Sashe 143
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke ki ka nema musu kuÉ—in, ido a kwabo" Yaya Abubakar yayi maganar yana dungure mata kai.
Aliyu ya ce "Mama, bana tunanin wannan abun ya kai a fasa aure saboda shi, dama rumaisa na buƙatar tsayayyen namiji jajirtacce, saboda halinta, sannan shi mutum ne fitacce, irin wannan sharrin ba abun mamaki bane ba, ban ƙaryata b kai tsaye, amma ke ki ka gaya mini addu'a da ki ka din ga yi, kina jin son abun a ranki, lamarin ya kwanta miki a ranki, da bai kwanta miki ba sai mu ce babu alkhairi, dan babu hijjabi tsakanin addu'arki gareta da Allah, a ganina mu cigaba da addu'a babu ma'ana a kawo wannan zancen ma, tun da ai ita ma rumaisan tana son sa ko?"
"A'a nifa ba son shi nake yi ba, kawai saboda a bani Sabir ne".
"To amma ai ke ki ka ce mai kuÉ—i ki ke so, kuma mai kyau wanne ne bashi da shi a ciki?"
"Wannan har wani kyakykyawa ne? Kullum yana wani zazzare ido"
Mama ta ce "Tashi ki bar wurin nan, mara kunya, ana maganar aurenki kina tsoma baki"
Aliyu ya ce "To sanin ma'anar auren ma ta yi? Amma mama ya kike gani? A kan wannan dalilin zaki saka a É—auki kuÉ—in da aka kawo shekaranjiya a mayar musu ne?"
Abubakar ya ce "A'a ba ayi haka ba, na gamsu da maganganunka nima, mu cigaba da addu'a dai, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi"
Mama ta amsa da Amin, sannan ta tashi ta saka Yasir a gaba suka tafi kasuwa.
Likitoci suka karɓi iman, kasancewar asibitin sun san matsalar Iman, nan da nan suka karɓeta.
A duk lokacin da ciwon ya tashi, Asibitin ake kawota, tun tana yarinya abu kaɗan sai ta yanke jiki ta faɗi ta suma. Aka din ga binciken abun da yake damunta har ƙasar waje, ƙarshe dai aka ce zuciyarta ce ke kumbura wasu lokutan.
Ammi ta alaƙanta hakan, da yawan damuwa da take yi, mussaman a lokacin yadda ake tsangwamarta, hakan ya sanya hankalin ammi ya tashi sosai.
Ta din ga faɗi tashi, domin ganin iman ta samu lafiya, tayi iya ƙoƙari iman ta samu sauƙi, sai dai lokaci zuwa lokaci jikin ya kan motsa.
Yanzu haka ammi hankalinta ya tashi, ba ta ƙaunar ganin wani abu ya sami iman, shiyasa kullum cikin addu'a take yi mata, Allah ya sanya iman ta samu miji nagari, wanda zai iya haƙuri da ita ya jurewa larurarta.
Sai dai a wannan karon, su kansu likitocin lalube suke yi a cikin duhu, ake ta bankawa Iman ruwa da allurai, aka yi hoton zuciya, amma zuciyarta lafiya ƙalau.
Hajiya Sauda ce zaune a turakar turaki, ta dube shi ta ce "Ranka ya daÉ—e, ni baka gaya mini ina ku ka je ba ranar juma'a, ka zo mana da abubuwa na ciye-ciye, haryanzu baka ce mini komai ba"
Turaki da yake cin ayaba, ya ce "Dama dole ne duk in mu ka je sai an gaya miki?"
"A'a tambaya dai kawai na yi, na zaci wani abun alkhairin ne ya samu ai"
Ya ce "Eh, kusan haka, abun farincikin ne"
"Kamar me fa?"
"Aure muka je nemawa takawa, na gidan galadima"
"A'a, neman aure kuma, yaushe Aishan ta rasu, da har za a nema masa wani auren?"
Turaki ya ce "Addini ya bashi dama, Aisha ta kai watanni huÉ—u da rasuwa babu laifi a ciki dan yayi wani auren".
Danne fushinta ta yi, ta ce "Amma wa zai aura haka da na ji ka ce, kun je nema masa aure".
"Eh, wata yarinya ce, Æ´ar mutunci iyayenta masu dattaku sosai, su suka bamu wannan kayan duk da na zo da su".
Cikin son bugun ciki ta ce "Kuma Æ´ar waye? Ai na zata iman zaku aura masa, ta maye gurbin aisha"
"To, idan lokaci yayi zaku ga koma wacece, koma itan ce, ko ba ita bace ba"
"Amma dai Allah ya baka yawan rai, ni na rasa dalilin da ya sanya, ka fi fifita ƴaƴan wasu a kan naka, na rasa me muka yi maka da ni da yarana. Tsakani da Allah duk yadda Samha take ƙaunar yaron nan a wannan karon ba zaku yi mata adalci ta maye gurbin aisha ba, taƙi auren kowa ta dage sai shi, amma ka yi burus, ku ke je waje nema masa auren wata?"
Turaki ya ce "Ban fifita kowa a kan ƴaƴana ba, sai dai son da nake yi wa ƴaƴana, ba zai sanya na zaɓi son zuciya ba. Ba zai yiwu sun kawo wadda suke so ya aura na wuce masa gaba a matsayina na ubansa, na yi amfani da ƙarfin ikona, na ce sai ya auri ƴa ta ba, ki sani zan iya tursasa shi ya auri ƴa ta, amma ba zan iya tursasa shi ya so ta ya kyautata mata ba, na yi mata nasiha tun ba yau ba, a kan ta haƙura da shi, ta yi addu'a ta nemi wani ta aura, har haɗata da na yi da ɗan gidan madaki, Muhammad Sani, ya ce ya na sonta ta watsa mini ƙasa a ido, sai yanzu kuma ku ce ga abun da ku ke so sai na yi, ba zai yiwu ba, kuma ku yi haƙuri, da Samha da takawa duk ƴaƴana ne, ba wanda zan yi wa dole a kan wani abu da yake son zuciya"
Ba ƙaramin ƙuluwa ta yi ba, da jin maganganun turaki, ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta bar ɗakin.
