← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 174

Sashe 173

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye shi da ba zai yi ƙarya ba? Na faɗa na zata ƙarya yake yi, tun da a gabana yake yi wa papa rashin mutunci, wai bai gaya masa anty aisha ta ɓata ba. Sai kuma ya zo ya ce mini papa bashi da lafiya na yarda? Ai ni a ganin farko nake gane mutum".

Ammi ta ce "Ruma ya isa haka, ki yi masa addu'a"

"Ammi ni fa rashin adalci ne da fuska biyu ba na so".

Kallonta duk suke yi, ba tare da gane in da zamcenta ya dosa ba.

"Ammi ki danne ni, ƙasusuwana karyewa suke yi" maganar takawa ta sa suka mayar da hankalinsu kan shi".

Iman ce ta yi sallama a bedroom É—in, jikinta a sanyaye ita ma.

Rumaisa ba tare da jin kunyar wani ba, ta zauna a gefensa, ta riƙo hannunsa da yake cikin na ammi, ta ce "Papa meye yake maka ciwo?"

Ya riƙe hannunta sosai, cikin tsananin ciwo ya ce, "komai ma, Allah idan mutuwa za ta zama hutu a gareni, Allah ka sanya na mutu, da wannan azabar da nake ji" yayi maganar yana sake riƙeta tare da yin ƙara.

Duk ta na jin azabar riƙon da ya yi mata, ta sunkuya dai-dai kunnensa ta ce "Papa ba kyau fatan mutuwa fa, idan ka mutu sabir fa, ammi fa? Dan Allah ka daina, ka bari in cikawa anty aisha alƙawarin da na yi mata, zaka warke gaba ɗaya har abada" ta yi maganar tana zubar da hawaye.

Samha wani uban tsaki ta doka, ta tashi ta fita, abun da babu wani take gaya mata game da zamansu daban, abun da take gani yanzu daban.

Mummy ma tashi ta yi ta ce "Giwa, Allah ya bashi lafiya, amma akawai buƙatar ki din ga kwaɓar sirikar ki, ta iya bakinta".

Ammi ta ce "To na gode".

Baba uwani ta kawo kai, suka haÉ—u da Mummy, Mummy ta yi mata sigina da ido, sannan ta tafi.

"Ki yi mini Addu'a" ya faɗa ya na sassauta riƙon da ya yi mata.

Baba uwani sai jera masa sannu take yi, iman ta kawo maganinsa, a shafa masa, ya ce ba ya so.

Iya abun da Allah ya sa rumaisa ta iya, ta din ga karanta masa, sai dai ta fi nanata la'iila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin. Saboda tana da yaƙinin duk wahalar da ta shiga, idan ta karanta ta na samun mafita.

Lumshe idanunsa ya yi, ya daina hargowar da yake yi, ta kalli ammi ta ce "Wallahi ammi asiri aka yi masa, wai ku ba kwa ganin abun da nake gani?".

Ammi ta ce "A'a rumaisa, Allah ne ya É—ora masa, muna fatan Allah ya yaye masa".

"Ammi, wai baku ga matar da take zaune tare da su Mummy ba, tana kallonsa, wata baƙa, idonta ya na ci da wuta, haka fa wataran idonsa yake yi, idan ransa ya ɓaci, kuma wallahi ni ban yadda da babar mahmud ɗin nan ba...... Kamar daɗi take ji abun da ya samu baban sabir, sai murmushi fa take yi ku.........

Hannun sa ya saka ya toshe mata baki, duk da idonsa ya na rufe.

Rumaisa baba uwani take kallo, idan har abun da Mahmud da kuma Asiya suka gaya mata a kan baba uwani gaske ne, to za ta yi amfani da shawarar yaya usman, dan ranar da suka je gida, ba abun da ba ta gaya masa ba, kuma shi ya bata shawarar ta faÉ—i wata maganar a gaban baba uwani, wadda ta san za ta iya zuwa kunnen Mummy.

A zahiri rumaisa ta ga matar da take faÉ—a, a tare da Mummy, sai dai a wannan karon ma, ta gane ita kaÉ—ai take ganin ta.

Bacci ne ya É—auke Adam, rumaisa ta tashi ta ce za ta yi salla.

Ammi sai sannu take yi mata, saboda ta san idan har ciwon adam ya tashi, duk wanda ya yi wa wannan riƙon sai ya ji jiki, amma ta ga rumaisa ras da ita.

Maimakon ta je ta yi sallar, sai ta fice harabar gidan.
Lelleƙawa take yi, ko za ta gano Mahmud, dan ta na da labarin gaya masa.

Bisa sa'a, ta ga yana tahowa daga waje, da alama masallaci ya je.

"Daddy" ta ƙwala masa kira.

Yana hangota ya yi murmushi, ya ce "Daughter, ina takwarana?".

"Ya na wurin ammi, dama kai nake nema, Allah ya sa na ganka".

"To gani ya aka yi? Amma ba kya tsoron kar mijinki ya ganki, ya kuma hantararki?".

Ruma ta tura baki ta ce "Bashi da lafiya fa, kuma kowa ya zo duba shi, har da mamanka amma kai ba ka zo ba"

"To ai kin san ba shiri muke yi ba"

"Daddy meyasa?".

Mahmud ya numfasa ya ce "Manta kawai, ya aka yi?".

"Ka san maganar da muka yi ai ranar ko?, kuma ka ce zaka taimaka mini".

