← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 174

Sashe 128

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa mita a cikinta, kamar an yi mata gori, yau wuni ta yi tana cigaba da mitar abubuwan da ake yi mata a unguwar nan, mama tun tana yi mata nasiha tana cewa ta bar wa Allah, har ta yi mata banza ta ƙyaleta, Abdallah ya sakata a gaba yana cigaba da kunnata, tana mita. Bayan fitar Abdallah rumaisa ta shiga ɗakinsu, ta duba wurin da yake ajiye fensiransa na zane kasancewar sa architect.

Ta zauna ta nutsu sosai, ta hau zane-zane.

Mama ta ce "Uban me ki ke yi musu a É—aki, ki ka shiga ki ka yi shiru?"

Rumaisa ta ce "Bakomai"

"To fito musu daga É—aki, tun basu dawo sun tarar da ke ba"

"Mama zan fito ina zuwa"

Sai da ta gama abun da Allah ya nufeta da yi, sannan ta fito ta fice ba tare da sanin mama ba.

Maƙwabciyarsu ta zana, kuma zanen ya fita sosai, ta yi headline da munafukar unguwa, a ƙasa ta rubuta by Rumaisa Mahmud ƙanwar maza. Ta je ta liƙe a ƙofar gidan matar, ta nausa ta tafi gidansu Habiba, ba tare da mama ta san ta fita ba ma.

Ayshercool.

paid book ne, ₦500 via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

*KANWAR MAZA*

*39*

*PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

Jin shirun yayi yawa ya kuma sanyawa mama ta ƙwalawa rumaisa kira, amma har ta kira kusan sau uku shiru, ba ta amsa ba, mama ta kaste abun da take yi, ta fita domin duba me rumaisa take aikatawa ta ji shiru. Sai dai da ta fito tsakar gida babu rumaisa ba alamarta.
Mama ta leƙa ɗakin ƴan maza, amma babu rumaisa ƙarshe ma sai shiga Maman ta yi ta kwaso kwanukan ta, da suka kai ɗakin suka bar su, ta fito ta duba banɗaki da kitchen duk babu rumaisa, tsayawa ta yi tana tunanin ina rumaisan ta tafi ba ta gaya mata ba?.

Tana cikin jimamin in da rumaisa ta tafi babu izininta, shamsiyya maƙwabciyarsu ta yi sallama, ita da wata mata.
Mama ta amsa musu cikin sakin fuska, ba tare da nuna mata ta san ta yi wa ƴarta ƙage ba.

"Maman rumaisa ni ba zama zan yi ba, ki shiga tsakanina da yarinyar nan, kalli abun da ta yi mini jiya a fuskata, da ɓarnar da ta yi mini a cikin gida, maigidana ya kawo ƙararta, ƙarshe ba wani mataki da kuka ɗauka, sai ma cin mutumci da ya biyo baya, yau kuma ta je ta yi zane ta liƙe mini a ƙofar gidana ya ƙi fita, wai munafukar unguwa, me na yi muku haka ne?"

Cikin dattaku mama ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yaran zamani ne sai godiyar Allah, wallahi da kaina na yi niyyar shigowa na baki haƙuri, wallahi ban san ta yi ba, kin san dai ni ba zan goyi bayan ta yi wannan rashin kyautawar ba, ban san ta yi miki ba, dan Allah dan annabi ki yi haƙuri, bari ta shigo gidan, zan hukunta ta kuma zan sanya ta je ta cire, dan Allah ki yi haƙuri"

"Wallahi banda ina jin nauyinki, Allah da sai na kama rumaisa na yi mata shegen duka".

Mama ta ce "Ashsha, ba za ayi haka ba, ai ke ma ƴarki ce, yanzu kina taɓata komai zai ɓaci, yayyenta ba sa ganin laifinta, amma dai ina baki haƙuri, da kaina zan hukunta ta, kuma zan aikota ta baki haƙuri".

