← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 174

Sashe 45

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jabir ya É—an yi gyaran murya ya ce "Ka ga dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka san ba a rasa irin waÉ—an nan a social media yaran talakawa ne kawai marasa tarbiyya amma dan Allah kawai ka share"

Takawa ya kalli Jabir ya ce "Ka kira mini Sidi na ce"

Jabir ya girgiza kai, wasu lokutan takawa akwai kafiya da gardama, da ga ganin comment É—in mace ce, kuma koma menene ba zai huce ba tun da ta riga ta yi.

Ya lalubo lambar sidi, ya kira masa shi, ya bashi wayar.

Cikin zafin zuciya ya karɓi wayar, ya yi wa sidi bayanin abin da yake son ayi masa.
Yana gama wayar, ya jefa wa Jabir wayar, ya fice daga É—akin gaba É—aya.

Sosai samha ta ɓata lokaci wurin yin kwalliya, kasancewarta 'yar ƙwalisa, sai dai babbar matsalarta ta ƙware a iya shigar banza, tun da garin Allah ya waye, bayan sun kammala waya da khalifa ta ji ta na son ganin takawa, dan haka da la'asar ta shirya ta tafi gidan, domin ganinsa.

Sai dai cikin sa'a, da ta shigo kan ta kai sashin Ammi, ta ga takawa ya taho fiuuu. Yanayinsa na rashin walwala bai sanya ta damu ba, balle ta saurara da abin da ta yi niyya.

Kai tsaye ta tunkari in da yake, ta fara yi masa magana, ko kallon in da take bai yi ba, yayi gaba abin sa, mamaki ne ya cikata, amma ba ta haƙura ba ta bi bayansa zuwa sashin Ammi, sai dai a sashin Ammi ma bai tsaya a falo ba, ya wuce ciki. Gaba ɗaya zuciyarsa a cunkushe take, an daɗe ba a gaya masa abin da ya ƙona masa rai kamar wannan comment ɗin ba, danganta shi da sata ba.
Samha kuwa gani tayi da kunya ta bi bayan takawa.
Nusaiba ce ta fito cikin shiri, da alama fita za ta yi, tayi arba da Samha a falo a tsaye.

"Ya dai na ganki a nan a tsaye, ko zama baki yi ba?" 'yan kame-kame Samha ta hau yi "Amm, dama takawa yana nan ne?"

"Ban sani ba, amma meyasa ki ke nemansa?"

Tsuke fuska Samha ta yi ta ce "Ina ruwanki da dalilin da ya sanya nake nemansa, ba abin da ya shafe ki bane"

"Haka ne, amma kamar yayi banbarakwai da yawa, ko kin manta waye shi a wurinki, Anty Samha ai ana barin halak dan kunya"

"Shut up! Na ce miki akwai wani abu ne a tsakaninmu, kin san bana son raini ko? Kuma ko ba komai ai takawa É—an uwana ne" Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya taimaka" ta wuce ta bar Samha a falon.

Samha ta damu ta ga Adam sosai da sosai, domin samun ƙwarin gwiwar yanke hukunci a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi.

Fitar Nusaiba babu daɗewa, Samha na tsaye na ta tunani, ma'aikatan sashin Ammi babu wanda ya tanka mata tun bayan gaisuwa, saboda sun san halinta na dizgi da wulaƙanta mutane da cin zarafi.

Iman ce tayi sallama a cikin falon, kamar kullum tana ganin Samha gabanta ya faÉ—i.
Salo-salo kamar mara lafiya iman ta ƙaraso cikin falon, ta kalli Samha ta ce "Anty Samha ina wuni?"

Samha ta ɗago kai ta kalli iman, ta yamutsa fuska, ta tsani iman fiye da yadda ta tsani 'yar uwatta. Ta ko ina iman kyakywar ce, ko da kwalliya babu, ko a wani yanayi yarinyar kyau ne da ita, ko kuka ko dariya, ko fushi ko fara'a komai kyau yake mata, ga tsananin kusanci da yake tsakaninta da takawa, bayan ɗaya katangar da ta yi mata shamaki da cimma burinta da take ta ƙoƙarin rusheta, iman ma wata babbar matsala ce a gare ta, dan duk tsanani akwai aure a tsakanin ta da takawa. Ba ta sake tabattar da Iman matsala ce a gare ta ba, sai da samarin 'yan matan gidan suke zamewa su ce suna son iman, sai da su Fauziyya suka yi da gaske, wurin damɓara mata mummunan fenti, da yayi mugun taka rawa wurin rusa farincikin rayuwar iman sannan suka samu sauƙi, ga yarinyar sumi-sumi kamar munafuka, tana da sanyin hali, nutsuwa da kuma girmama mutane, shiya sanya kowa yake sonta, ban da yanzu ma da ake janye jiki daga gare ta.

"Anty Samha, wai ya na ga kina ta kallona? Me na yi kuma?"

Wani mugun kallo ta yiwa iman ta ce "Zan yi maganinki ne, magani na har abada, idan har baki bar sabgar takawa ba" iman na shirin magana, Ammi ta fito da sauri daga sashenta tana ƙwalawa iman kira.

Ganin Ammi a ruÉ—e ya sanya iman bin Ammi da sauri, ba tare da tunnin komai ba, Samha ma ta rufa musu baya.

A ɗakin Ammi suka tarar da takawa a sheme a ƙasa.

Cikin ruÉ—u Ammi ta ce "Iman ina maganin sa"

Cikin rawar jiki iman ta ce "Ammi me aka yi masa kuma ciwon ya tashi?"

"Ban sani ba, kawai yana shigowa ya faÉ—i yi sauri ki É—auko".

