Sashe 158
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƴan uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce "Dama ɗaki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida".
Da sauri rumaisa ta ce "Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama".
Adam ya ce "Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a É—an tayata zama"
Gwaggo ta ce "A'a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga saƙonki nan babarki tana gaishe ki"
Tashi rumaisa ke ƙoƙarin yi, amma ya riƙeta, ya hanata tashi.
"Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?" Ta yi maganar tana kuka.
Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo.
Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya"
Ta ce "Babu komai, Allah ya sanya alkhairi"
Ya ji daÉ—in tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba.
Ɗago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faɗin "Is ok, yi haƙuri kukan ya isa haka"
Ƙoƙarin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ƙyaleshi.
Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koÉ—a yadda gida yayi kyau.
Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce "Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taɓa zaton zaka auri ƙaramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ƙaramar yarinyar ce ta kuɓuta da Sabir, daga hannun 'yan bindiga"
"Ai babu mamaki a ikon Allah, ƙanƙantarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saɓawa shari'a ba".
Ta kalli rumaisa ta ce "Sannu Æ´ar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan É—auka"
Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama.
Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara.
Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faÉ—e-faÉ—en maganganun su, da yada habaici.
Da azahar É—in kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana.
Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi.
Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata É—akinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe É—in ta, ga su iman nan, su tayata a haÉ—a mata É—akin.
Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi.
Tana ƙoƙarin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce "Bar shi, zan yi da kaina"
Kallonta suka yi gaba É—aya,Nusaiba ta ce "Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so"
Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi".
Nusaiba ta ce "To shikenan, baba uwani ƙyale mata".
Adam ya shigo É—akin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan.
Nusaiba ta ce "A'a ta ce a ƙyale mata, za ta yi abun ta da kanta".
"Shikenan, ku ƙyale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la'asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba".
"A'a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?".
Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce "Do as i said"
Baba uwani ta yi mamakin yadda ƙiri-ƙiri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa taƙi. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo.
Sannan ta yi mamakin yadda suka haɗu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara ɓoye mata wasu abubuwan.
Kan su ƙarasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ƙarasa gida.
Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce "Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi".
"Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru".
Iman ta ce "Ammi kin san me?"
"A'a sai kin faÉ—a".
"Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ƙyalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun 'yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama"
Ammi ta yi shiru ta ce "Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam da rumaisa, sai ya bawa mara É—a kunya in sha Allah".
Nusaiba ta ce "Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wataƙila Mummy ce zata saka su, ai daɗinta maman Sabir ɗin ma ba kanwar lasa ba ce".
Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faÉ—a sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa'a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya.
Mummy ta kalleta ta ce "Ya aka yi?".
"Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ƙyalle, ya ce wannan tsohuwar al'ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya....
Samha ta ce "Dakata, ƙarya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ƙarya yake babu abun da ya faru"
Mummy ta ce "Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace".
Ta risuna ta ce "In sha Allah uwar É—akina".
Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window É—akinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo.
A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ƙasan bene bata taɓa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ƴan gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta ɗan rage damuwa, da yin la'asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta.
A kwana na huÉ—u ya lura, tana gujewa haÉ—uwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai.
Bayan sallar magariba ya shiga É—akinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru.
ÆŠaga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya.
Ƙasan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ƙasan benen.
Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buÉ—e gaban motar ya ce ta shiga.
Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar.
Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huÉ—u, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan.
Security light duk ta haske ko ina a gidan.
Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.
Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.
Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita"
"Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta"
Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.
Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki"
Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman".
"Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai"
"To ni kaÉ—ai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka"
Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga É—ebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta".
Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, É—auke da Sabir a hannunta.
Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman"
Rumaisa ta ce "Mata ina wuni"
Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa"
Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu.
Adam ya ce "Kai, kwana huÉ—u baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki É—auke shi"
Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.
Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir.
Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haÉ—o mini kayansa, na tafi da shi ko?"