Zainab ce ta shiga falon mama, in da Samha ke zaune tana kallon tv, hannunta riƙe da wayarta, ta zauna tana faɗin "Ohh God, ita wannan yarinyar ita kenan kullum cikin ciwo?"
Samha ta kalleta ta ce "Wacece?"
"A status É—in Nusaiba na gani, wai iman babu lafiya, ba ta san waye a kanta ba ma, shikenan ita giwa kullum tana hanyar asibiti saboda Æ´ar tsintuwa, dama ta mutu ko sa huta gaba É—aya"
Samha ta yi ajiyar zuciya, tare da ji a Jikinta, aikin ta ya fara aiki kenan.
Fuuu mama ta shigo falon,. Kamar mai tafiya a kan iska.
Duk suka bita da kallo, suna tambayar ko lafiya?.
"Hmm, ni da turaki mana, ya gaggaya mini magana a kan kawai na ce, meyasa bai saka adam ya auri Samha ba, wai nema masa aure suka je yi ranar juma'a.
Ƙuuuu Cikin Samha ya bayar, wani irin fargaba da faɗuwar gaba ya kamata, neman aure aka je yi wa Adam?.
"To kin ji, a wannan karon dai kya haƙura ko?" Zee ta yi maganar tana kallon Samha.
"Mama, neman aure kuma? Ba iman za su bashi ba?".
"Bana tunanin ita ce, wata ce daban gaskiya, tun da ya ce sun je nema masa ne, da ita ce ai ba sai sun yi haka ba"
Wani irin gumi ne ya shiga ratsowa daga cinyar Samha, gaba É—aya kanta ya toshe, saboda jin abun a bazata an shammaceta da yawa.
"Amma mama wacece haka?"
"Oho ina na sani, bai gaya mini ba, ni takaici ma bai barni na san wacece É—in ba".
Cikin hanzari, ta tashi tafi ɗakinta zuciyarta na yi mata zafi, tsabar wulaƙanci a waje ma ake je aka nema masa wata bayan ita gata a zaune an san tana san shi
Zama ta yi daɓas a gefen gado, zuciyarta na ƙuna, wannan shine baba na ɗaka gemu na waje, amma mayar da ita wata sako tumaki ɓallo jakai.
"Tun da naga aikin malamin nan yana aiki, Adam da ni ka ke zancen, wallahi kana ji kana gani sai an mayar da kai mace, ba zaka amfani kowacce mace a rayuwar aure ba, sai dai ta kalleka ka kalleta, amma kai da sake kwamciya da wata matar, har abada sai dai idan ni ka aura, zaka gane baka da wayo".
***
Mai sunan baba yana tsaye a kitchen, yana kwashe abinci, kasancewar mama bata nan, babu kowa a gidan, mama tana kasuwa, sai shi da ya dawo gidan yanzu, yayi saurin É—ora girki, dan ya san tsaf rumaisa zata dawo a kowane lokaci idan ba a gama abinci ba, idan ta din ga kwanciya tana kuka, sai ta saka ya daketa. Ga lokaci ya riga ya ja.
Mama ce ta kira shi a waya, ya É—aga yayi sallama.
Ta amsa sannan ta ce "Babana kana ina ne?".
"Na dawo gida, na É—ora girki ne".
"Yauwwa, dan Allah idan rumaisa ta dawo, ka saka ta yi wanka ta yi salla, ka tafi da ita asibitin da ta kwanta, an kwantar da iman ku wakilceni ku dubata, yanzu muka yi waya da hajiyar, wai an kaita asibiti ba ta san waye a kanta ba, ni kuma bana tunanin zan dawo da wuri".
"Tom" ya faɗa a taƙaice ya ajiye wayar, ya cigaba da aikinsa.
"Assalamu alaikum" rumaisa ta yi sallama, sai dai kan ya amsa ta fara cewa "Wani gardin ne yake yi mana abinci yau, Allah ya sa yayi daɗi, na ji ƙamshin miyar har tsakiyar kaina, Allah yasa ko shinkafa an gama, in fara rage hanya, dan yunwar da nake ji ba a cewa komai" ta ji shiru ba a amsa ba, ta nufi kitchen ɗin tana cewa "Baƙon aljani muka yi ko kurma, da nake magana aka shareni".
Tozali da tayi da shi ne, ya sa ta ci wani wawan burki, rabon da yayi girki har ta manta, dan haka ba ta kawo shi ne ba.
"Yi haƙuri, ban san kai ne ba, dan Allah ka yi haƙuri"
Kifi yake sakawa a miyar, ba tare da ya kalleta ba, sum-sum ta bar wurin ta koma É—aki ta kwanta.
Mai sunan baba bai tashi gaya mata saƙon mama ba, sai da ta fara shirin islamiyya, ya ce "Na gaya wa shugaban makarantarku ba zaki shiga ba yau, zamu je dubiya"
"Ina?" Ta tambayeshi tana kallonsa, sai dai ta manta shi mai sunan baba, idan ya ce ayi kawai ayi, ba tare da tambayoyi ba.
Har suka tafi dubiyar, mamaki take yi, waye babu lafiya, ta lissafa wannan ta hango wancan, amma ta kasa gano waye babu lafiya.
Sai dai ba ta ƙara sarewa da al'amarin ba, sai da ta gansu a asibitin da aka kwnatar da ita.