Sashe 12
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.
Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya É—ago ya kallesu ya ce "Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?"
Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi"Mama tana nan?"
"Eh tana nan" Aliyu ya bashi amsa.
Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba'asi.
"Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?".
Mama ta É—an yi sororo ta ce "Wace irin sikila kuma?"
"To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ƙi sai a bayana na goyota"
Yaya Umar ya kalleta ya ce "Ke meya sameki?"
Cikin in da in da ta ce "Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata 'yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita".
"Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?" Yayi maganar cikin tsare gida.
Cikin kuka ta ɗage ƙafar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce "Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?"
Cikin tsawa Yaya Umar ya ce "Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba"
A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta riƙe hannun Huzaifa, ta ɓuya a bayansa.
"Ni nake miki magana ki ke ɓuya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba"
"Dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi idan suka san ƙarya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan" kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.
Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.
Yaya Sadik ne ya fito daga É—akinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita É—akin su.
Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya ɗan ƙura mata ido sannan ya ce "Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?"
Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji"
"To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?"
"Gani nayi za a kashe ni da duka, ni bana son a dake ni".
"Gaskiya ba ka kyautawa, dan me yarinya za ta yi laifi ka hana a hukunta ta, me kake ƙoƙarin koya mata ne?" Umar yayi maganar a mugun fusace.
Yaya Sadik ya waiwayo ya kalli Hussainin na sa, ya haɗa hannayensa alamar ban haƙuri ya ce "Tuba muke, zan wa tufkar hanci in sha Allah, on behalf of her, ayi haƙuri gobe in Allah ya kaimu da kaina zan mayar da ita makarantar in basu haƙuri" gajeren tsaki Umar yayi yai waje, babu wanda yake masa katsalandan kamar yadda Abubakar yake yi masa, ya fuskanci idan aka biyewa Yayan nasa ruma tsiyarta zata tsula ba tare da an kwaɓeta ba, da tayi laifi sai ya ce ƙuruciya ce.
Wunin ranar kowa share ruma yayi, yaya Sadik ne kawai yake kulata, Huzaifa da yasir suka ƙare mata zagi tsaf suka tsangwameta.
Ko a jikinta, tun da Allah ya sa ba a mayar da ita makarantar an ce ƙarya take ba, hankalinta ya kwanta.
Washegari Yaya Abubakar da kansa ya rakata makarantar, aka dinga yi mata sannu ana mata ya jiki, ta basar ta dinga amsawa.
************
Sanye yake da fararen kaya ƙal, fuskarsa sanye da fari siririn glashi, taku yake cike da ƙasaita ya biyo wata doguwar baranda.
Sannu a hankali ya ƙarasa gaban wata ƙatuwar ƙofa, ya sa hannu ya murɗata a hankali. A take ta buɗe wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinsa.
Da sallama ya shiga ya mayar da ƙofar ya kulle, babu kowa a falon sai wata matashiyar budurwa tana saka turaren wuta.
Amsa masa tayi tare da faÉ—in "Sannu da zuwa".
"Yauwwa 'yar aikin Ammi, ina ma'aikatan ne ki ke aikin da kan ki?"
Ta É—an kalle shi sannan ta ce "Nima 'yar aikin ce ai" yayi murmushi ya ce "Sorry idan haushi ki ka ji, ina Ammi?".
"Bacci take" ta bashi amsa lokacin da take cigaba da saka turaren wuta.
"Ba kowa kenan?"
Cikin ƙosawa da tambayoyinsa ta ce "Duk sun tafi makaranta".
"Ke me ya hana ki je makarantar?"
"Ohh God, uncle J am sick shi ya sa ban je ba, Ammi idan kana son ganinta ka dawo an jima, ina fatan zan iya tafiya na gama amsa tambayoyin ka?"
Ya girgiza kai ya ce "No, saura É—aya ina yayan ku?"
Tayi murmushi ta ce"Wannan tambayar ai kai yakamata a yiwa, i don't know " daga haka ta bi wata hanya ta bar falon.
Ya girgiza kai a hankali ya ce "Wannan yarinyar ta fi mai kora shafawa, izzarki tayi yawa"
Wayarsa ce ta fara ringing, ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar.
"Ke nifa kin isheni, ni kaina ban san in da yake ba, anjima kuma kilisa zan fita, zan neme ki amma" daga haka ya kashe wayar, ya saka a aljihunsa ya fice.
