← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 174

Sashe 147

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa gaba É—aya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan Æ´ar yarinyar takawa zai aura?.

Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ƙawayen amarya.

Babu zato babu tsammani, sai ga ƴan mazan mama sun dira a wurin, da shigar ƙananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.

Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.
Yasir ya ce "Taɓ, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?"

Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ƙaiƙayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan ɓata kwalliyar"

Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau"

Mamaki ne ya kama Æ´an wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.

Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ƙara gyara cake ɗin da yake kan table.

Rumaisa ba ta taɓa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.

Gaban table ɗin ya ƙarasa, kusa da iman ya ɗauki ƴar ƙaramar wuƙar yanka cake ɗin, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buɗe bakinta, ta buɗe kaɗan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ƙanwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake ɗin idonta ya cika da ƙwalla.

Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haÉ—e rai ranar aurenta"

Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ƙoƙarin yin abun da zai kwantar mata da hankali.

Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba ɗaya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a ɓangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haɗa ido, gabanta ya faɗi.

Ƙarshe dai da su aka gama partyn, suka ɗauki ƙanwarsu suka yi gida.

Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.

Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.

Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.

"Me ki ke jira baki tafi gida ba?"

A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho".

"Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command.

Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.

Ayshercool
08081012143
What's app only please
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*.

Adam bai taɓa ta ba, sai bin ta da ya yi da kallo, idanuwanta na neman su kakkafe, sai daddagewa take yi, jikinta yana cigaba da tsuma.

Usman ya ce "Lafiya kuwa?"

Mai sunan baba kuwa wani irin takaici ne ya mamaye shi, ganin rumaisa a jikin Adam gaba É—aya.

Takawa ya ce "Ban san meya sameta ba, gani na yi ta haÉ—a kai da gwiwa tana bacci, kawai ta zabura ta faÉ—o jikina".

"Iman! Iman ba ta da lafiya fa, Iman ba ta da lafiya" ta yi maganar cikin surutu da magagi.

"Wace kuma iman?" Mai sunan baba ya tambayeta a ƙule.

Haushi ne ya kama Adam, saboda yadda mai sunan baba ya raina wa kansa hankali, wai wace kuma iman, ya lura da yadda yake a ƙule, dan haka ya ture rumaisa daga jikinsa, ya ja da baya.

Mama tuni ta fito tsakar gida, dan jin abun da ya faru, amma ta kasa ƙarasawa soron, saboda jin nauyin adam.

Sosai take kuka tana neman abun riƙewa, "Iman fa, na gaya muku ba ta da lafiya"

Mai sunan baba ya saka hannu ya É—agata tsaye, amma jikinta ya riga ya saki, tana neman ta faÉ—i.
"Ki buÉ—e idonki menene?" Ta sake rintse idanunta, kamar mai tsoron ganin wani abu.

Cak ya É—agata ya shiga da ita cikin gidan, ya kwantar da ita a tsakar gida, gaba É—aya suka rufu a kanta.

Adam har yayi niyyar tafiya, sai ya ga idan yayi haka bai kyauta ba, mussaman da ya ji tana ta ambatar sunan Iman.

Sallama ya yi ya shiga, ya tarar da su a kanta, mama tana girgiza ta, tana tambayarta menene.

Idonta dai a rufe, tana ta zubar da hawaye, ta ce "Iman, ba ta da lafiya sosai da sosai"

Mama ta ce "A'a jikinta da sauƙi ai, har an sallameta daga asibiti, tana gida".

Ta É—aga hannunta ba tare da ta buÉ—e idon ba, ta É—ora shi a saitin zuciyar mai sunan baba, idonta a rufe ta É—aga kai in da yake ta ce "Mai sunan baba, ka ji bugun zuciyarka, ai kai ka yadda ba ta da lafiya ko? Ku yi mata Addu'a dan Allah kar ta mutu".

Ya ce "To, kema ki yi addu'a"

Takawa ya É—an yi gyaran murya ya ce "Ni zan tafi, Allah ya bata lafiya"

Mama da sai a yanzu ta lura da shi, ta ce "Yi haƙuri mai babban suna, wallahi tun da aka yi garkuwa da ita na kasa gane kanta, ina ga wani abun ta kwaso a zaman dajin da ta yi".

Adam ya ce "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, abun ya bani mamaki, lafiya take zaune, ta ce idan ban ci abincin da ta kawo ba, an ce za a zaneta, da ban ci ba sai ta ci, ta ce ba za a gane ba, sai ta haɗe kai da gwiwa tana bacci, shikenan kuma ta fara ihu" yayi maganar cikin ƙoƙarin wanke kansa, yadda gaba ɗaya ƙartan nan suka zubo masa ido,sun ga ƙanwarsu a jikinsa, ga mai sunan baba sai muzurai yake yi.

Mama ta ce "Bakomai wallahi".

Usman ya ce "Lallai yarinyar nan baki da mutunci, dama zuwa ki ka yi ki ka cinye abincin?"

"Ba cinyewa na yi ba, dama ba na gaya muku ba zai ci ba, na san halin sa fa hmmm" ta yi maganar kamar wadda ta sha ta bugu.
Duk suka tsira mata ido, ta miƙa hannu tana yi wa adam nuni da ya zo.
Chapter 147 · 0% Book details