← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 174

Sashe 8

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce "Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki leɓe kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki roƙi Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi" kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ɓingirewa ta kwanta.
Aikuwa mama ta ƙule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta miƙe tana sosh-soshe.
Mama ta bata riga da É—an kwali ta É—aura, ta korata tayo alwala.

Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla.
Kusan mintuna arba'in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfiÉ—arta taga bata wurin.
Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta.
Lelleƙawa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?" Tayi maganar lokacin da ta ƙarasa soro tana haska fitila, amma taga ƙofar gidan a rufe.

Ƙofar ɗakin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ɗan ƙarfi.
Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce 'Mama lafiya kuwa?".

Cikin tashin hankali ta ce "Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa".

Ƙwalalo ido waje yayi, ya ce "Ruman? To ina ta tafi?"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, na duba ƙofar gida tana rufe da sakata ba a buɗe ba"

Mamaki duk ya cika Usman ya ce "To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a buÉ—e gidan a dudduba".

Ya shiga cikin É—akin, ya kunna wutar lantarkin É—akinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.

Kunna fitilar ne ya sanya Huzaifa ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji mutum a kusa da shi, yayi zaton Yasir ne, dan haka ya dage ya hankaɗa Rumaisa, ta kifa kan Yasir amma ba ta farka ba.

Usman Ya ce "mama leƙo kiga"
Jiki na rawa mama ta shiga É—akin, daidai lokacin da Yasir ya ji nauyi a kansa shi ma ya dage ya hankaÉ—ata gefe guda.
Mama ta shiga tafa hannuwa tana salati, a irin magagin bacci, da shirme na Rumaisa tsaf za a saceta tana wannan baccin na asara.
A ƙufule Huzaifa ya tashi yana zage-zage ya zata Yasir ne yake damne shi, amma ya ga Ruma a tsakiyar su, ga su Mama a tsaye.

"Ke uban me ki ke yi a É—akinmu, mama meyafaru?"

Jin hayaniya ya sanya Sadik ma farkawa, ya dinga kallonsu É—aya bayan É—aya 'mama lafiya kuwa'.

'lafiya lau, kai Huzaifa taso mini ita'
Abubakar ya kalli in da Rumaisa ke ta more laushin katifa tana barci.
"Wai me ya kawo yarinyar nan É—akin nan?"

Usman yayu masa bayani kamar yadda Mama tayi masa.

Sadik ya ce "Kai Huzaifa, kai da Yasir ku sauko ku bar mata katifar dan Allah, wannan ba tashi zata yi ba"
Yasir ya ce "Kaii, Yaya haryanzu fa yarinyar nan tana fitsarin kwance, kawai a tasheta ta fita, kar ta tsula mana fitsari dan katifar nan wuyar bushewa za ta yi".

Yaya Umar kuwa tun shigowar Rumaisa yana kallonta, lokacin bai daÉ—e da kwanciya ba, ya ganta ta shigo tana tangal tangal, ta nemi wuri ta kwanta, tun da ta shigo yana kallonta.

Mama ta ce "Ba zata kwana a nan ba, taso mini ita ta wuce mu tafi".

Yasir ya daddaki Rumaisa a kafaÉ—a, amma ta hau surutai da irin faÉ—ace-faÉ—acen da suke yi da yara a makaranta.

Ƙarshe haushi ya ƙule, Umar ya tashi danƙo Ruma ya hankaɗowa Mama ita tsakar gida, ya rufe musu ƙofa.
Mama har mamakin wannan magagi da kuma suratan baccin da Rumaisa take yi, ita duk wani da mutane suke yi, nata ya zarta ƙa'ida.
Har mama ta kama hannunta zuwa É—aki, magagin bacci take yi.

******
Sassanyar iskar da bishiyoyin ke bayarwa ne ya haɗu da ƙamshin furanni, tare da samar wani kyakkyawan yanayi mai sanyawa zukata nutsuwa da annashuwa.

Duk da wannan tarin ni'ima, gaba É—aya Samha ba ta jin dadin yanayin sam.
Wayar hannunta ce ta fara ringing, wadda ta katse mata dogon tunanin da take yi, É—agawa tayi ta kara wayar a kunneta ba tare da ta ce komai ba.
"Ki fito mu tafi, ina haraba".

"Ok, ya maganar mu? Kun yi magana da ita, zasu zo ne".
Nusaiba ta ce "Hmm, Samha kenan ke meya hana ki tambayeta?"

"Nusaiba bana son wasa, am serious about it".

Nusaiba ta ɗan taɓe baki ta ce "Eh, za su zo" Ta sauke wayar daga kunnenta, ta nufi hanyar fita daga lambun.

***
Mama tana yawan yin istigfari da nemawa Rumaisa shiriya, musamman yadda bakin mutane yayi yawa a kanta, duk wani rashin ji irin na ɗa namiji shi take yi, bama irin na mata sa'aninta ba, duk sa'aninta ta kere su a rashin ji. Babu yadda Mama ba tayi ba a kan aje a bawa malaman makarantar allon su haƙuri, ta koma amma mirsisi Yaya Umar ya ce sai dai a sauya mata makaranta, in da zata fi mayar da hankali, amma a ƙasan zuciyarsa zafin maganganun da malaman suka yi a kan Rumaisa ne ya fi ɓata masa rai har ya sanya ya ce ba zata koma ba.

