← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 174

Sashe 117

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*Paid book ne, ₦500 via 0009450228
Aishs adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143

A hankali ya rufe datarsa, ya yi shiruu yana tunanin mai ya yi wa mutane haka, da har wasu suka sanya rayuwarsa a gaba suka mayar da ita hanyar su ta neman abinci.

A hankali ya ajiye wayar ya kunna motarsa ya tafi.

Baba uwani ce durƙushe a gaban Mummy, jikinta sai rawa yake yi, Mummy ta dubi baba uwani ta ce "Uwani me ki ke nufi ne? Ƴan kwanakin nan duk wasu ayyuka da na sakaki ba kya iya yi mini, sannan babu wani rahoto da ki ke kawo mini"

"Tuba nake ranki ya daÉ—e, ayi mini afuwa, ayi mini aikin gafara".

Ta É—an ja numfashi ta ce "Yarinyar da aka ce ta zo da É—an wurin Adam an ce ta na zuwa gidan nan haka ne?"

Baba uwani ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Wallahi ba na ce ba uwar ɗakina, kin san yaron ko fito da shi daga sashin giwa ba ayi, babu wata hadima da aka amincewa zuwa in da yaron yake, ciki har da ni, dan haka ba na ce ba, amma akwai wata yarinya da take yawan zuwa, ban san alaƙarsu ba, amma zan iya cewa ita ce dan kuwa kwanaki na ji an ce za a kaita wurin mai girma turaki, amma abun da ya sa ban gazgata ita ce ba, yarinya ce fa sosai bana tunanin ita ce".

"Ba tunaninki nake son ji ba, abu É—aya zan saka ki, daga yau idan ki ka sake ganin ta zo, ki yi gaggawar zuwa ki sanar da ni, bana son ta zo ta bar gidan nan ba tare da na sani ba".

"An gama ranki ya daÉ—e, in sha Allah zan sanar da ke"

"Saura wannan karon ma ki tsaya shashanci, tashi ki bani wuri " jiki na rawa baba uwani ta tashi ta bar É—akin.

***
Jamil ne zaune a turakar turaki, bayan sun gaisa, ya É—an gyara zama ya ce "Allah ya taimake ka, wata magana nake son mu tattauna idan babu damuwa"
Turaki ya jinjina masa kai ya ce "Ina sauraronka".

"Dama na ce game da riƙon ɗan wurin aisha, a hannun giwa yaron zai zauna kenan su cigaba da riƙonsa?".

Turaki ya ce "Eh, wannan hukunci in da zai zauna mahaifinsa ne yakamata ya yanke, ya rasa matarsa bai kamata É—an kuma a saka masa ido a kan sa ba"

"Amma, ba kwa tunanin yana da kyau a sanya ido, idan maganar aure ta taso ya auri wadda za ta riƙe yaron da amana ta kula da shi?"

"Adam ba ƙaramin yaro bane ba, na san zai samo mace mai mutunci da kirki, ba zai auri wadda za ta cutar da yaron ba".

Jamil ya sake gyara zamansa ya ce "Amma ina ganin ku yakamata ku zaɓo wadda za ta maye gurbin aisha, kuma a ganina Samha ita yakamata ta maye gurbin aisha, a wannan karon yakamata a ba ta wannan damar"

Turaki ya É—an yi shiru yana nazarin maganarsa, ya É—ago ya ce "Ka zo da magana kai ma, amma ka bari zan yi tunani a kai, kuma zan yi magana da shi in sha Allah, Allah Ya sanya hakan ya zama alkhairi"

"Amin ya rabb, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"

Turaki ya jinjina masa kai tare da É—an yin murmushi.

Duk wani ƙoƙari da dagewa, rumaisa tana yi wurin ganin ta kawar da tunanin sabir daga zuciyarta, amma abu ya ci tura, kullum sake jin ƙaunarsa take da tunanin sa a cikin zuciyarta.
Idan ta tuno da maganganun adam sai ta ji ina ma za ta iya zuciya, ace ko kallon sabir ba zata sake yi ba, balle ta É—auke shi, amma ina sai ta ji ba zata iya ba, yanzu ma kawai daurewa take yi.
Gashi yanzu an ƙara mata tsaro, wataran mai sunan baba da kansa yake makaranta, islamiyya kuma tare da su huzaifa suke tafiya dan haka ba damar satar hanya. Haka za ta ɓoye ta yi kuka wasu lokutan dan tana kewar sabir sosai da sosai.

Yau asabar tana ta shirin tahafiz, mama ta ƙwala mata kira tana daga ɗaki.
Rumaisa ta shiga ɗakin, mama ta miƙa mata waya ta ce "Gashi Gwaggo ce za ta yi magana da ke".

Rumaisa ta karɓi wayar ta kara a kunnenta ta yi shiru.

"Hello rumaisa"

"Na'am".

"Ja'ira ki na ji na ba zaki yi magana ba"

Rumaisa ta ce "Ina kwana"

"Lafiya ƙalau, ya ki ke ya ƙarfin jiki?"

"Na ji sauƙi ai, har na koma makaranta ma"

"Ahh to Alhamdilillah, ya firgitar da ki ke yi fa cikin dare kin daina?"