Mahmud ya ce "Ko zan yi wa kowa ƙarya, ban da ƴa ta".

Rumaisa ta ce "To ni fa na ce mamanka ce ta ke yi wa mijina asiri a gaban baba uwani".

Ya É—an yi shiru ya ce "Ke waye ya gaya miki haka?"

"Haka nake tunani, kuma nake son tabattarwa, amma so nake na kama baba Uwani, yaya usman ne ya bani shawara. Ni fa ban yadda matar nan mamanka ba ce, jiya mafarki na yi tana tura papa rami, yau kuma na ganta da wata mata, ba wanda yake iya ganinta sai ni, baƙa mummuna, idonta sai wuta yake yi, abar tsoro kawai dai ni ba ta tsorata ni ba. Papa sai ihu yake yi, abun tausayi"

Yayi zuru da ido yana kallon rumaisa, sai kuma ya ce "Da gaske ki ke ko da wasa?".

"Ni ba kullum nake yin ƙarya ba" ta bashi amsa.

"So, you want expose my mother daughter?".

Ta yi shiru, tare da zuba masa ido.

Ya ce "Shikenan, ni na yi alƙawari ai kuma zan cika in sha Allah, duk wani support da ki ke nema, i will assist in sha Allah, zan taimaka miki, ki cika alƙawarin da ki ka yi wa fulani, amma yaushe zaki bashi bayani a kan abun da yake nema na binciken? Ya na son aisha sosai, a yanzu ba shi da burin da ya wuce, ya gano wanda suka saceta".

Rumaisa ta ce "Kamar ka na son takawa? Tun da har ka san abubuwa a kan sa, amma meyasa ba kwa shiri?"

Jiki a sanyaye ya ce "Kar ki damu, lambar wayata na nan, na rubuta miki, a bayan sashin su mijinki, duk lokacin da ki ke buƙata ki kirani, idan har ina Nigeria" yana gama faɗa ya juya zai tafi ta ce "Idan kuma na gane ka zaɓi uwar riƙon ka, ka yaudareni, zan yi maka abun da ba ka zata ba, zan iya yin komai a kan uban ɗa na"

Cak ya tsaya, ya waiwaya ya kalleta, kawai ta kwashe da dariya, ta ce "Kamar a film ko? Zan iya acting ashe, ai na san ba zaka yi mini haka ba"

Tun da ya dawo ƙasar nan, suka haɗu da rumaisa, suka yi magana, yake jin kamar wani abu ya sauya a tare da shi, sosai yake jin tausayin Adam, kuma a jikinsa yake jin, lokaci ya yi, da yakamata Mummy ta tuba, shekaru sun fara ja, ko ba komai ta mutu ta samu rahamar Allah, sarautar da take yi masa ƙuzu kuma, shi ba a gabansa take ba ma.

A ɗakin Iman rumaisa ta yi salla, iman ta baya doguwar rigarta ta saka, suka zauna su na ɗan taɓa hira, iman ta ɗan bata labarin, irin wahalar da yake sha, idan yana ciwon nan, da kuma wahalar neman magani da ammi take yi, ba yau ba gobe".

Iman ta ɗora da cewa  "Anty rumaisa, da kin sani ba ki faɗi maganar nan ta ɗazu a gaban mutane ba, ba zan musa miki mummy ba ta asiri ba, amma idan maganar ta koma kunnenta fa? Zai iya haddasa wata rigimar".

"Ai na ga duk wanda yake wurin, amintacce ne. Waye zai je ya faÉ—a? Ammi ce za ta gaya mata, ko kuma ke? Ko kuma baba uwani, da dama dan ita na faÉ—a"

Iman ta kalli rumaisa da mamaki, rumaisa ta yi dariya, ta ce "Iman, ina da wayo fa, kawai dai ba na ji ne, amma dan Allah Meyasa papa suke gaba da daddyna? Ko da ba ammi ce ta haifesu duka ba, amma ai Æ´an uwa ne"

Iman ta ce "Duk Æ´aÆ´an ammi ne"

Rumaisa ta ce "Ai na zata kema zaki raina mini hankali ne, ai na sani, na san duk ammi ce ta haifesu, amma daddy ya dage wai waccan matar ce babarsa, amma dan Allah meyasa gaba É—aya gidan nan naku, a hargitse yake? Kowa ba shi da gaskiya".

Iman ta rausayar da kai ta ce "Ai ba abun da ki ka gani, family ne mai cike da rikici da ƙulla-ƙulla".

"Ai shi ne wannan yayan anty aishan, zai raina mini hankali, ni kuma wallahi yadda mutum ya mu'amalance ni a farko, haka nake tafiya da shi, kin ga rashin mutuncin da suka yi mini ranar da muka je gidan su, da shi, da wannan masifaffiyar mai jan kaya ta É—azu, da wannan jabir É—in, shi ma jabir É—in da babarsa, wadda ta riga Mummy tafiya É—azu.
Wai takawa ya turo shi ya ɗauke ni daga makaranta, na ce ba zan hau motarsa ya kashe ni ba, dan na san haushina yake ji, saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, wai ni zai yi wa dabara, a gabana fa ya yi wa papan wulaƙanci, wai an sace ƙanwarsa bai gaya masa ba, shi a wa? Sai ka ce son anty aishar suke yi".
Chapter 173 · 0% Book details