← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 174

Sashe 92

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*₦500 ne, via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*

Ammi sai da ta É—an yi jimm, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ita aishan ce ta saka masa wannan sunan?"

Ruma ta ce "A'a, ni na saka masa, sunan babana ne, ina son sunan sosai"

"Ba shi ne sunan da na yi niyyar sakawa É—ana ba, ba zan saka wannan sunan ba" Takawa yayi maganar cike da iko, sai da mama ta É—an ji babu daÉ—i, ko da zai canza sunan bai kamata ya faÉ—a a gaban ruma haka ba, ba za ta ji daÉ—i ba.

"Ka ga ba fa É—anka bane ba, tun da ni ta ce ta barwa shi, É—ana ne Mahmud na saka masa, kuma ba zan canza ba" ta yi maganar tana yi masa kallon banza.

Ammi ta ce "Madalla, suna mai girma da karama, Ubangiji Allah ya raya Mahmud, ta zauna maman baby, mun karɓi sunan" kallon da Ammi ta yi wa takawa ne ya sanya shi haɗiye maganar da yayi niyyar yi.

Ammi ta dubi ruma ta ce "Rumaisa, Haryanzu baki gaya mana ya ki ka baro aisha ba? akwai buƙatar ki bawa Adam haɗin kai wurin amsa tambayoyin da zai yi miki, tun da shi ma jami'in tsaro ne. Yaya Aisha take? Ya aka yi ki ka fito da ke da jaririn babu ita?"

Rumaisa ta ɗan yi shiru tana wasa da gefen bedsheet ɗin da take kai, hawaye ya taru a idonta, sai dai babu tsammani ta yi ƙara tana kare fuskarta da hannunta, da sauri mama ta ƙarasa wurinta tana tambayarta ko lafiya?.

Jikin ruma sai rawa yake yi, ta rungume mama tana ɓoye fuskarta.

Mama ta ce "Rumaisa ki yi magana mana, menene?"
Ruma ta ɗago a hankali tana duba jikinta ta ce "Sha tara ne ya harbe wani mutum jininsa ya ɓata mini jiki".

Jiki a sanyaye mama ta ce "A asibiti fa ki ke a tare da mu, duba ki gani, jikinki babu komai babu jini" mama tayi maganar tana nuna mata rigarta, sai dai duk da haka ruma sai haki take kamar ta yi gudu.

Ammi ta ce "Haryanzu akwai sauran razani a tare da ita, dole ta razana tun da ki ka ga haka, Allah kaɗai ya san abubuwan da ta gani. Bari mu tafi ta samu ta huta, sai dai duk da ban san zuwa yaushe za a salleme ku ba da yaron nan, zan roƙi alfarmar ku, ya ɗan zauna a wurinku kan a sallami rumaisa, muna ƙoƙarin shawo kan wata matsala ne, kan mu kai shi gida kowa ya sani" abun ya ɗan ɗaurewa mama kai, wace irin matsala kenan? Amma ba ta tambaya ba ta ce "A'a babu damuwa, Ubangiji Allah ya raya mana shi a bisa tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam".

Ruma daga kwance ta ce "Ni fa ba wanda zan bawa É—ana, É—ana ne fa".

Ammi ta ƙarasa gaban gadon ruma, ta shafi kanta ta ce "Dama naki ne, aro zaki bamu ai, Allah ya baki lafiya ya tsare gaba" ta yi maganar tana murmushi.

Ruma ta amsa da Amin, daga nan suka yi sallama suka tafi.

Suna tafe a hanya Ammi ta ce "Gaskiya akwai matsala, idan har yarinyar nan ba ta yi bayani ba, dole mu nemi yadda zamu yi"

Takawa ya ce "Ammi, ni fa na riga na gama shirin tarar kowane irin ƙalubale zan fuskanta, na san duk yadda muka kai ga ɓoye lamarin nan, nan kusa zai baiyyana, ko da a yanzu ma kalli a halin da nake ciki, kuma kar ki manta, da dogarai uku ki ka zo wurin nan, a gabansu aka faɗi komai, na san a kowane lokaci maganar nan zata watsu".

Ammi ta É—an yi jimm sannan ta ce "Lokacin da Abokin ka bashir ya yi mini waya, babu halin in fita nikaÉ—ai, kuma ban san kiran me yayi mini ba, wannan dalilin ne ya sanya na tafi da su, kuma jiya na ja musu kunne a kan su yi shiru da bakinsu".

Ya girgiza kai ya ce "Ammi, kin manta gidan nan ne, lokacin da aka fitar da zancen ina shaye-shaye na yi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, mutum nawa ne a wurn, wa zaki kama ki tuhuma ki ce shi ne? Haka wannan ɗin ma, dole zan matsa lamba yarinyar nan ta yi mini bayani, na san in da zan nemi mafita"

Ammi ta yi shiru, abubuwa sai sake cakuÉ—ewa suke yi, ba a warware wannan ba wancan sai ya kunno kai.

"Ammi, meyasa ki ka amince da sakawa yaron nan Mahmud? Ni ba sunan da zan saka masa ba kenan, sunan Alhajinmu na so mayarwa, ni bana son sunan nan"

Ammai tayi murmushi mai ciwo ta ce "Haba babban mutum, ban ji daɗin jin wannan maganar daga bakinka ba, a bar wannan zancen dan Allah, ina roƙa mata alfarma, a bar mata wannan sunan tun da shi take so".

Takawa ya ɗan duƙar da kai ya ce "Tuba nake".

Bayan tafiyar su takawa kuwa Abdallah ne a ɗan hasale ya ce wa ruma "Dan ubanki ba a yi wa masu mulki magana yadda ki ke yi musu, gatse-gatse babu ɗa'a, wai ma ke kowa sa'anki ne da zaki din ga magana son ranki? Na fuskanci ba ki yi laushi ba haryanzu. To wallahi sai an basu ɗan su, ke gama rainonki aka yi da zaki janyo mana wani? Ki kuma cewa ɗanki ne ki ga yadda zan yi da ke" Jin Abdallah kawai take yi, amma gani take idan zasu mayar da ita ƙuli, babu wanda zai rabata da jaririn nan.

Washegari 'yan Katsina su gwaggo da iya, da sassafe suka yi dirar mikiya a Kano, yayin da 'yan uwa da abokan arziki, malaman islamiyya da makarantar bokonsu rumaisa, haka mutane daga lungu da saƙon unguwa, suka din ga zuwa dubiya gami da jajen abun da ya samu rumaisa, sai dai fa unguwarsu rumaisan ta ɗauka a kan jaririn da rumaisa ta dawo shi, nan da nan zantuka kala-kala suka hau zagaya cikin unguwa, masu daɗi da marasa daɗi a kan rumaisa.
Aliyu ya cika alƙawari, ya kawo Habiba har ɗakin da rumaisa take na jinya,ita da babarta, suka rungume juna suka din ga kukan farin ciki.

Gwaggo kuwa sai da ta yi kuka tana neman mama ta yafe mata da ta sanya a ka kai ruma aka ɓoye, ta ɗora alhakin faruwar komai a kan ta, har da su lawisa duk aka zo, rumaisa ta yi farincikin yadda mutane ke ta shiga suna fita duk saboda ita.
Chapter 92 · 0% Book details