Sashe 172
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi a zahiri ma ba film É—in yake kallo ba, yanzun ma fitowa ya yi, domin ragewa kansa damuwa, da kaÉ—aici, atleast ya É—an ji releif kaÉ—an, ya saka a ransa zai yi mai yiwu wa, wurin bin shawarar Bashir, ya saki jiki da rumaisa su samu kusanci sosai da sosai.
Har dare, ba ta sake yadda sun haÉ—u ba, dan ya gama ba ta kunya gaba É—aya.
Har É—aki Asiya, ta kawo mata uniform É—in ta, an wanke wanda ta cire an goge mata su.
Ta karɓa ta yi wa Asiya godiya, ta cewa Asiya dan Allah ta dafa mata indomie, dan ba za ta fita ta haɗu da adam ba.
A É—akin ta bar kwanun, ta yi sallar isha'i, ta hau aikin nata na bacci.
A cikin mafarke-mafarkenta, da ta saba yi, yau ta ga Mummy riƙe da sarƙar da take yawan ganin an ɗaɗɗaure adam da ita, yau ta ga mummy riƙe da sarƙar, ta hankaɗa adam cikin wani rami.
Ba ta san ya aka ƙare ba a mafarkin, ta tsinci kanta a tsaye, tana ta haki zuciyarta na bugawa da sauri.
Da sauri ta fita daga É—akin, ta tafi na takawa, ta tarar da shi ya na bacci.
Kuka take yi sosai, tana dukan pillown sa, "Ka tashi"
Kasancewar baccin na sa ba nisa ya yi ba, ya farka, dan bai daÉ—e da yin baccin ba.
Da fari ya zata ko ciwon marar ne, ya tamabaye ta lafiya?.
"Ni tsoro nake ji".
"Tsoron me kuma?"
"Ni dai tsoro nake ji" ta yi maganar tana kuka.
Ya tashi zaune ya ce "To zo ki kwanta a nan" ba musu ta haye gadon nasa, ta kwanta, ƙarshe dai har asuba bai samu ya yi bacci ba, ita ma kawai bakan ta yi, amma idonta biyu..
Sai dai tun lokacin da ya tashin, yake jin kamar an zare masa lakar jikinsa, ya fita masallaci, ta sauka daga kan gadon ta koma É—akinta, tana ta addu'a a zuciyarta.
Sai dai kamar jiya da safe, walwalarsa ta sake ɗaukewa, bai ko karya ba, ya tafi kaita makaranta, sai dai a tuƙinsa kawai, ya isa ka fuskanci lallai akwai matsala. Ta yi masa a dawo lafiya ya jinjina mata kai ya tafi.
Sai dai ita ma ta shiga cikin tunani, tun da Allah ya sa ta ga Mummy, take yawan mafarkinsu tare da takawa.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi wurin aiki, dan ko gani ba ya yi sosai.
Tun da ya shiga office, jiki yake nema ya rikice, ya rufe kansa a ciki, yake ta fama da matsanancin ciwon kai.
Bai iya aikata komai ba, ya kunna karatun Alkur'ani a wayarsa, ya ajiye dan idan ya shiga wannan yanayin ba ya iya karanta komai.
Ya daÉ—e a haka, kan a hankali ya fara samun nutsuwa, ya É—au wayar, ya kira Jamil a waya, ya ce dan Allah ya zo office É—in sa.
Ko mintuna biyar ba ayu ba sai ga Jamil, ya na ganin adam ya ruÉ—e ya ce "Lafiya kuwa? Ba ka da lafiya ne?".
"Bana jin daÉ—i ne, dan Allah so nake ka kaini gida wurin ammi, ba na son kowa ya san halin da nake ciki, bana son ayi ta mun sannu, ko azo a zagayeni ban san me zai iya faruwa ba".
Jamil ya jinjina kai, ya É—aukar masa wayoyinsa, ya rungume shi suka fita.
Ko da suka je can gida, adam ya yi garajen buɗe ƙofa ya fita, ya faɗi a wurin. Dai-dai da shigowar motar hajiya jamila da Hajiya Lubabatu.
Saukkowa suka yi, suka nufi adam tare da ma'aikatan, suna tambayar ko lafiya.
Jamil ya ce "Bashi da lafiya, ya ce na dawo da shi gida, kuma ya faÉ—i".
Haka aka kama adam, zuwa cikin gida sashin Ammi.
Ammi ba ƙaramin tsorata ta yi ba, rabon da haka ta faru an kwana biyu, dan an samu kyakkyawan cigaba a lamarin lafiyar Adam.
Kamar gawa haka aka kwantar da shi, a bedroom É—in ammi, su Mummy suka je suka tsaya a kan sa suna yi masa sannu.
Tamkar wanda aka mintsuna, ya fara daddagewa jikinsa ya na rawa, yana danƙar bedsheet ɗin kan gadon, yana girgiza kai.
"Ammi, Ammi! Jikina ki danne ni" ya din ga maganar cikin É—aga murya.
Tuni hawaye ya cika idon ammi, ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya".
Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai wannnan lamari, ni abun nan na rasa gane kansa, Wannan wace irin larura ce?".
"Ammi! Ana kakkarya ni fa, Ki zuba mini ruwan sanyi a jikina" yayi maganar yana neman abun da zai riƙe.
Jamil ya ce "Takawa, ka yi addu'a Allah ya baka lafiya".
Hajiya Lubabatu ta ce "Jamil yo baya fa, kar ya yi maka illa, ko ka manta abun da yake yi, idan ciwon ya tashi haka?"