*********
Ruma ta sha kashedi a wurin su Huzaifa, a kan ta shiga hankalinta a makarantar nan, dan ba ƙaramin girmansu ake gani ba, halinta ba zai sa mutuncinsu ya zube ba.
Ta cigaba da zuwa makaranta, amma ba ta gane komai, idan Yasir ya zaunar da ita zai koya mata kuma, sai ta ce ita ta gaji ba ta so.
Ranar wata juma'a da yamma, Abdallah yana ta haÉ—a kayan miya, za a kai markaÉ—e, Yasir ya kalleshi ya ce "Abdallah kyanta na É—au hotonka kana haÉ—a kayan miyar nan, na je na nunawa yarinyar nan mai awara".
HaÉ—e rai Abdallah ya yi ya ce "A'a mai wake zaka nunawa ba mai awara ba"
Yasir ya yi dariya ya ce "Zaka ga mai wake, wallahi yarinyar nan ta mato a kan ka, kawai ka nutsu ku daidaita, wallahi shar da kai awararka zaka yi ta ci"
"Na rantse idan ba ka yi mini shiru ba sai na ɓarar da kai"
Yasir ya ce "Yaya ba zan ƙoƙari na tayata kafa gwamnatin ta ba, kullum sai ta kyauta mini".
Buut Ruma ta fito daga É—aki ta ce "Yasir yakamata muje ka gabatar mata da ni, na dinga biyawa idan zan je makaranta".
Tsaki Yasir ya yi "To munafuka waye ya sako dake, na zaci ma bacci take wallahi "
Abdallah ya ce "Wallahi ko da wasa ki ka je, sai na kakkarya ki".
"To ni ce maka ma nayi zan je?"
"Ke dai ki ka sani gulayya" Yasir yayi maganar yana hararta.
"Wallahi ni ba gulayya ba ce" shareta suka yi suka cigaba da hirarsu, yayin da Ruma ta koma gefe tana naÉ—ar abin da suke faÉ—a.
Kamar yadda a islamiyya ruma ba wani ja take ba, haka ma makarantar boko ba uwar da take ganewa sai wasa.
Ta na cikin top 10 na marasa ganewa a aji, sannan ta farko a sahun marasa ji.
Yau bayan an taso daga makarantar boko, ta biyo ta hanyar da lambun mai unguwa yake. Ƙaton lambu ne da ya kasance mallakin wani a babba masarautar Kano, wanda yake ƙarƙashin kulawar mai unguwa, ba kowa ya san da hakan ba sai ɗaiɗaikun mutane.
Gaba É—aya hanyar ba ta cikin jerin hanyoyin da zata bi su sada ta da gida, amma tun da ta ji 'yan ajinsu suna labarin mangwaron lambun ya fito yayi kyau, tayi alwashin bi ta hanyar dan ganewa idonta abin da suka gaya mata.
Aikuwa babu ƙarya, lambun ƙato ne na gaske, wani wurin an kewaye shi da katangar bulo, wanu wurin kuma aka ƙarasa kewaye shi da waya.
Akwai bishiyoyi kala-kala a ciki, wasu duk sun yi 'ya'ya kasancewar lokaci ne na damuna.
Mangwaron nan yayi 'ya'ya sosai gwanin ban sha'awa.
Ƙatuwar ƙofar shiga wurin ta gani, babu kowa a wurin, dan haka kai tsaye ta kutsa a gaban wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ta tsaya, yanayin wurin yayi mata kyau sosai da sosai.
Ta samu dutse, ta dinga jifan bishiyar, suna faÉ—owa tana É—iba, ta tara ta cika jakarta, sannan ta nufo hanyar fitowa.
Tana fitowa wani matashi yayi caraf ya danƙeta yana faɗin "Alhamdilillah, shegiya ɓarauniya ashe ku ne masu shiga lambun nan suna ƙurguma mana sata".
"Ban gane ba wace iri ɓarauniya me nayi maka?"
"Zaki ga me ki ka yi mini, gidan mai unguwa zan kai ki, ke saboda ƙwarewa ma, da ki ka sata sai ki ka biyo ta ƙofa zaki fita, kina 'ya mace kina sata"
Cikin rashin kunya Ruma ta ce "Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, ta ƙofar nan fa na shiga, ba wanda ya haura gida ne ɓarawo ba?"
"To da ki ka bi ta ƙofar, wa ki ka tambaya ki ka shiga ki ka ɗebo abibda ba naki ba?"