Sashe 160
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya saka hannu ya karɓi ledar ya ce "Godiya take, kin san amaryat ta wa akwai jan aji, da gudun raini, kyauta ko da ga ni take, sai ta tantance, gaku sarakai, amma ta fi ku sarauta" yayi maganar a baibai, cike da mayarwa da Hajiya Lubabatu martani.
"Ikon Allah, da alama auren haÉ—i zai koma na soyayya, ai labarin zuciya a tambayi fuska takawa".
Adam ya ce "Eh to, ba zan musa miki ba, amma hausawa suka ce É—an hakin da ka raina.."
Murmushi kawai hajiya Lubabatu ta yi, tana yi musu su gaida gida. Rumaisa tuni ta yi waje, dan idan ta cigaba da tsayuwa, matar nan tana washe baki, tana gaya mata magana, ba abun da zai hana ta zageta.
Shi kansa adam mood ɗin rumaisa ya gani, ya san a ƙule take kamar ta fashe dan takaici, la'asar ta riga ta yi sosai, ya ga idan suka koma gida, shi ficewa zai yi, ya san zama za ta yi, tayi ta ƙunci a gidan, dan haka ya wuce da ita da ita gida.
Ammi ba ta nan, sai Nusaiba da Iman, da kuma Sabir, ganin Sabir ya sanya ya manta wani ɓangare, na fushin da take yi.
Ba ta fiye shiri da Nusaiba ba, ta fi yi da Iman, dan haka da ita suke ta hirarasu.
Iman ta saka aka kawo musu abinci, nan iman take bata labarin, bayan ta dawo gida mai sunan baba ya kirata, ya ga missed calls É—in ta, a lokacin take gaya mata, yadda suka yi da shi, da ta kira shi tana tambayar sa, ina take.
Ruma ta din ga dariya ya ce "Baban mama, sa ba ka dariya sai hamma, kirarin da mama ke yi masa kenan, shi dai kar a raina shi".
Iman ta ce "Anty rumaisa gara haka fa, ina son in ga namiji mai aji, rashin kintsi ko ga namiji bai yi ba ai". Suka cigaba da dariya, iman na nunawa rumaisa hotunan biki.
Nusaiba kuwa kallon iman take, yadda fuskarta take nuna jin daÉ—in hirar mai sunan baba da suke yi.
Nusaiba a ranta ta ce "Iman, wannan ba irin mutumin da ya dace ki so bane, ya fiye zafi, larurarki kuma tausasawa take buƙata, kuma wataƙila ba zai amince da ke ba, idan ya san ke wacece, uncle J ɗin dai, shi ya san k wacece, shi zai iya zama da ke, wannan wahalar sarrafawa zai yi miki'.
Ana idar da sallar magariba, Adam ya dawo, ya ce rumaisa ta tashi su tafi, ta ce ya bari ta ga ammi, ya ce a'a so yake ya je je ya huta, haka ta tashi ta bishi, sai dai suna barin gidan, ta tuna abun da ya faru yau, ta ji ɓacin ran ya dawo mata.
Ko da suka je gida, baba uwani ce ta fito tana yi musu maraba, sauran hadiman sam ba sa abun da take yi, rumaisa har mamaki take yi, kawai yau sai ta din ga ganin dariyar baba uwani, kamar dariyar hajiya Lubabatu da ta din ga yi musu É—azu, tana yi musu dariya, kuma tana ci mata mutunci.
A ƙasan benen ta bar shi, shi da baba uwani, ta hau saman benen ta wuce ɗakinta, ta shiga banɗaki, ta duba pad ɗin jikinta, tana fatan ta ga babu komai, dan ta gaji da zubar da jinin yake yi, amma ta ga ɗan kaɗan, kuma adam ya ce mata, idan ba ta saka, ta ga babu abun da ya zuba a kai ba, kar ta kuskura ta ce za ta yi salla, dan kamata yayi tana salla washegarin da period ɗin ya zo mata.
Ta yi wanka, ta canza wata, ta saka kayan barcinta Æ´ar rigarta sai wando, ta hau kan gado ta baje, dan ta gaji.
Ba ta yi tsammani ba, bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari da safe, rumaisa da kanta ta sauka kitchen ɗin ƙasa, ta tarar da barira da Asiya, suna aikace-aikace.
Suka hau gaida rumaisa ta ce "Ni fa ku daina gaishe ni dan Allah, kunya ku ke bani, doya zan É—auka".
Asiya ta ce "Wani abun za a girka miki ranki ya daÉ—e".
Ta ce "A'a, ni zan yi da kaina.
Ta É—auki abun da take so, ta koma.
Ta yi ta gyare-gyaren ta, sai dai abubuwan da suka faru jiya, suka cigaba da damunta.
Ta saba Adam da wuri yake tashi ya fita, ta samu ta gyara É—akin, amma ta ji shi shiru. Dan haka kai tsaye ta nufi É—akinsa ta shiga babu ko sallama.
Sai dai tozali ta yi da shi a tsaye, daga shi sai gajeren wando, ya ajiye towel a gefen gado alama wanka zai shiga.
Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka saka kayanka, zan yi gyaran É—aki, ko ka fito waje, idan kuma ka yafe shikenan".
Girgiza kai kawai ya yi, ya ce "Zo ki gyara".
