Sashe 10
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Za ki tashi ko sai na yi ball dake?" Cikin hanzari ta tashi, ta É—auke katifarta ta nufi banÉ—aki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding É—in zai kaita kamar yadda ya ce. Gabanta ne ya faÉ—i ta fara tunanin ko ta gudu.
Kai tsaye ta nufi banɗaki, tana shiga ta tarrar da an haɗa ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe ƙofa ta hau wanka da shi.
Yasir ne ya nufo banɗakin da sauri, wuyansa ɗauke da soson wankansa, zai shiga banɗaki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga ƙofar a rufe.
Iya ƙarfinsa ya hau dukan ƙofar yana faɗin "wani ɗan rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?"
Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce "Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara.
Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun ƙofar.
Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta buɗe ƙofar banɗakin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya haɗa ruwa, Ruma ta zubar da komai.
A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce "Wallahi yau mai ƙwatarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini".
Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce "To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba"
Wani ranƙwashi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta durƙusa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.
Yaya Umar ya ɗaga labulen taga ya leƙo ya ce "Ƙyaleta tun da ka daketa" ba ƙaramin ɓaci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi haƙuri.
Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa riƙe da leda ya miƙa mata ya ce "Maza ki shirya ki wuce mu tafi"
Karɓar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur'ani ake yi da gaske ba wasa ba.
Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.
Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga É—akin Mama, ta saka uniform É—in jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba.
Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.
A zuciyarta tana ta addur Allah ya sa makarantar suce ba zasu karɓeta ba, bata tunanin ko su Huzaifa sun san za a sakata a makarantar su, dan da sun sani cewa zasu yi basu yadda ba.
Tun da suka shiga makarantar, tashin karatun Alqur'ani kawai ka ke ji, daga kowacce kusurwa, kuma da alama É—aliban makarantar a nutse suke.
A ofishin shugaban makarantar aka titsiye Ruma ana yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da ƙyar ta kai.
Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.
Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya hau ta da faɗa a gaban mutane.
Cikin kuka ta ce "Wallahi yaya na iya karatu"
"To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka ƙara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa"
Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji "Tiryan-tiryan da ƙira'ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntuɓe babu"
Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce "Ahh gaskiya 'yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz É—in, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu"
Yaya Umar ya ce "To masha Allah, haka muke so" aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji.
Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce "Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya" ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi faÉ—ansa ya gama ya tafi.
Gaba É—aya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna.
Gaba É—aya É—aliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.
"Ke ya ba kya karatun?" Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.
Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na É—alibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.
"Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba" ta bashi amsa kanta tsaye.
Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran É—aliban.
Ta dubi wata É—aliba ta ce "Ke, dan Allah nan aji nawa ne?"
ÆŠalibar ta kalli Ruma sannan ta ce "Aji É—aya ne"
"Kutmar, ban gane aji É—aya ba, kina nufin aji É—aya aka kawo ni?"
"Eh mana" yarinyar ta bata amsa.
Ruma ta jinjina kai ta ce "Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji É—aya ba".
ÆŠaliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta.
Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangyaÉ—i.
Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba.
ÆŠalibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta. Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam.
Tun da aka fita break da salla, wuri É—aya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu. Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.
Aka dawo aji aka ɗora da karatu babu ƙaƙƙautawa, gaba ɗaya Ruma ta gaji da zaman makarantar. Malamin ajinsu ya fara yi musu ƙari, ta buɗe Alqur'anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaɗinta.
Tun da Ruma ta shigo ajin É—azu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
Ƙarshe ta haɗa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta ɗau jakarta ta bar ajin.
Zagayawa take tana lelleƙa azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum ɗaya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ƙarfe ɗaya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.
Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan ƙarin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta "Huzaifa, dama nan ne ajinki tun ɗazu nake neman ku" gaba ɗaya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.
Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba "ka ganni a makarantar ku ko? Hmm É—an zo ka ji wata magana mana".
"Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?" Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.
"Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa" ta faɗa tana sake leƙo cikin ajin.
Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?.
Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce "Je ka ka sallameta"
Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haÉ—e rai ya ce "Uban waye ya kawo ki makarantar mu?"
Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce "Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba haƙuri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba".
"Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba".
"Saboda gani annoba ko?" Tayi maganar tana hararasa.
"To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?"
Ta yatsuna fuska ta ce "Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida"
Huzaifa ya ce "Lallai baki da hankali, to ke da gida sai ƙarfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaɗai"tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir.
Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.
Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami "Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaÉ—e"
"Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci"
Yasir ya dungure mata kai ya ce "Shegen ci kamar kazar hausa" suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.
Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur'ani, ana jiran wani malamin ya shigo.