← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 174

Sashe 161

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da maganganun da take, da toothpaste É—in da take sha, duk yana kallonta, ta ajiye ta nufi bath É—in.
Nan ma wata mitar take yi "Wato ma kawai an kawo masa baiwa, na yi gyaran ɗaki, ya ci abinci na yi wanke-wanke, kuma wai ni zan haɗa masa ruwan wanka, ga shower ya kunna ya yi wankan, amma ba zai iya ba, ko da waye yake haɗa masa ruwan  oho? Zai ga tsiya, wallahi ruwan zafi zan haɗa, idan ya ƙone gobe ba zai kuma sakani ba. Saboda tsabar wulaƙanci, mutumin nan ma bashi da kunya, kuma ammi ba ta san yana yin maganganun batsa ba, a haka kamar na Allah, kuma da alama ba ya yi wa kowa sai ni, to wallahi ni ina da tarbiyya ".

Ta din ga surutu a banÉ—aki, kuma ko da wasa ba ta waiwaya ba, balle ta ganshi, ta kunna ruwan zafi, fiye da rabin bath É—in nan, sannan ta kunna na sanyi, ruwan sai tururi yake yi, ta ce "Allah ya sa yana zuwa kawai ya shiga, gobe ba ya kuma sakani aiki ba, bayan ya gama ci mini mutunci".

Ji ta yi an rufe ƙofar banɗakin, da sauri ta tashi ta waiwaya tana kallonsa.

Ya shigo kamar zai wuce ta, ya shammaceta, ya danƙota, ya shiga cikin bath ɗin da ita.

Ihu ta kurma, jin zafin ruwan, ga kayan jikinta nylon ne, ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhhhh, ai gara mu ƙone tare".

Kiciniyar tashi ta hau yi, amma ya riƙe ta sosai a jikinsa, ya din ga ɗibar ruwan, yana zuba mata a kanta.

Ayshercool.
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

A gigice ya tashi zaune yana tambayar rumaisa ko lafiya.
Idanuwanta duk sun yo waje, sai sauke numfashi take yi, hannunta ɗaya riƙe da cikin ta, tana kuka.

"Ki yi mini bayani, menene meya same ki?".

"Cikina ciwo, zan mutu dan Allah ka taimakeni, wayyo mama" a gigice ya sauka daga kan gadon, ya kunna fitila hakse ya gauraye É—akin.

Tana durƙushe ta riƙe cikinta, hankali tashe ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya saka jallabiya, ya ɗauki mukullin motarsa, ya tafi ɗakinta da sauri, ya ɗauko mata hijjabi, ya saka mata, ya riƙo hannunta.

Da ƙyar take iya takawa, sai yarfe hannu take yi tana kuka, suka saukko ƙasan benen.

Baba uwani na jin motsi but kamar fitar tusa ta fito, "Ranka ya daÉ—e lafiya? Meya samu Æ´ar ta wa?".

"Ba ta jin daÉ—i ne, zamu je asibiti".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya sameki haka?"

Rumaisa ba ta amsa mata ba, ta cigaba da kuka.

"Yallaɓai ko biyoku zan yi, ko za a buƙaci wani abu, ba ka tafi asibiti kai kaɗai ba, daga kai sai ita".

Adam ya ce "A'a baba uwani, ki yi zamanki dan Allah, ba sai mun wahalar da ke ba, zan iya kula da ita".

Ya saka rumaisa a mota, ya kunna ya fita.

A cikin motar ma, she was very restless, ta rasa in da za ta sanya kanta, ta juya nan ta juya can, sai kuka take yi.

"Ko dai wani abun ki ka ci ya ɓata miki ciki? Ko kuma abincin da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin".

"Nima ban sani ba, cikina zai haɗe da ƙafata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku".

"Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu".

Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka buÉ—ewa rumaisa file ya shiga da ita.

Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa.

Ta ce masa "Cikina ne da ƙafafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai".

Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?"

Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?".

Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?".

"Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa.

"Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne".

Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?"

Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban taɓa yi ba"

Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar? Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?".

"Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta.