Kanta a ƙasa ta shiga, ta fara kwashe kayan duk da ya barbaza tana mita. "Wai sai ka ce wani Sabir, komai sai ka watsar da shi" bai ce mata uffan ba, ta cigaba da mita.
"Ga kuÉ—inki nan a kan mudubi, 100k ne, hajiya Lubabatu ta baki jiya".
"Allah ya kiyaye, ba abun da zan yi da su, ka ɗauke ni ka kaini, ana ci mini mutunci, amma nayi-nayi ka ƙi ka kaini gidanmu na ga mama. Wallahi matar nan ba dan ta kusa zama tsohuwa ba, babba ce da sai na yi mata rashin mutunci, ina fa gane baƙar magana, shi ma wannan Jabiru yake da wannan ɗayan, suka din ga ce mini wannan abar. Ni na tsani wannan jabir ɗin, shi kuma ɗayan mai kama da mugwaye. Ita kuma wannan matar har da ce wa, wai ni ba mace ba ce, Hansai take ko Hasana, duk kana ji ana ci mini mutunci.
Ta manta ai ni dama ƙanwar maza ce, a namiji aka haifeni, sai da ga baya da na fara girma aka lura ashe ni mace ce, ni na ce kar ka aureta da za a din ga zagina? to wallahi ba ruwana da wata masarauta, duk wanda ya yi mini, sai na rama, a wayance matar nan ita ma tana nufin, ni ƴar talakawa ce na aureka saboda kana da kuɗi fa take nufi, ba ta san taimaka wa na yi na aureka, saboda ammi ba da kuma Sabir" sosai take masifa, domin dama, dama take son ta samu ta amayar da abun da yake ranta.
Takowa ya yi zuwa gabanta, tana tsaye a gaban mudubi, sai iya shege take yi, tana masifa.
Sai kuma tsoro yakamata,ba yau ta saba ganin namiji ba riga ba, idan da sabo ta saba a gida, amma ganin adam a haka, ya sanya take jin, tamkar ta aikata wani jibgegen saɓo.
"Ke dama mace ce nan a haka?" Ai ba ta san lokacin da ta É—ago ta kalleshi ba.
Ya janyota gaban mudubin sosai ya, ya cire hular kanta, gashin nan na ta baƙi wuluk, ta yi parking ɗin sa. ya ce "Wannan ɗan gashin naki ne kawai zai sa a san ne ba namiji ba ce ba, kamar namijin haka ki ke ai, taimakawa na yi na aureki, dan ba yadda zan iya, amma kalleki fa sosai a mudubi" yayi maganar yana nunata a cikin mudubi.
ÆŠaga kai ta yi tana kallonsa.
Ya ce "Eh mana, ke ba kwalliya ba, ke dai gaki nan, behaviors ɗinki ma na mazan ya rinjayi na matan. Wasiƙar da ki ka rubuta mini, ki ka ce na taɓa miki nono ni ban gansu ba ai.
Kawai da ma sharrinki ne, abun bai fi girman wake ba, wata ƙwaila da ke, ai ba ƙarya aka yi ba, dole kowa ya tausaya mini, look at you.
Da ma na ce nawa sun fi naki baki yadda ba, look at me, bai fi naki ba?" Yayi maganar yana shafa ƙirjinsa.
Rumaisa ji ta yi tamakar ƙasa ta tsage ta nutse, sai ta nemi duk wasu kalaman rashin kunya, da fitsararta, ta rasa, ta rasa me ma za ta yi, ta saka hannu ɗaya ta rufe ƙirjinta, ɗaya kuma ta rufe fuskarta.
"Meye a wurin da ki ke rufewa, abu fayau kamar filin ball, ni aure zan yi nan gaba kaÉ—an, dan da gaskiyarsu, ba mace ba ce ke, haryanzu dai namijin ce, ba a gama tantancewa ba, macen ce ko namiji, ga rashin kunya, ga fitsara da faÉ—an tsiya, duk ke kaÉ—ai, ba zan iya É—auka ba da wanne zan ji?".
Dummmm haka rumaisa ta ji maganar, jin ya ce wai zai ƙara aure, saboda ba ta da nono, idan ba batsa ba, meye haɗin sa da wannan abu?.
Gaba É—aya jikinta yayi sanyi, ta ma rasaa wani muhallin, yakamata ta ajiye wannan maganganun da adam yake yi mata, ba tare da kunya ko tsoro ba.
Ya kuma haÉ—e rai ya ce "Wuce toilet ki haÉ—a mini ruwan wanka"
"Ruwan wanka kuma sai ka ce wata baiwa?".
"Ba zaki wuce ba kenan?"
Kamar ta saka ihu, haka ta tafi tana ƙunƙuni, ya bi bayanta, ta shiga banɗakin, sai dai ba ta san yana ƙofa a tsaye ba.
A Tsakiya banɗakin ta tsaya, ta riƙe ƙugu, cikin ƙwalla ta ce "Lallai ma, wai ni rumaisa ake yi wa wannan abubuwan, wallahi da sake". Idonta ya sauka a kan toothpaste ɗin da adam yake amfani da shi, a wani tube mai kyan gaske.
Ta ɗauka ta buɗe, ta lakata ta saka a bakinta. "Dan mugunta ni ya bani mai yaji, shi kuma nasa mai zaƙi, saboda ga wadda dauɗa ta kashewa haƙora, ban yafe ba duk abun da yake mini".