Haka Jamila ta yi ta farfaɗar maganganu, mama tana bata haƙuri, da alwashin hukunta rumaisa, bayan tafiyarta mama ta dafe kai, haryanzu rumaisa babu alamar hankali a tare da ita, tuno damben da suka sha da ƴar ajinsu ta yi, abu har wurin ƴan sanda saboda wannan shegen zane-zanen da take yi, shi kansa Abdallah dan ba yadda za ta yi da shi ne, abun da yake karanta kenan, ga rumaisa na neman gadarsa, in dai zane-zanen banza da na wofi ne, a litattafan makarantar ta ma yi take.

Mama ta rasa mai ma yakamata ta yi, ba ta san ta ina zata fara neman rumaisa ba.

Rumaisa kuwa gidansu habiba ta tafi, suka shantake suna ta hira, ta bawa habiba labarin abun da ta yi wa maƙwabciyarsu.
Habiba ta ce "Kin mini daidai, da nice ba zan iya ba, tsoro nake ji, kin ji yadda matar nan ta din ga yayata maganar nan a cikin unguwar nan, ummanmu ce ta fara taka mata burki ta ce ƙarya take yi, daga nan ta je ta gayawa mamanku"

Rumaisa ta ce "Hmm, ai sai ta gane ba ta da wayo kan ma bar unguwar nan, da ina mutunta ita da mijinta, amma tun da ta taɓo ni, za ta gane bata da wayo"

Cikin rashin fahimta habiba ta ce "Ki bar unguwar nan ki koma ina?"

Rumaisa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Ke share kawai, na san zuwa yanzu wataƙila ta je ta kai ƙarata gidanmu"

"Me ki ka yi mata?"

Cikin ƙwarin gwiwa rumaisa ta ce "Zanata na yi, na rubuta munafukar unguwa, na liƙe mata a ƙofar gida, na san yau za a azabtar da ni a gida, amma ba zan koma yanzu ba"

Habiba ta ce "Wai ruma ba kya jin tsoro ke? Mama ba ta san kin zo nan ba?"

"Ba ta sani ba, idan aka kai ƙarata ina gidan, a gabanta mama zata bani rashin gaskiya, duk da abun da ta yi mini, zuwa yanzu kuwa na san ta tafi, in koma gida a haɗani da mai sunan baba, ya bani gwale-gwale"

Dariya habiba ta yi ta ce "Wato ke har ma kin san me za ayi miki, ina yaya Aliyu?"

Rumaisa ta yi mata kallon ƙasan ido ta ce "Yana makaranta, in ce kina nemansa ne?"

Habiba ta waro ido ta ce "Ke a'a, kawai dai tambayarsa na yi"

"Meyasa duk cikin yayyena shi ki ka sani?"

Habiba ta ce "Bakomai, ya na da kirki ne"

Rumaisa kawai ta yi dariya, tana lissafa yadda zata wanye da mama idan ta je gida.

Mama kuwa sai kallon agogo take yi, tana lissafa, ina rumaisa ta tafi haka? Ta ƙi dawowa, zuciyarta ta bata saboda abun da ta aikata ne ya sanya ta fece.

Kasancewar azahar ta yi, kuma juma'a ce ya sanya Æ´an samarin mama dawowa gida, domin shirin masallaci, kuma aka yi sa'a ana public holiday, rumaisa ba makaranta ta je ba.

Faɗan Abdallah mama ta jiyo, yana faɗin "Uban waye ya taɓa mini kayan zanena, bana son rashin mutunci, Huzaifa ban hanaku taɓa mini kaya ba?"
Huzaifa ya ce "Ni na iya amfani da wannan abubuwan naka ne? Sai dai ko Yasir"

Yasir ya tari numfashin Huzaifa ta hanyar cewa "Saboda ni ka raina ba, yaushe na zauna a gidan balle na taɓa masa kaya".