Adam ya ce "Za ayi watanni takwas".

Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a.

Yayi counseling É—in ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba.

Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya karɓa ya ja hannunta suka fita.

Ta bashi tausayi ba kaÉ—an ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba.

A durƙushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata.

Sai dai ta ce Allah karta ba za a buÉ—e mata jiki a ganta a gaban Adam ba.

Ga ciwo na cinta, ga zunzurutun wauta, in da Allah ya taimaka, nurse É—in da take on duty mace ce.

Ƙarshe ta tsaya ayi allurar nan, ba ta tsaya ba, dai da adam ya fita, daga waje yana jiyo kukanta, sai ka ce ƴar shekara biyar, saboda an yi mata allura.

Sai dai ana gama yi mata allurar ta hau amai, kasancewar tun rana rabonta da abinci.

Aikuwa Adam ya din ga yi mata faɗa, na rashin cin abincin da ba ta yi ba, sai dai gaba ɗaya hankalinta ba ya tare da ita, ƙarshe sai da suka dangana da saka mata ruwa.

Haka Adam ya zauna da ita, har asuba a asibitin, aka gama yi mata abun da za ayi mata, na ƙarin ruwa da allaurai ya ɗauke ta zuwa gida.
Suna tafe a hanya ta samu barci, dama tun suna asibiti yayi sallar asuba.

Da ƙyar ya kaisu gida, saboda barccin da yake ji.

Sai da suka isa gida ya tasheta, ta fita daga motar tana takawa a hankali.

Baba uwani na jin tsayuwar motar, ta fito tana yi musu maraba, tana tambayar jikin rumaisa, Adam ya ce mata da sauƙi.

Suka nufi step É—in bene, baba uwani ta sake cewa "Takawa ko zan zo na taimaka da wani abun ne?"

Ya ce "A'a ta warware, ciwon ciki ne dama, yanzu bacci za ta yi"

Ta ce "To shikenan babu laifi, Allah ya ƙara lafiya".

Ya amsa mata da Amin.

Sai da ya raka rumaisa har É—akinta, sannan ya juya ya fita, sai dai yana fita ya ji kukanta ta na faÉ—in "Na shiga uku, zan mutu".

Da sauri ya koma yana tambayarta menene?.

Ta ɗage doguwar rigar jikinta, Jini na bin ƙafarta.

"Dan Allah ki yi wa mutane shiru da wannan koke-koken, maganin me zai yi miki?"

"Jinina ne zai ƙare, idan ya ƙare mutuwa zan yi".

"Ai gara ki mutun in huta, ki yi mini shiru ni, bari na yi wa baba uwani magana, ta zo ko da abun da zata taimaka miki da shi".

Da sauri ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka kirata, ka kirawo mini su Yaya usman a waya, dan Allah"

Kallonta yake, cike da mamakin wauta da rashin hankalinta.

"Ke wai ya ki ke so na yi ne?, shikenan ba zan huta ba saboda na aureki? Tun da ba za a kirata ba, sai ki wuce toilet ki gyara jikinki".

"Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin".

Guntun tsaki ya ja, ya wuce banÉ—akinta, ruwa ya haÉ—a mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banÉ—akin.

Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banÉ—akin, ya janyo akwatin lefenta, ya É—auko mata pad, kasancewar lokacin da aka haÉ—a lefen har da ita a ciki.
Ya É—auke bedsheet É—in daga kan gadon.

Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banɗakin, tana ta raɓe-raɓe.

Ya kalleta ya ce "ƙazamar ina ce ke? Ba ta ɓaci da jini ba ki ka kuma sakawa?".

"To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.

Ajiye mata pad É—in yayi, ya É—auki bedsheet É—in ya fice.

Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad ɗin na  in da ya ajiyeta.

"Ba zaki saka bane?".

"Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani"

Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba.

Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad É—in ta É—aure a leda, ta canza phant ta canza wata.
Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata É—akin.

Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haÉ—a da kayanta da ta cire suna banÉ—akinta.

Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice.

Ko da baba uwani ta ciro bedsheet É—in, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya.
Chapter 161 · 0% Book details