"A'a ina yi wataran"

Gwaggo ta ce "Subhanallah, ki din ga addu'a sosai da sosai, dama zama a cikin wannan dajin ai dole ki yi gamo, wataƙila ma kin kwaso makarai. Zan saka a haɗo miki magunguna, a haɗo miki da kayanki a kawo miki".

Da sauri rumaisa ta tari numfashin Gwaggo ta ce "A'a gwaggo, kar a kawo mini kayan nan yanzu, ki ɗaure mini su, ki ɓoye su sosai, kar ki bari wani abu ya same su, zan gaya miki lokacin da za'a kawo mini"

"To shikenan babu damuwa in sha Allah, zuwa sati mai zuwa zan aiko miki da magunguna"

"Ni fa lafiyata ƙalau, ba wasu aljanu da na kwaso"

"Idan ma kin kwaso ai ke ba zaki sani ba, kuma idan aka kawo magani ki ka ƙi yi, da kaina zan zo har kanon na zane miki jikinki"

Rumaisa ta yi shiru, gwaggo ta gama maganganunta, ta miƙawa mama wayarta ta ɗau jakarta ta fice zuwa makaranta.

***
Ringing ɗin da wayarsa take yi ne ya sanya shi farkawa daga baccin da yake yi, a hankali ya yi miƙa ya buɗe idonsa, ɗan guntun tsaki ya ja, dan ya ji haushin katse masa barcin da aka yi.
Ya miƙa hannu ya ɗau wayar, ya ɗaga ya saka a kunnensa.
"Assalamu alaikum warahmatullah, barka da safiya"

"Yauwa barka" ya amsa murya can ƙasa.

"Ya gida ya ƙoƙari"

Cikin ƙosawa ya amsa da "Alhamdilillah, waye?".

"Khalifa Usman wakili ne, na kiraka ne domin yi maka ta'aziyya tare da jajanta maka abun da ya faru da kai".

"To ka saɓa lamba, ba wanda yakamata ka kira ɗin ka kira ba"

Khalifa ya ce "Na sani, ba Mahmud Sharif Galadima ba ne?"

"Eh, Adam sharif galadima yakamata ka kira"

"Ba laifi bane idan kai ma an yi maka ta'aziyya ai, abun da ya shafi adam ya shafeka"

"Kai ka ga, abun da ya shafe shi shi ya shafa, ku je can ku yi abun ku, don't ever involves me, ba na son fuska biyu, wataƙila da har zuciyarka da gaske ka ke ka kirani ka yi mini ta'aziyya sai in amsa maka, amma kowa ya san abun da yake tsakaninsa da mahaifinkaa da kai kanka, jiya mahaifinka yayi masa ta'aziyya a kafafen watsa labarai, kai kuma yau ka kirani wai kana yi mini ta'aziyya bana son munafuncinku na ƴan siyasa, kar ka sake kirana" ya yi tsaki ya kashe wayar ya ajiye.
Ya tashi zaune yana mamakin tsabar rashin kunya na wasu Æ´an siyasar, ya san da biyu ya kira shi, ba dan Allah ba.

Ya miƙe ya shiga banɗaki domin ya yi wanka.

Ya gama abun da yake yi, ya fito ya shirya, ya fita falo domin karya, a falon ya tarar da Samha da Fauziyya ga ruky da Mummy sai hira suke yi, kuma da alama hirar ta su na da alaƙa da takawa.

"Wai ku ba ku da wata magana sai ta mutum É—aya? Look for something else mana, kowa adam adam ku bar shi ya ji da abubuwan da suka dame shi".

Gaban Mummy ne ya faÉ—i, yaushe Mahmud ya fara damuwa da lamarin adam?.

Fauziyya ta ce "Kawai muna É—an yin hira ne a kan yadda abubuwa ke ta faruwa da shi, social media ma sai zancen ake yi".

"Ni ma yanzu wannan yaron ya kirani, É—an gidan wakili wai yana yi mini ta'aziyya, na ce kar ya sake kirana bana son munafunci da fuska biyu".

Waro ido Samha ta yi ta ce "Khalifa wakili kuma?".

"Shi fa, kar ma ya kuskura ya sakani a shirmensu ni buÉ—e masa aiki zan yi, rukky kawon breakfast zan karya"

'Mai wakili yake nufi da kiran Mahmud a waya wai zai yi masa ta'aziyya?' Samha ta tambayi kanta.

Tashi ta yi da sauri ta ce ta na zuwa, ta fice ta bar sashin zuwa harabar gidan, ta kira Khalifa a waya.

Sai da ta kira shi sau biyu sannan ya É—aga.

"Wai me kake aikatawa ne da ka ke ɓoyewa?"

"Kamar me fa?" Ya tambaye ta cikin ko in kula.

"Kai ka ke sponsoring ake ɓatawa adam suna a gidajen jaridu ko?"

"Meye shaidarki na ni nake hakan?"

Cikin fushi Samha ta ce "Waye idan ba kai ba?"

"A tunaninki ni kaɗai ne maƙiyin adam? Ai ba mahaifina kaɗai yake da burin tozartawa ba, dan haka bani da lokacin sponsoring ɗin wasu gidajen jaridu su ɓata masa suna".

"To me kake nufi da kiran ƙaninsa wai kana yi masa ta'aziyya, shi ma janyo shi zaka yi cikin tsiyar ta ka?"

"Wow, kuna tare kenan few hours da kiransa har kin samu labari"
Chapter 117 · 0% Book details