Mama ta fita tsakar gida ta ce "Ba aikin kowa bane, rumaisa ce ta taɓa maka, ita ta shiga ɗakin ta yi shiru, ita ce ba wani ba".

"Tana ina, sai ta ci ubanta yau sai na zaneta, har da gum É—ina ta buÉ—e ta bar mini a buÉ—e"

"Hmm, wannan yarinyar ai sai fatan shiriya, ina fatan Allah ya sanya auren nan ne mafi alkhairi, ko yau aka ce za ayi zance a É—aura su tafi da ita"

Abdallah ya ce "Tana ina?"

Mama ta ce "Ina na sani, ta yi wata aika-aikar ta gudu, ban ma san ta fita ba".

Yasir ya ce "Kai wannan yarinya, Allah ya yi mata maganin abun da yake damunta yake sanyata rashin ji".

Rumaisa ba ta tashi tafiya gida ba, sai da unguwa ta yi tsit, duk an tafi masallaci, sannan ta nufo gida, cikin shirin karɓar kowane irin hukunci za a yanke mata.

Da sallama ta shiga gidan, ta yi sa'a mama tana salla, ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta zauna, tana jiran mama ta idar, ta shirga mata ƙaryar da zata kare kanta.

Mama tana jin motsin rumaisa, amma ta shareta, ko da ta idar da sallar ma ta yi lazumi, ba ta tankawa rumaisa ba.

Cikin tsoro rumaisa ta ce "Mama" banza tayi da ita ta shige uwar É—aki ta bar rumaisa.

Tun rumaisa tana É—ar-É—ar har ta É—an saki jikinta, da ta ga mama ba ta da niyyar kulata.
Sai dai ba ta ankara ba, mama ta shammaceta, ta janyota ta din ga É—irka mata dundu.

Ihu rumaisa take yi, tana neman agaji rabon da mama ta daketa har ta manta.

Tun daga waje Yaya Abubakar ya jiyo ihun rumaisa, a soro ya yasar da sallaya, ya shiga da gudu, ya tarar da mama ta samu mafici, tana jibgar rumaisa tana yi tana haÉ—awa da hannunta.

Ai da hanzari ya ƙwaci rumaisa yana faɗin mama lafiya.

"Rabu da ni, yau yarinyar nan ta kaini bango, rumaisa a rayuwarta ba zata bari na huta ba, daga wannan sai wancan, gidan ubanwa ki ka tafi?"

Cikin kuka rumaisa ta ce "Gidansu habiba"

"Gidansu habiba gidan ubanki ne? Wato kin san abun da ki ka aikata ko?, To fita ki je ki bata haƙuri, ki cire takardar da ki ka liƙe mata a ƙofar gida, tun kan na murɗe miki wuya ki mutu in huta, da ɗaukar maganar da ki ke yi, kullum nike nan cikin bayar da haƙuri da faɗa da mutane saboda ke?
Bari na kira babar adam É—in a waya, idan sun shirya ko jibi su zo a É—aura auren nan na huta na gaji" Rumaisa ta yi fici-fici da ido tana kuka.

"Ba zaki fice ki je ki bata haƙuri, ki cire abun da ki ka liƙa mata ba?" Ruma ta fita da sauri, tana jin haushin sake kai ƙararta da matar ta yi.

Ta je ta yi iya ƙoƙarin ta, wurin cire cardboard paper da ta yi zanen a jiki, amma gum ɗin da ta yi amfani da shi ya kama sosai, dan haka ta samo wata ƙusa, ta dinga durzawa takardar, ta haɗa da sabon fentin da aka yi wa ƙofar duk ta kankare abun ta, sannan ta shiga cikin gidan matar.

Ta tsaya daga soro ta yi sallama, matar ta amsa sannan ta fito, ta sakawa bakinta da goshinta shanshanbale, in da rumaisa ta fasa mata da dutse.
Chapter 128 · 0% Book details