← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 174

Sashe 138

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*PAID BOOK NE, ₦500 ME VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

Gaba ɗaya Adam bai san yadda aka ƙare zaman ba, da ƙyar ya tashi ya nufi ɗakinsa, yana neman yayi karo da bango, dan ko gabansa ba ya gani sosai, saboda matsanancin ciwo da kansa yake yi, ga juya masa da duniyar take yi, ga wata irin kururuwa da yake ji a kunnensa.

Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yake ta maimaitawa.

Gadonsa ya laluba ya kwanta, yana ta sauke numfashi, yana addu'a, sai dai kamar a hayaniyar yake jin muryar rumaisa, duk da baya gane me take faÉ—a, daga haka bai kuma sanin in da kansa yake ba.

Bai san iya adadin lokacin da ya shafe a haka ba, ya ji ƙamshin turaren ammi, tana taɓa shi ta ce "Adam wai lafiya kuwa?" Ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ammi.

"Wa meyafaru da kai ne? Tun da turaki ya zo aka yi maganar nan, daga yi masa rakiya, na dawo na tarar baka nan, tun É—azu kake bacci sallar magariba fa ake yi yanzu"

Haryanzu kansa bai daina ciwo ba, ya dubi ammi ya ce "Bacci ne yayi mini nauyi, bari na tashi"

"Ka hanzarta ka rama sallolinka, kar ka sake bari lokaci ya ƙure maka ba ka yi salla ba, sonake mu je gidansu rumaisa, mu sanar musu, yau asabar ka ga nan da kwanaki shida kenan za a kai kuɗin"

Magana yake son yi, amma ammi ta ce "Bana son musu, ka hanzarta bana son ɓata lokaci"

Kawai ya jinjina mata kai, dan shikaÉ—ai ya san abun da yake ji, cikin dakiya ya tashi ya shiga yayi alwala, ammi kuma ta koma falo.

Iman kuwa tausayin rumaisa take ji sosai da sosai, ji take kamar ta sanar musu da abun da yake faruwa, da irin furucin da Samha ta yi.

Sai dai tana tsoron abun da ka iya biyo baya, mussaman yadda Samhan ta ƙware a iya fuska biyu da masifa, dan ita ba ta tausayawa kanta, yadda Samha ta yi zaton ita adam zai aura, kamar yadda take tausayawa rumaisa.

Adam saboda yanayin jikinsa, ya ce wa yaronsa sidi ya kaisu gidansu rumaisa, yayi iya ƙoƙarinsa da jarumta ya danne yanayin da yake ciki, sai dai jirin ya kasa barinsa.

Rumaisa kuwa, tana gida jikin mama tana ƙunƙuni, ta yi wa Huzaifa da Yasir rashin kunya, sun ce wannan satin ba za su wanke mata kaya su goge ba sai dai ta yi abun ta. Mama ta goya musu baya, ta ce "Kar ku wanke mata, tun da ba ta da ta ido, ai yakamata ta fara wanke kayanta da kanta yanzu, ke zaki wanke abunki yau"

Cikin shagwaɓa ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, idan na yi wanki rashin lafiya zan yi"

Mama ta kalleta baki buɗe ta ce "Sangarta mai sanya kifi kukan wanka, samun wuri ne ya sanya ki ke wannan maganganun ma, ke ba dan Allah ya sa da su ɗin ba, ai shekara tara kin fara wankin ki, ko yaushe su suke yi miki, ba kuma dan baki iya ba, dole ki karɓi abunki"

Rumaisa ta sake langaɓe kai ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, ni fa yarinya ce"

"Eh nono ma ki ke sha" ta kwanta a jikin mama tana cewa "Mama dan Allah" mama na shirin ture rumaisa, ruman ta tashi zaune da sauri, ta É—an tsuke fuska.

Mama ta ce "Lafiya kuwa?"

"Kamar baban Sabir zai zo gidan nan, yana hanya"

"Baban Sabir kuma?" Ruma ta jinjina kai ta ce "Haka nake ji a jikina"

Huzaifa ya ce "Iyeee soyayya da ƙauna, bari zamu gani ai"

Rumaisa ba ta iya yi wa Huzaifa martani ba, saboda ji ta yi ƙirjinta ya yi nauyi, jikinta kuma yayi sanyi ƙalau.

A hankali ta zame ta kwanta a jikin mama, ta lumshe idonta.

"Ki tashi bana son barcin la'asar, ki yi shi ki tashi da fushi ki hanamu sukuni da koke-koke da ɓacin rai"
Maimakon ta tashi, sai ta sake langaɓewa, ta riƙe hannun mama.

Mama ta kalli rumaisa ta ce "Ke! Lafiya kuwa?"

Ruma ta jinjinawa mama kai alamar eh.

Mintuna ashirin, sai ga sallamar ammi, mamaki ne ya kama mama, dan ba su yi waya ammi za ta zo ba.

