Sashe 55
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyu ya galla mata harara, ta basar kamar ba ya ganshi ba.
Haka kuwa aka yi, sai da aka samo shayi sannan ruma ta karya.
Gwaggo ta ce lawisa ta zagaya da ruma sashen matan yayyenta su gaisa, su ga ruma.
Jiki na rawa lawisa ta amsa, ta jagoranci ruma zuwa ɓangarorin gidan.
Ruma ta sha mamakin waÉ—anda ta din ga gani a matsayin ma'aurata, duk yara da su.
Sai dai Mutanen gidan akwai su da kirki, hannu bibbiyu suka din ga karɓar ruma, suna yi mata barka da zuwa.
A hanyar komawarsu sashen gwaggo ruma ta ce wa lawisa "Wai duk wannan sirikan gwaggo ne?"
Cikin jin daÉ—in ruma ta kulata lawisa ta ce "Eh" ruma ta jinjina kai.
Bayan sun koma sashin gwaggo, lawisa ta ɗau niƙa za ta kai, ruma ta ce za ta bita. Suna tafe a hankali ruma ta fara sakin jiki da lawisa, ta din ga kallon garin, yayi kyau sosai, 'yan garin ma'abota noma ne.
Duk wanda ya ga Lawisa da ruma sai ya tambaye ta wacece ruma, ta ce musu 'yar uwatta ce. Abin yayi ta bawa ruma mamaki, ita a gida unguwarsu wa ma ya damu da wani, da za a din ga tambayarka waye wannan.
Ko da suka dawo gida ma, ruma a hankali take sakin jiki da lawisa, suka fara aiki tare suna ɗan taɓa hira.
Wajen sha ɗaya na safe, lawalli ya ɗauki Aliyu a babur ɗin sa suka tafi can wani ƙauye, in da a nan wasu daga cikin gonakin nasu suke, wurin gidan wani kawunsu da suke kira da baba Habu.
Ruma ta zazzage kayan da ta zo da su tana sake ninkewa, bayan ta gama ta É—auko wayar nan ta ta, ta fara kallon hotunan ta.
Lawisa ta zauna a kusa da ita tana leƙawa. Gwaggo ce ta kira lawisa, ta tashi ita kuma ruma ta cigaba da kallon wayar.
Hotuna ne da videos da ta din ga yi ciki har da wani sashe na wannan jakar ta bullet da É—aya daga cikin mutanen nan ya rataya, sannan a hotunan akwai in da gefen fuskar É—aya daga cikinsu ta fito.
Ruma ya ajiye wayar tana tunin wasu abubuwa da suka dabai baye mata kai ta kasa gane kansu.
Bindiga dai jami'an tsaro ne suke ta'amalli da ita, amma ta yaya za ayi ace da saninsu ana shiga da fita da su ba tare da sun tsawatar ba?' ajiye wayar ta yi, tana son ƙara nutsawa cikin tunani, amma kwanyarta ta gaza bata komai.
"Ruma zaki je rafi, muje ki ga ruwa da duwatsu".
Gwaggo ta ce "Ke kar ki kaita ki wahalar da ita mana"
Ruma ta ce "A'a gwaggo zan je" tayi maganar tana miƙewa tsaye, ta saka hijjabi suka sake fita.
Wani É—an madaidaicin rafi suka je, 'yan mata wasu na wanki a gefe, wasu kuma suna É—iban ruwa. Ruma ta samu na yi, ta din ga É—aukar hoto, ta din ga tsalle-tsalle a wurin, yanayin ya burgeta.
Kan wani ɗan dutse ta hau, can nesa ta hango wani wuri baƙiƙirin kamar an yi gobara. Ta kalli lawisa ta ce "Lawisa, can gobara suka yi ne?"
Lawisa ta ce "Wallahi wasu fulani ne suka kafa sansani a wurin, cikin dare aka kawo hari, aka ƙona musu shanunsu, suka ce manoma ne suka yi musu ake ta rigima, da ƙyar abin ya lafa"
"Kaii aka ƙona musu shanunsu, kuma da gaske manoman ne suka yi musu?"