"Kin san ya daɗe ciwon bai tashi ba, sai na binciko shi a in da na ɓoye, bari na ɗauko"

Samha ta ce "Ammi meya same shi ne?"

"Bashi da lafiya ne" Ammi ta bata amsa a taƙaice.

Iman ta ɗan jima sannan ta kawo maganin, wani mai ne a doguwar kwalba ta zo da shi, ta buɗe tana shafawa takawa a goshinsa, jikinsa sai wani irin rawa yake yana ƙamewa kamar mai farfaɗiya.

Iman ta dinga shafa masa tana karanto adduoi daban-daban, kusan mintuna goma sannan ya daina abin da yake yi, da kansa ya tashi ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya je ya hau kan gadon Ammi ya kwanta ya rufe idonsa.

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ammi bari na tafi, dama mama ce ta aiko ni wurin Mummy, na biyo na gaishe ki, bari na tafi Allah ya ƙara lafiya".

Har samha zata fita, Ammi ta kirata, Samha ta dawo gaban Ammi.
Ammi ta riƙo hannun Samha ta ce "Dan Allah Samha kar ki gayawa kowa takawa bashi da lafiya, waɗanda suka san yana da wannan rashin lafiyar sun zata tuni ya warke, dan Allah ki rufa mini asiri, ki yi shiru da bakinki" Ammi tayi maganar kamar zata yi kuka.

Cikin kulawa Samha ta ce "Ammina, kar ki damu, babu wanda zan gayawa in sha Allah, rufin asirinki ai namu ne, ba wanda zai ji in sha Allah "

Ammi ta jinjina kai, ta yiwa Samha godiya, iman kuwa tausayin Ammi yakamata, ammi haryanzu ba ta san halin samha ba, ko da yake ba wanda zai yadda da samha fuska biyu ce da ita.

Jiki a sanyaye Samha ta wuce sashin Mummy, sai dai sashin na ta shiru babu kowa. Kai tsaye ta nufi É—akin Mummy.
Ta tarar da mummyn na waya, ta samu wuri ta zauna tana jiran ta kammala wayar.
Mummy ta kammala wayar ta dubi Samha ta ce "Samha 'yar ƙwalisa, ya aka yi ne, na ga duk jikinki a sanyaye?"

Samha ta dubeta ta ce "Mummy, wai dan Allah baki da masaniya a kan rashin lafiyar Adam?"

"Wace rashin lafiya kuma?"

"Rashin lafiyar da ake cewa yana da ita, yau na gani da idona"

Mummy ta waro ido waje ta ce "Ki na nufin bai warke ba dama?"

"Eh, mahaifiyarsa ta nemi na yi shiru da bakina, amma na kasa jurewa, sai da na ga iman tana ta shafa masa wani abu a fuska, sannan ya tashi, anya Mummy babu hannunki a ciki?"

Mummy ta yi wani murmushi sannan ta ce "Samha kenan, ke idan da hannuna a ciki zan kasa gaya miki ne, ai da ko a wurin mahaifiyarku zaki ji, babu ruwana a cikin lamarin nan, ni ban ma san haryanzu yana da wannan ciwon ba, a zatona tuni ya warke"

Samha ta rausayar da kai, sannan ta miƙe tsaye ta ce "Na tafi, dama sauri nake" bayanta mummy ta bi da kallo, sannan tayi wani irin murmushi ta ce
"Yarinya man kaza, wannan labari yayi mini daÉ—i da ki ka zo mini da shi, dama na daÉ—e ban ji labari mai daÉ—in wannan ba. Zan cigaba da amfani da wawancinki ina ruftaki, dole in je gidan Galadima, sai Hajiya Luba ta ji wannan zancen"

****
Ruma kuwa tuni ta manta abin da ta yi, dan ba ta ɗauki abin da tayin wani abu mai muhimmanci ba, sabgoginta ta cigaba da yi, sai dai tana iya ƙoƙarinta yanzu a kan kar ta yi wani abun da zai kuma haɗata da mai sunan Baba, dan karonsu babu daɗi sam.

***
Kamar ko yaushe, haka yanzu ma muryarta ta yake ji a kunnuwansa, a hankali ya buÉ—e idonsa, yana son tabattar da a ina yake, abin da ya iya tunawa shine ya shigo cikin gidan sashin Ammi, amma daga haka bai iya tuna komai ba.
A hankali kunnuwansa suka jiyo masa muryar Ammi tana karatun Alqur'ani.
Ya juya, ya kalli Ammi, ta na sanye da hijjabi, iman kuma ta ziro masa ido tana kallonsa.

Da sauri iman ta ce "Ammi ya farka"

Cikin kulawa Ammi ta dube shi, ta É—ora hannunta a goshinsa tana yi masa sannu.
Ya jinjina kai, Iman ma ta shiga jero masa sannu yana jinjina kai.

"Takawa, duk da na san ba ka so, amma ya zama dole ka yi haƙuri mu cigaba da neman magani, a baya abu ya lafa amma Kwatsam yau sai gashi ka faɗi, dole mu yi wani abu a kai kafin a farga a samu abin faɗa.

Shiruu Adam ya yi yana sauraron Ammi, ba tare da ya iya cewa komai ba.
Ammi ta kalli iman ta ce "Auta, duk da bani da matsala da ke, amma ke ma ki yi shiru, ko waccan ruÉ—aÉ—É—iyar Nusaiba kar ki gayawa"

Iman ta ce "In sha Allah Ammi, bari na je na mayar da maganin".

Zuwa washegari takawa ya ware, kamar ba shi ba,  ya cigaba da azalzala a kan a nemo masa mamallakin account ɗin nan da aka ce masa ɓarawo da shi.
Chapter 45 · 0% Book details