Ta ɓoye mamakinta, ta amsa mata cikin mutuntawa.

Suka gaisa da mama, ammi ta ce "Maman sabir bacci take yi ne?"

Mama ta ce "Rigima dai take ji, wai sai an yi mata wanki, na ce ma ta tashi kar ta yi mini barcin la'asar, ta tashi ta ishi mutane da kukan banza"
Ammi ta yi murmushi ta ce "Haba maman rumaisa, kamar rumaisa idan ba ayi mata wanki ba, ai ba zata iya ba, kar a ramar mini da ita kan ta zo fa"

Suka yi dariya, ruma daga kwancen ta ce "Ammi ina wuni"

"Lafiya ƙalau rumaisa, kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

Ammi ta ce "To masha Allah, tare muke da takawa fa"

Mama ta ce "Ahh kuma ki ka bar shi a waje, Yasir ka ce ya shigo mana"

Ɓoye mamakinsu suka yi, dan rumaisa ta ce ta ji a jikinta yana hanya.

Tun da yayi sallama jikinta ya kuma sanyi, ta rasa menene yake yi mata daÉ—i.

Ya shigo É—akin mama, suka gaisa, mama ta ce wa rumaisa "Ba zaki tashi ki gaishe shi ba?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli Adam sau É—aya, ta kawar da kai ta sake kallonsa na biyu amma ta kasa magana.

Mama ta ce "Ba magana nake yi miki ba rumaisa?"

Ammi ta ce "Wannan Æ´ar tsamar ta su, idan da sabo sun saba".

Mama ta ce "wannan rashin É—a'a ne, ya girmeta, kuma mutumin da zaka aura ka din ga yi masa haka, iskanci ne kawai, ai ba haka take yi wa sauran mutane ba"

Rirriƙe mama ta yi cikin kuka ta ɓoye fuskarta ta ce "Mama baki san me nake gani ba ne"

A rikice ammi ta ce "Me ki ke gani rumaisa, yi mini bayani?"

"Hararata yake yi, idan ya harareni ni tsoro yake bani" haka kawai mama ta ji rumaisa ƙarya take yi, dan ta sha faɗa ita fa ban da fuskar mai sunan baba, babu wata fuska da take bata tsoro.

A zahiri kuwa, a karo na biyu yau ta ga abun da ta gani a tare da adam, kamar yadda ta taɓa gani, lokacin suna asibiti.

Idonsa gaba ɗaya ya koma baƙi ƙirin, babu wannan farin, sai hayaƙi da yake fita, kamar ana kunna itace, a wannan karon har da kamar harshen wuta daga idanun nasa.

Shi kansa adam, cikin jikinsa wata irin rawa yake yi, amma a zahiri yana zaune normal, jikinsa ji yake tamkar ana sassra shi, ba bu wani abu da yake muradi, banda ya shaƙe ruma ko ya riƙe ta, ya samu sassauci.

Ya sunkuyar da kai, mama kuma ƙuluwa ta fara yi, da lamarin rumaisa, dan a ganinta rashin mutunci ne kawai.

Ammi ta ce "Haba rumaisa, shi ne har da kuka, ba hararki yake yi ba, haka yake dai bai fiye fara'a ba, ku da kun kusa zama abu guda ma. Maman rumaisa dama zuwa na yi na gaya muku, a sanar da dangin mahaifinta, ranar Juma'a za a kawo kuÉ—in aure"

Mama jikinta yayi sanyi ta ce "Da wuri haka?"

"Kar ki ce haka maman rumaisa, jinkirin ba shi da wani amfani, kin san mu masaurata ba sa son jira, ayi musu addu'a dan Allah, in sha Allah za a kawo kuÉ—in aure"

Har mama da ammi da suka gama tattaunawar su, babu wani ƙwarin gwiwar cewa wani abu, a tsakanin adam da rumaisa, kowannensu shi ya san halin da suke ciki.

Bayan sun gama magana, suna fita rumaisa ta tubure da kuka ta ce ita fa ba ta so, ba zata aure shi ba, da fari mama ta fara rarrashin ta, ta zaci abun na ta na hankali ne, amma ta ga ba ta da niyyar nutsuwa, ita dai ba ta gaya wa mama, me take gani ba, amma ta ce ba zata aure shi ba.

Shihowar mai sunan baba ce, ta sanya ta É—an nutsu, Aikuwa tambayar da ya fara yi, shi ne meya sameta take kuka.
Mama ta sanar masa da duk abun da ya faru, rumaisa ta zaci yanzu ma zai turje, sai ji ta yi ya ce "Allah ya tabattar mana da alkhairi, nan kano zasu kai, ko can katsina?"

Mama ta ce "Wai da su kai wa kawunku na mandawari, ba sai an wahalr da su ba"

Mai sunan baba ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu"

Cikin kuka rumaisa ta ce "Mai sunan baba ni fa na fasa bana son shi".
Chapter 138 · 0% Book details