Lawisa ta kai bakinta kunnen Ruma ta ce "Ke 'yan ta'adda ne fa suka yi musu, amma aka ce faÉ—an fulani da manoma ne, amma kar ki É—aga hankalinki fa, mu nan haka lafiya lau muke zaune, an fi tashin hankalin a wuraren su Baba habu".
Ruma ta yi ajiyar zuciya ta ce "To kuma ba a gayawa 'yan sanda ba?"
Lawisa ta ƙwalo ido ta ce "'yan sanda, a ina zamu ga 'yan sandan ko sun zo me zasu yi, wataran dai sojoji na zuwa ayi ta harbe-harbe abin tsoro"
"Zo mu je wurin, in ga wurin sosai da sosai "
"Ke, Aikuwa tsaf fulanin nan zasu illata mu, yadda suke a ƙule zo mu tafi gida, na cewa Gwaggo ba zamu daɗe ba"
"Ke ki tafi, ni ba yanzu zan taho ba".
"To ai baki san hanya ba"
Ruma ta ce "Idan na ɓata na tambayi hanyar, ni wurin can nake son zuwa " tsoro ne ya kuma kama Lawisa ta cewa ruma "Ki zo yanzu mu koma gida, akwai hanya mai sauƙi da zan bi da ke muje wurin ".
Ruma ta ɗan rausayar da kai ta ce "Ina fatan ba ƙarya ki ke yi mini ba, ina son in ɗauki hotunan wurin in ɗau komai, yadda zan ji daɗin bayar da labari, kuma idan na bayar a yadda tunda ina da hoto".
Lawisa ta yi murmushi ta ce"Haka ne, karki damu" ta lallaɓa ruma suka koma gida.
Sai dai a washegari ruma ta faki idon mutanen gidan ta fice, kai tsaye wurin da aka yi wa fulanin nan ƙone-ƙone ta je. Sai dai tafiyar da nisa sosai, wurin shiru ba kowa sai ragowar abubuwan da aka ƙona, da tsirarun bukkoki a can gaba kaɗan, wurin kamar an yi wata annoba.
"Ke wace wannan me ki ke yi a wurin nan?" A hankali ta waiwaya taga wani dattijo a tsaye s bayanta, hannunsa riƙe jallon ruwa.
"Sannu baba" ya amsa da yauwwa.
Yana cigaba da ƙarewa ruma kallo.
"Baba gidan 'yan uwanmu mu ka zo, na hau wani dutse na hango nan shine na ce bari na zo na gani, Allah ya mayar da alkhairi amma kun gayawa 'yan sanda abin da ya faru?"
Kallon ruma yake, yadda take magana fiye da shekarunta.
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Gidan wa ki ka zo a garin nan?"
"Gidan dagaci ne, É—an uwan babanmu ne" ya jinjina mata kai ya ce "To mun gode da jajen da ki ka yi mana, amma maza ki tafi kar sauran mutanen rigar nan su ganki".
"To in sun ganni mai zai faru me na yi musu?"
"Kasheki za su yi, dan haka muje na raka ki hanya" babu musu ya saka ruma a gaba har zuwa cikin gari, suna tafe suna hira ruma tana addaba masa da tambayoyinta da ba sa ƙarewa"
A hanya suka yi sallama, ya koma ita kuma ta ƙarasa gida.
Gwaggo duk ta tashi hankalinta rashin ganin ruma, ita kuwa ko a jikinta ta ce kallon gari ta fita yi.
Sai dai a tattaunawar ta da dattijon nan ya gaya mata wasu abubuwa da suka sake É—aure tunaninta.