Ita kuwa Rumaisa ganin Yaya Umar ya hana a mayar da ita makarantar allon Malam Babba, tayi ta murna a ganinta ta huta da zuwa makarantar nan mai cike da takurar tsiya, Allah ya sa makarantar bokon ma a cireta, ta dawo gida Mama ta bata jari ta dinga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida. Murmushi ta yi bayan wannan tunanin ya zo ranta.

Ta dubi Abdallah da yake ninke kayan da ya wanke ta ce "Yaya Abdallah, dan zaka gayawa abokananka zan fara sayar da wainar fulawa, naga kai ne me abokai masu kuɗi, ka talatta musu su zo su dinga saya, ba irin abokan su Huzaifa ba gayyar ƙolawa da tsamaye ba"
Saroro ya kalleta ya ce "wace irin wainar fulawa kuma?"

"Eh tun da na daina zuwa makarantar allon, sai Mama ta bani jari na diga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida".

Huzaifa ya ce "Eh dama kin yi kalar sayar da wainar fulawar ai, ai ni da kai na zan din ga yi miki ciniki, ai suyar wainar ce ta dace da le delu"

MurguÉ—a baki tayi ta ce "Da dai ban san halinka bane, ci ka tsere ka rusa mini jari, kama kar ka sake ce mini wata deluna gaya maka.
Ta mayar da hankalinta kan Abdallah ta ce "Dan Allah Yaya Abdallah ka yi magana mana".

"To ai Ruma na rasa me zance miki ne, wace irin wainar fulawa ana zaman lafiya".

"To Yaya ba gara ace ina sana'a ba, kuma ku huta ba, ana ta shelar mata su kama sana'a, Mama ai zaki bani jari ki saka mini albarka ko?"

Mama ta ce "kada Allah ya nuna mini wannan rana, kuma kar ki sake sakoni a cikin shirmenki, idan kuma ki ka sake sai na ci ubanki ke da soya wainar fulawa a ƙofar gidan, tun da ke dai Allah bai sa an raba hankali kin samu ba" ɓata fuska tayi a ranta ta ce 'sai na tambayi Yaya Abubakar, na san shi ba zai hana ni ba ai, tun tuni ake cewa mata su kama sana'a ni kuma zan yi ana hanani'.

Umar yana ɗaki yana jin shirmen da Ruma take, ji yake kamar ya ɗauketa ya kai ta boarding kowa ya huta, amma ya san Mama ba zata taɓa amincewa ba.

Wayewar garin Allah, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe, mama na shirin fita, telar da take yiwa Mama ɗinki ta aiko da ɗinkin da Mama ta kai mata, bayan mama ta karɓi ɗinkin ta sallami yaron, ta kalli Ruma ta miƙa mata ledar ta ce "gashi nan kayanki ne".

Da murna ta karɓi ledar ta buɗe, cike da son ganin menene a ciki.
Tana buɗewa tayi karo da wata atamfa koriya da yellow, ta kalli Mama ta kalli atamfar sannan ta ce "Wallahi Mama wannan Salamatu mai kayan ba ta kyauta mini ba, sai da nace ba na son atamfar nan, amma dan taga ba na nan shine ta liƙa miki, ki ka saya amma shikenan na gode, amma dai ba dan an ɗinka ba sai na mayar mata" ba ta gama rufe baki ba, ta buɗe kayan taga riga da zani jaka a tsaye, da wata uwar bunjumemiyar riga kamar zata tashi sama.

"Ta kalli mama ta ce "Mama wai wannan kayan nawa ne ko kuma naki?" Ruma tayi maganar a rikice.

Mama ta ce "Ni ce zan saka wannan kayan? Naki ne mana"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu mama wannan ne kayan salla na, dan Allah kalli rigar tsaf sai an saka irina sittin a ciki, mama ko gwada ni fa ba ayi ba aka É—inka kayan"

A fusace Mama ta ce "Naji na gode, ki ajiye mini kayana tunda ba ayi miki gwaninta".

Yasir ne ya dubi Ruma ya ce "Amma Ruma baki da kirki, yanzu mama ta sai miki kaya ta bayar a ɗinka miki, amma ƙiri-ƙiri ki nuna ba kya so".

Mama ta ce "Rabu da ita, ta je ta ƙarata".

"Mama kiyi haƙuri, ba cewa nayi bana so ba, amma dan Allah kalli rigar nan, ni ba tattabara ba ina zani da wannan rigar kalli hannun kamar fuka fukai, ba irin wannan rigar na gani a jikinku a wannan tsohon hoton naku ba?"
Yasir ya karɓi rigar yana dubawa, ƙunshe dariyarsa yayi ya ce "To dan ubanki maje gaba aka yi miki, tun kina yarinyarki da ke, wato kin fi son matsatsun kaya ko, to baki isa ba, wannan rigar da ita zaki yi wankan idi mu je masallaci, maje gaba ce "
Haushi ne ya gama cika Ruma, ta tura baki tana jin kamar ta yi ihu.

"Wace irin maje gaba, ai sai a bari nayi gaban tukuna, sai a É—in ka mini daidai ni, idan ban je gaban ba fa?"
Chapter 8 · 0% Book details