← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 174

Sashe 90

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Abubakar ne ya shigo, yana dira daga tasha ya wuto asibitin ba tare da ko gida yaje ba, da gudu ya ƙaraso ya rungume rumaisa, ko sauran mutanen da ke ɗakin bai kalla ba, ya rungume rumaisa yana zubar da hawaye.

"Yaya Sadik ɗina" rumaisa ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana kuka"

Bashir ya kalli Usman ya ce "Abokina, wai har ku nawa ne yayyen nata ne?"

Usman ya yi murmushi ya ce "Mu bakwai ne, ita ce autar mu"

"Masha Allah, ba wanda zai ce mamanku ce ta haifeku, sam ba ta tsufa ba" yayi maganar yana murmushi.

Abubakar ya kalli Usman ya ce "Meyasa ba a gaya mini tun a jiya ba, sai yau da asuba Aliyu ya gaya mini".

"Mama ce ta ce kar a gaya maka, kar ka ce zaka taho a jiya, ga wanda ya tsinto ta a katsina nan" yayi maganar yana nuna masa bashir.

Abubakar ya nufe shi ya miƙa masa hannu yana faɗin "Ɗan uwa, mu gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi, tun da aka ɗauki rumaisa muka rasa nutsuwa mun gode sosai Allah ya biya" ya sake komawa wurin ruma yana dubata ya ce "Allah sarki autarmu, haka ki ka koma duk kin rame ruma, kullum tunaninki muke yi"

"Nima kullum sai na yi tunaninku, sai na ganku a mafarkina" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Bashir ya dubi Adam ya ce "Akwai buƙatar mu tafi, na san masu zuwa dubiya zasu yi ta zarya, mu ƙyaleta ta keɓe da 'yan uwanta" takawa bai iya cewa komai ba, Bashir ya ja hannunsa suka fita.

Suna tafe a hanya Adam ya ce "Ka wuce da ni gidana, bana son komawa gida yanzu".

Bashir ya ce "Shikenan, amma dan Allah kar ka je ka damu kanka, ko ka yi ta tunani, hakan ba wani amfani da zai yi maka" still dai Adam bai ce masa komai ba.

Can bashir ya kuma cewa "Amma it seems you know each other before kai da yarinyar nan, a ina ka santa?"

"Bashir, dan Allah ka ƙyaleni, ina cikin tsaka mai wuya, dole yarinyar nan ta yi magana, kan al'aamrin nan ya ƙara kwaɓewa" yayi ya a hasale.

Bashir ya ɗan gyaɗa kai ya ce "Haka ne, amma dole ka rage zafin zuciyar nan mu bi a hankali, dan yarinyar nan da alama gardamammiya ce ta fika taurin kai" ya cigaba da tuƙi, ba wanda ya kuma cewa komai.

Can gidansu Adam kuwa, su Iman suka ƙara shiga damuwa, ganin ammi ba ta fito karyawa ba, kuma sun je wurinta hadimarta ta tabattar musu da cewa ta ce kar wanda ya je wurinta, tana buƙatar kaɗaici.

Cikin damuwa Nusaiba ta ce "Iman, ko ke kin san wani abu ne da yake faruwa, why are they behaving like this? They all look strange today"

Cikin damuwa iman ta ce "Tare fa muka kwana muka tashi da ke, ban san komai ba, nima dai na shiga damuwa da mamaki, wani abu yana faruwa amma maybe ba sa son mu sani ne".

"Amma ko menene wannan, abu ne mai girman gaske, tun da har ta kai ga ammi ta ce kar wanda ya je wurinta, ga takawa tunda suka fita da abokinsa bai dawo ba" suka koma suka zauna suna tattaunawa a falo.

Baba uwani ce ta same su ta ce "Yaran nan meya samu giwar Galadima ne yau, daga ita har É—an gidana na kasa gane kansu yau, ko abinci ba ta bari an shigar mata da shi ba, shi kuma ina magana bai ko kalleni ba, duk da miskili ne amma ba ya shareni idan na gaishe shi"
Iman ta ce "Zancen da muke yi kenan, bamu san meyake faruwa ba"

"To Allah ya sa dai lafiya" tayi maganar ba tare da ta ji daÉ—in rashin samun wani bayani ba.

Ƙamsshin turarensa da ya daki hancinta ne ya sanya ta san shine, a take ta ƙara tsuke fuska.

"'yan matan ammi, ya na ganku kun yi tsilli-tsilli da ido kamar marasa gaskiya ne?"

