ku ba". Tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta taka a hankali ta ƙarasa gaban gadon Sabir, ya ƙara zama ƙato sosai, sai bacci yake yi.

Takawa kuwa kamar an gina shi, wasu gaɓoɓi ta taɓo masu muhimmanci, amma ya san yanzu da yayi yinƙurin ya cigaba da yi mata maganar, zata koma masa ainihin rumaisanta, ta fara rashin kunya.
Chapter 148 · 0% Book details