Gaba É—aya suka tsaya daga baya, sai ammi ce ta zauna a kusa da shi, tana cigaba da yi masa sannu, su iman duk suna makaranta, da ma daga ita sai sabir.
Kan ka ce kwabo, sai ga samha ta shigo tare da Fauziyya, suna sashin Mummy, Mahmud ya gaya musu.
Samha na zuwa ta ganshi jikinta ya yi sanyi, ta na jin labarin rashin lafiyar sa, tun suna yara, wasu lokutan abun ya kan tayar masa, amma ba ta taɓa tunanin abun ya kai haka ba.
Ya na cikin wannan halin, ya koma cewa "Rumaisa! Ammi a É—aukkota daga makaranta, kar wani abu ya sameta. Rumaisa! Ammi Rumaisa".
Jamil ya ce "Ka kwnatar da hankalinka, wace makarantar ce, in je in É—aukkota".
Mummy ta ce "Takawa ka na ta kanka, kana ta wata daban, ka yi addu'a, fatanmu ka samu lafiya"
"Ammi rumaisa" ya sake nanatawa.
Haushi ne ya ƙule Samha, kamar ta buɗi baki, ta ce Allah ya tsinewa rumaisan.
Ammi ta gaya wa Jamil makarantar, ya fita da sauri ya É—au mota.
Mahmud kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, atleast ya na son jin ya jikin Adam, a wani situation yake, abun da bai taɓa ji ba sai yau.
Rumaisa kuwa tuni aka tashi, har ta fara ƙuluwa, ta ce "Lallai papa, zaton sa ba zan iya tafiya ba kamar yadda na ce masa ko? To wallahi tafiyata zan yi, in bi hanyar da ba ta gida ba, in ɓata sai ya nemo ni". Ta na cikin mitar, ta ga motar adam, sai dai ta ga jamil a ciki, dan haka ta tsaya ta na kallonsa.
Ya sauke glashin ya ce "Zo mu tafi"
"Mu je ina?".
"Can gida, takawa ba lafiya, ya ce na É—aukkoki, ya na cikin gari wurin ammi".
"Sai ka ce ba ni da hankali zan hau motar da ka ke tuƙawa, in je ka kasheni a banza, tun da na san ka tsaneni, saboda papa bai auri ƙanwarka ba, to ba zan hau ba".
Ya kwantar da muryarsa ya ce "Da gaske nake yi miki, ni ba kasheki zan yi ba, ba dan shi ya ce na É—aukko ki ba, ba abun da zai kawo ni".
"Taɓ, ka isa ka gaya mini magana in yadda, ai ni yadda mutum yayi mini a haɗuwarmu ta farko da shi nake amfani. Ba ɗazu papan ya kawoni ba ka ce shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, bayan a gabana ranar ka ke yi masa rashin mutunci, ka ce wai bai gaya maka anty aisha an sace ta ba, to ba zan hau ka kasheni ba, ba kai ne yayan anty aisha ba, duk na san komai, da ku ka din ga cin zalinta, tun tana ƙarama, sai da ta mutu za ku nuna kuna son ta. To wallahi ba zan hau ba, gara na tafi da ƙafata".
Baki buɗe yake kallon rumaisa, ita ba ta manta abu, waye ma ya gaya mata wannan zancen, ita aishan ce ko adam ɗin ne ya gaya mata? Kuma ai ba shi ne ya nuna wa aisha ƙiyayya ba.
Ya dai-daita nutsuwarsa ya ce "ƙanwata ki na ji, shigo mota mu tafi, sai mu yi magana, duk wanda ya gaya miki zantukan nan ƙarya yake yi, na san dai aisha ba zata gaya miki ba".
"Kai ni fa ba a lallaɓani, kuma ba a hantarata ko ayi mini dole, ka tambayi mijina ka ji" ta juya tayi tafiyarta, kan ya kunna motar, ya bita, ta haye a dai-daita sahu, ta ce a kaita gidan tsohon galadima.
Ana zuwa ta sauka abun ta, sai masu gadi ne suka biya kuɗin napep ɗin, ta nufi sashin Ammi, a ranta ta na raya idan ƙarya Jamil yake, sai ya gane ba shi da wayo.
Sai dai ga mamakinta ta ga baba uwani a falon ammi, bayan a gida suka bar ta.
Ta na ganin rumaisa ta hau kuka, ta ce "Tun É—azu aka ce a zo a É—aukko ki daga makaranta, yanzu aka kirani a waya, takawa babu lafiya".
Ruma ba ta amsa mata ba, ta fara laluben a ina adam ya ke.
Ta na kaiwa bedroom É—in ammi, ta ji tsigar jikin ta ta tashi, kanta ya wani sara.
Kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, ta shiga ɗakin.
Duk ga su Mummy a gefe, har da Samha da su Fauziyya su na kuka.
Rumaisa ta ƙarasa kansa ta tsaya, sai fizge-fizge yake yi, kamar zai fita hayyacin sa.
Rumaisa ta waiwaya, ta ƙurawa mummy ido, a take jikin Mummy ya hau rawa, ta fara kame-kame "Rumaisa ko?, kin ga takawa ba lafiya ko? Dama yanzu yake ta kiran sunanki ya ce a ɗaukko ki".
Ammi ta ce "Rumaisa, ashe jamil É—in ya É—aukko ki?".
Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ni ba shi na biyo ba, saboda ya tsaneni, haka kawai in je ya kashe ni, ai haushina yake ji saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, na zata ma ƙarya yake yi, lafiyar papan ƙalau, yaudarata zai yi na hau adaidaita sahu na taho".
"Yaya jamil ɗin ne yake yi miki ƙarya?" Samha ta yi maganar a ƙufule.