← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 174

Sashe 122

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haushi ne ya kama mama ta ce "Ke ubanki, kin tashi ko sai na zo?" Ba dan ta so ba, ta tashi ta É—aura zani ta nemi wuri ta kwanta.

Washegari da safe bayan tafiyar runaisa makaranta, suka yi waya da Abubakar, ya tabattarwa da mama cewa da azahar zai zo gida.

Mama ta ji daɗin zuwan Abubakar sosai da sosai, saboda ya fi mai sunan baba sauƙin kai, da sauƙin fahimta. Bayan ya ci abinci ya huta, mama ta gabatar wa da Abubakar halin da ake ciki na batun son auran rumaisa.

Abubakar ya nisa ya ce "To mama ai babu wani laifi a ciki, wataƙila a dalilin auren ki ga ta nutsu, ni kaina ba wai ina son a aurar da ita ba ne, amma bamu san mai Allah ya ɓoye a lamarin ba.
Dan haka mama ki yi ta Addu'a tare da istikhara, sannan kuma a nemi amincewar ta, idan ta yarda shikenan"

"Nima abun da nake tunani kenan, bana son takurawa a lamarin nan, mussaman yadda ake surutu a kan ta, kuma ina jin nauyin matar sosai. Amma dan Allah ka shawo kan É—an uwanka, dan shi ba ya son sabgar".

Abubakar ya ce "Karki damu mama, ki rabu da shi ki yi ta addu'a, idan da alkhairi Allah ya tabbatar mana"

Mama ta amsa da Amin.

Ammi ta cigaba da addu'a, tare da tsumayin jiran amsar da mama za ta bata.

***
Hajiya Lubabatu ce ta kawo wa mummy ziyara har gida, in da suka ƙule a ɗaki suna tattaunawa tare da shirya mugunta kamar yadda suka saba.

Hajiya Lubabatu ta ce "Wai dan Allah jamila zuwa yaushe zaki samo maganin nan mu koma wurin malamin nan?"

Mummy ta ce "Rabu da ni kawai, na saka wannan shashashar matar, ta kasa samo mini ranar a gabana aka fito da maganin aka yi masa amfani da shi, amma na kasa É—aukowa saboda suna wurin".

"To yanzu shikenan kin fasa cimma ƙudurin birkita shin? Tun da dai malam ya ce aikin da kika buƙata ba zai yiwu ba sai an samu maganin da ake yi masa amfani da shi"

"Ba fasawa na yi ba, yanzu dai kan wani abun na mayar da hankalina"

"Wane abu kenan?"

"Yarinyar da ta zo da É—ansa ce, Mahmud ya ce mini ya ganta a gidan nan, tana zuwa yarinyar ce da bakinta ta gaya masa, kuma har shi adam É—in ya ce kar a bari ta sake zuwa, idan da gaskiya mai zai saka ya ce kar a bari ta sake shigowa gidan nan? Kuma ba wannan ba kin san meya fi bani mamaki?"

"Sai kin faÉ—a"

Mummy ta gyara zama ta ce "Wai yarinyar yarinya ce ƙarama, ba babba ba ce ba, tayaya ƙaramar yarinya za ta kuɓuto da jariri, kuma ace an hanata zuwa gidan nan, ni fa ina tantama idan ɗan nan ma da gaske ɗan sa ne, da ƙyar idan ba wata ƙulalliyar suka shirya ba, na ji haushin rashin sanin yarinyar tana zuwa gidan nan tun a baya, da na san yadda zan na haɗu da yarinyar nan"

Hajiya Lubabatu ta ce "Kaii jamila, to ki yi mata me? Me za ta yi miki?"

"Ahh in samu bayanai mana, yadda zan kar giwa, in tona mata asiri".

"Ke ai ni lamarin giwar nan yana bani tsoro, hatsabibiya ce ta gaske"

Mummy ta ce "Ni zan gaya miki hatsabibiya ce ta gaske, shiyasa na yi alwashin kawo ƙarshenta"

Hajiya Lubabatu ta ce "Aikuwa sai mun cigaba da zagewa dan da alama ita ma a tsaye take, bari na tashi na tafi".

Suka yi sallama ta tafi.

Mama gaba ɗaya ta rasa ta ina za ta ɓullowa rumaisa balle ta yi mata bayani, ta san halin kayarta, idan ba ta so ba ana gabas tana yamma.

Abubakar ya samu suna tsaka da hira da shi da mai sunan baba, ya yi gyaran murya ya ce "Ni kuwa mama ce ta zo mini da wani zance"

Mai sunan baba ya ƙura masa ido, alamar yana sauraron sa.

"Mutanen da ta zo da yaronsu, suna son a basu aurenta"

"Kana goyon bayan hakan kenan?" Mai sunan baba ya katse shi.

Abubakar ya ce "Ba maganar ina goyon bayan hakan bane, makomar jaririn nan za a duba"

"Ita kuma ta ta makomar fa, karatunta da sauransu, kawai sai a aureta dan ta je ta yi raino, ita ba ta da ƴanci kenan? Ni dama tun da naga ana ta yi mata ɗawainiya na san akwai wata buƙatar da za su zo da ita, kuma guda nawa rumaisan take da za ayi mata aure yanzu?"