****
Hajiya Lubabatu ce ta tsaya a tsakiyar ɗakinta, tana kallon hoton Galadima mai ci a yanzu, wands ya kasance mijinta da yake can ƙasar Germany yana jinya, ta ɗan lanƙwasa yatsan hannunta ɗaya sannan ta furta "Ka yi haƙuri ranka ya daɗe, bani da isasshen lokacin da zan cigaba da ɓatawa a kan ka, goben ɗana ita ce a gabana yanzu " ta yi maganar tamkar na cikin hoton yana jinta.
Khalifa ne zaune a kan kujerar da take kallon wadda mahaifinsa yake, mahaifinsa sai murmushi yake sannan ya nisa ya ce "Ina jinka Khalifa".
"Yauwwa daddy, kamar yadda nayi maka bayani, na tsara komai kuma ina da yaƙinin komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".
"Haka ne, banƙi ta taka ba, na kuma yabawa ƙoƙarin da kake yi, amma gani nake komai zamu yi wa yaron nan ba zamu huce ba, yanzu haka bayanai sun zo mini yana garin Abuja, sai dai ban san wurin wa yaje ba, idan har ya cigaba da abin nan EFCC zata bincike ni, kuma daga haka ya ɓata siyasata, ya ci mutuncina kuma ya ɓata gobenka".
Khalifa ya gyara zama ya ce "Daddy, ai shiyasa nake ta ƙoƙarin aikin nan ya tabatta, ta yadda zan kau da hankalinsa a kan komai, ya tattarashi a wuri ɗaya, ka harda dani, abin nan zai yiwu daddy, kuma akwai nasara a ciki".
Senator wakili ya yi murmushi ya ce "To shikenan, ina saurarenka, sannan duk abin da kake buƙata, i will make sure that I provide it".
"To Shikenan Daddy, godiya nake "
Yayi murmushi tare da jinjina masa.
***
Kwanakin su ruma uku, ta saki jikinta, duk da kullum sai sun yi waya da mama, yawo kuwa kamar ta ci ƙafar kare, har gona suke zuwa ita da Lawisa, har ta saba da sirikan gwaggo da yaran maƙwabta.
Sai dai gona É—aya aka samu aka sayar, a gonakin baban nasu, kuma shima dubu É—ari bakwai kawai aka samu, saboda yanayin in da gonar take babu tsaro sosai.
Ana i gobe zasu dawo kano, Gwaggo ta shirya ruma, ta haɗata da lawisa lawalli ya kai su can wani ƙauye, gidan wani ƙanin mahaifinsu, wai su gaishe su.
Aliyu sai mita yake yana tambarat gwaggo yaushe su ruma za su dawo, saboda da sassafe yake son su kama hanya, gwaggo ta ce kar ya damu, gobe da safe zasu dawo.
Har washegari da safe su ruma ba su dawo ba, Aliyu ya ce "Gwaggo, wai haryanzu su ruma ba zasu dawo ba, tafiya fa zamu yi, bana son rana tayi mana".
Gwaggo ta ce "Gadanga, sai dai kayi tafiyarka kai kaɗai, ina sane na tura ruma can, sai za a koma makaranta zan dawo da ita da kaina, yanayi ya nuna mini babu isasshen tsari a jikinta, kuma akwai buƙatar ta zaga ta san dangin mahaifinta suma su santa"
Aliyu ya ce "Amma gwaggo ba mu yi haka da mama ba, dan Allah kar ki yi mini haka".
Gwaggo ta ce "Mhmm, sai kuma ka yi, na gama magana"
Saroro Aliyu ya yi ya ma rasa mai zaice, ya ciro wayarsa ya kira mama a waya.
Yana kira mama ta É—aga ta yi sallama.
"Mama, gwaggo fa ta tura ruma wani ƙauye, wai ba zamu taho tare ba sai an koma makaranta zata da wo da ita".
Gwaggo ta É—an É—aga murya ta ce"Eh, ni na ce ba zata dawo yanzu ba, sai na gama nema mata tsarin jiki, sannan kuma ta san dangin mahaifinta, tunda ba zuwa take ba"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Aliyu ka taho kawai, idan ka tsaya zai zama abin magana, ƙyaleta taho"
"Amma mama...