Nusaiba ce ta fara cewa "Uncle J ina wuni?"

"Lafiya lau" ya amsa yana ƙarewa iman kallo. Banza ta yi masa taƙi kulashi.

"Iman ba zaki kulani ba?" Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya ja wata irin ajiyar zuciya ya ce "Ina ammi ne?"

Nusaiba ta ce "Tana hutawa ne, ta ce kar a dameta yau"

"Takawa fa, tun jiya rabona da shi, ga wayoyinsa ba sa shiga gaba É—aya, a gidan nan ya kwana ne ko gidansa?"

"Eh a nan ya kwana, amma yanzu baya nan"

Ya É—an yi shiru sannan ya kuma cewa "Ba ku san in da ya tafi ba?"

Nusaiba ta waro ido ta ce "Uncle J, takawa ne zai gaya mana wani wuri da za shi? Bamu sani ba".

"Wai ya nake ganinku duk wani iri ne, ko akwai abun da ku ke ɓoye mini?".

Nusaiba ta ce "A'a Bakomai".

Miƙewa iman ta yi zata bar falon "Iman" ya kira sunanta.

Ta tsaya cak ta waiwayo tana jiran abun da zai ce.

"Zo ki zauna ina da magana da ke"

Ji ta yi tamakar ta ce ba zata dawo ba, amma ta nemi wuri ta zauna.

Yayi wa Nusaiba alama da ido, a kan ta basu wuri. Ba musu Nusaiba ta tashi ta bar falon.

Kujerar two seater da iman ke kai, ya zo ya zauna, ya É—an tsura mata ido, amma ta takure jikinta, kamar yana motsawa zata zura da gudu.

"Iman" ya kira sunanta, ta É—an É—ago amma ba ta kalleshi ba.

"Meyasa ki ka yi blocking É—ina a what's app, da phone É—inki gaba É—aya?" Tayi shiru tana sauke numfashi.

"Am talking to you, or just because i ask for your pictures, you can deny it if you don't want, meyasa zaki yi blocking ɗina, bari abun da ki ke ta gudun kar in faɗa, i love you, ina son ki iman, kuma zan bi ta in da na san zan samu abun da nake so kai tsaye, kin san tsarin gidan sarauta ai, so gara ki kwantar da hankalinki ki daina kaucewa" hawaye ne ya cika mata ido, amma ta yi ta ƙoƙarin kar su zubo. Ya gama surutansa ya tashi ya tafi.

Kamar zata kifa haka take sauri, yau ko bari ba ta yi daren yayi ba, saboda yadda maganar ke mimtsininta ji take idan ba ta je ta kai rahoton ba, wani zai rigata.
Sashin Mummy ta isa, ta nemi iso aka yi mata, mummy na ganin yadda baba uwani ta shigo jiki na rawa ta san akwai magana, dan haka ta sallami barorinta, ya rage daga ita sai baba uwani. Ta dubeta ta ce  "Meyasa ki ka shigo mini a yanzu? Sai kin saka an fara zargin mu, ina fatan dai abun da ki ka zo mini da shi, mai muhimmanci ne ba shirme ba?"

"Allah ya baki yawan rai, wani ƙwai ne yake gangarowa daga kan dutse, kuma da alama idan ya fashe zai yi warin da zai addabi kowa".

Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Bani labari".

"Alamu sun nuna akwai wani abu da giwa take ɓoyewa ita da ɗan ta, dan tun jiya sun kasa sukuni, sun gaza zaune sun gaza tsaye, dan ita yau ta hana kowa ya je in da take har 'ya'yanta, shi ma kuma tun da ya fita shi da wani abokinsa bai kuma dawo ba, suna ta ƙumbiya-ƙumbiya, amma ina nan zan sanya ido, da na ji ƙyas zan kawo miki rahoto"

Mummy ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ta kaɗaice ta hana kowa zuwa in da take, ciki har da 'ya'yanta, lallai abun da yake cikin ƙwan nan, ba ƙarami bane ba, ki cigaba da sanya ido, ƙwan ya fashe a kan idonki, kuma da zarar ya fashe ina son ki riga kowa sani, ya kuma nice wadda za ta fara jin ko menene, ina nan ina jiranki, haka zalika nima zan sanya ido a nawa ɓangaren"

"Allah ya baki masara, in Allah ya yarda za ayi duk abun da ki ka ce, na barki lafiya" Mummy ta É—aga mata hannu alamar zata iya tafiya.
Chapter 90 · 0% Book details