"Sunna ne a addinance ko ka manta Sheikh? Early marriage is better than early fornication, ko an gaya maka wannan tsalle-tsallem da take yana nufin jikinta ba ya jin komai na girma? Bai kamata mu yi saurin yin adawa da lamarin mu yanke hukunci ba, Addu'a yakamata mu yi.
Na san ka na sane da yadda ake yi da ita a gari, da mu baki É—aya, wanda bamu da damar hana mutane cigaba da yaÉ—a jita-jita wanda dole ya shafi rayuwarta.
Kuma batun karatunta bana tunanin wani abu ne da zai gagara, yanzu sai ka gama zaƙewar ita kuma ta ce tana so, mu yi mata fatan alkhairi, atleast za ta shiga gida mai daraja da muke sanya ran ya zame mata alkairi a rayuwa, kar mu rarrabawa mama hankali"

Har Abubakar ya yi ya gama, mai sunan baba bai kuma kulashi ba, dan shi sam baya goyon bayan lamarin.

Rumaisa tana shimfiɗa tana waƙe-waƙenta, mama ta kalleta ta ce "Idan kin gama shimfiɗar zan yi magana da ke"

"Innalillahi, Allah ya sa ba wani abun na yi ba"

"Ni dai na ce zan yi magana da ke"

Rumaisa ta ajiye abun shimfiÉ—ar, ta tafi gaban mama ta zauna ta ce "Gaya mini kawai hankalina ya kwanta"

Mama ta É—an yi shiru tana nazarin rumaisa, sannan ta numfasa ta ce "Ki na ji na ko?" Ta jinjina kai alamar eh.

"Waya muka yi da hajiya, kakar sabir"

Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Hajiya ammi".

"Eh, ta zo mini da wata magana ne, da dole sai da yardarki abun zai yiwu".

"Ni kuma, menene to?".

"Rumaisa, ta ce tana son ki auri baban sabir, É—anta adam"

"Eyeee wai wa? Ni ko wa?"

Mama ta ce "Da wa nake magana?"

Rumaisa ta ce "Taɓ Ubangiji Allah ya kiyaye, haka kurum duk ƙawayena ba ayi musu aure ba sai ni, sai ka ce a ƙauye, ba sai na yi tsawo na girma za ayi mini aure ba, sai ayi mini aure ina ƴar haka, to wallahi bana son shi, ba zan aure shi ba taɓ baki san wannan mutumin ba ne".

Mama ta ce "Wai meye haÉ—inki da shi ne me yayi miki?"

"Ni bana son shi ne, haka kurum idan aka yi mini aure na daina yawo yadda nake so, kuma wai fa komai ya ce sai na yi, to wallahi ni ba zai saka ni abu na yi ba, sai dai ya kasheni"

Mama ta ce "Yanzu dai a cewa hajiyarsa ba kya so kenan?"

Kai tsaye rumaisa ta ce "Eh"

"To shikenan, je ki kwanta sai da safe" rumaisa ta tafi wurin kwanciyarta, tana ta yatsine baki kamar takawan ne a gabanta.

Ita rumaisa jin abun ma ta yi kamar almara, ita banda a ƙauye ba ta taɓa ganin amarya yarinya ba, ko ta ƙauyen ma tafi ta girma, sai ita a wani ce za ayi mata aure, auren ma da maƙoyanta a fili ta ce "Taɓ Allah ya kiyaye, wallahi ba na son shi".

Mama ta ce "Ai kin gaya mini na ji ko"

"Au, na zata a zuciyata na yi maganar" har ta yi bacci tsaki take yi, da ganin an raina mata hankali.

Da safe ta gama shirin tafiya makaranta, ta saɓa jakarta ta fito tsakar gida, ta tarar da mai sunan baba a tsaye, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata ya ce wuce mu je. Ba ta ce komai ba ta yi gaba ya bi bayanta.

Suna tafe a hanya ya ce mata "Mama ta yi miki wata magana ne?"

Rumaisa ta ce "Eh mana, wai aure za ta yi mini"

"Ke me ki ka ce mata?".

"Ni dai na ce mata bana son shi, ai ba a yi wa yara aure"

Mai sunan baba ya jinjina kai ya ce "Good, zan tsaya miki duk yadda za ayi kar ki yadda da batun auren nan, ki ce ba kya so kin ji abun da na gaya miki ko?" Ta gyaÉ—a kai alamar eh ya ce "Good, idan kuma ki ka amsa zaki ga yadda zan yi da ke" suka cigaba da tafiya.

Ammi ta É—an fara tsorata da shirun da ta ji, dan har ga Allah tun da ta yanke shawarar ta ji abun ya shiga ranta sosai da sosai, gashi haryanzu mama ba ta ce komai ba, gashi ba ta son yawan takura musu da ta sake kiran waya.
Ko da ta yi wa adam zancen haryanzu gidansu rumaisa ba su ce mata komai ba ya ce "Ina ga basu amince ba, kawai ki ƙyalesu"

"A'a idan ka ga na ƙyale, to na ga ba yadda zan yi ne, ni lamarin ya shiga raina sosai, ina saka ran da alkhairi a ciki".

Adam a ransa ya ce Allah ya sa su ce a'a, dan shi har wata kunya yake ji idan ya tuna wai rumaisa za a aura masa.

Gidan mama kai ya rabu biyu, Aliyu yana cikin waÉ—anda suke murna da abun, dan dama shi yana shiri da takawa, yayin da mai sunan baba Abdalla da usman suma suka ce ba su yadda ba. Yasir da Huzaifa kuwa, ba su ce eh ba ba su ce a'a ba, yasir ya ce gara ta tattara a aurar da ita mu huta.
Huzaifa ya ce "Ni babban jin daɗina, gidan masu kuɗi ne, da wani ƙojalallen wahalallen ne wallahi ba zamu yadda ba, amma nan mu je mu ci kayan daɗi, wallahi dan ubanta sai ta yadda ba zata yi mini baƙin ciki ba"

Rumaisa ta ce "Oho muku, ni dai bana son shi, kome za ayi".
Chapter 122 · 0% Book details