← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 174

Sashe 77

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nusaiba ta ce "Uncle J ina kwana?".

"Lafiya lau, ya gida ya Ammi?"

"Ammi na lafiya, ta fita ne".

Jabir ya mayar da idonsa kan Iman ya ce "Iman, ashe baki ji daÉ—i ba, ya jikin?"

Cikin yanayinta na rashin son magana da kuma ƙosawa ta ce "Da sauƙi"

"Allah ya baki lafiya autarmu, duk na kasa sukuni tun da aka ce mini jikinki ya motsa, amma na yi mamakin da na ganki a gida, takawa ba za a kaita asibiti ba?".

"Eh na za a kaita ba, amma tun da ha ka ka zo, sai ka kaita?".

"Kar ka gaya mini magana mana, daga tambaya, dole na tuhumi yadda ake nema ayi sake da lafiyar auta". Haɗe rai iman ta kuma yi, ba ta ce komai ba, dan gaba ɗaya ta ƙosa da zaman.
Samha kuwa da zancen iman ya fara ƙular da ita, ta yi gyaran murya ta ce "Takawa duk ka rame wallahi".

Jabir ya ce "Ba dole ba, ya sanya tunani da damuwar a ransa, gaba É—aya ya koma wani iri".

Samha ta din ga zubo zance, amma takawa ya ƙi kulata, ya kashingiɗa yayi musu shiru.

Iman ta ce "Ni dai zan koma É—aki jiri nake ji, sai anjimanku".

Takawa ya kalleta ya ce "Ko na mayar da ke É—akin?".

Samha ta yi zumbur ta tashi, ta nufi iman ta na faÉ—in "Haba dai, gani a zaune, bari na rakata tun da jiri take ji" sai da gaban iman ya faÉ—i, sam ba ta so haka ba, dan ta san da biyu ta ce zata kaita É—aki.

Ta rungumi iman, ta nufi sashin Ammi da ita, iman ta ce "A'a É—akina zan koma".

Samha ta ce "Bakomai, bari na rakaki" tayi maganar kamar gaske.

Sai da suka shiga ɗakin iman, sannan ta taƙarƙare, ta hankaɗa Iman kan gadon, ba tare da tausayin halin da iman ɗin ke ciki ba.
Ta murtuke fuska ta ce "Ke 'yar tsintuwa, kalleni da kyau, ya muka yi da ke?".

"Anty Samha me na yi miki?".

Cikin ƙulewa Samha ta ce "Ke fa tsohuwar munafuka ce, kullum na yi magana sai ki ce mini, ke babu komai a tsakanin ki da takawa, amma kullum cikin naniƙe masa ki ke, ko abun da ake faɗa ɗin gaske ne, kina kai masa kanki?"

Iman ta yi shiruu, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, amma ba ta da bakin magana, 'yar tsintuwa ce kamar yadda Samha ta faÉ—a.

Maganar samha ce ta dawo da ita hayyacinta, "Wallahi idan ki ka cigaba da shishshige wa Adam, sai na sa kin yi dana sanin zuwanki duniyar nan, sai na mai da ke matacciya da rai, sai na yi miki illar da ba kya zato, ki kiyayi adam ki daina yi masa shishshigi idan ba haka ba zan aikata abin da na faɗa, banza mai kyan banza 'yar tsintuwa, ke ban da abinki ma, har kina tunanin haɗa jiki da jinik sarauta ƙasƙantacciya irinki, da babu wanda yake da taabbcin 'yar halak ce ke, ƙila ma 'yar gaba da alfatiha ce"

Duk yadda Samha ta din ga yi wa iman baƙaƙen maganganu, ba ta tanka ba, tayi ta gama ta fita. Sai da ta fitan sannan iman ta bawa hawayen idonta damar zubowa.

Tana tsaka da kukan baba uwani ta shigo É—akin " 'yar auta ya jikin naki?".

Iman tayi maza ta rufe idonta kamar tana bacci.

Ta leƙa fuskar iman, ta ga idonta a rufe, cikin sanɗa ta koma gaban mudubin ɗakin iman, ta hau laluben mukullin drower mudubin iman.

A hankali iman ta buÉ—e ido tana kallon baba uwani, tare da tunanin binciken me take yi mata a É—aki haka.

Tari tayi tare da ƙoƙarin gyara kwanciyarta, ta buɗe idonta tana kallonta, nan da nan baba uwani ta diririce, ta fara kame-kame "Amm..amm...'yar auta dama idonki biyu ne? Dama na ce bari na zo na yi miki sannu, sannan na ɗan tattare miki ɗakin".

Iman ta ce "Bakomai baba uwani, ai gyaran É—akina ba aikin ki bane ba, ke da ki ke a kitchen, kuma ga hadimai, an gyara É—akin da safe karki damu".

"To..to...toooo shikenan, Allah dai ya baki lafiya iman, Allah ya yaye miki ya baki lafiya, bari na koma kitchen É—in" ita da iman ta bita da kallo, ba ta ga alamar gaskiya a tare da ita ba.

***
Cike da wata irin mummunar faÉ—uwar gaba, rumaisa ta farka daga baccin da ya É—an É—auketa, ta ga jaririn nan dai yana rungume a jikinta, idonsa biyu sai cin hannunsa yake, kai da gani babu tambaya ka san yunwa yake ji.

Tana É—aga ido ta hango barde a kan babur shi da wani, sule na ganinsa ya ce "Yauwwa dama kai muke jira".

Su ka yi parking ɗin baburin, barde ya sauka hannunsa riƙe da leda.

Ya ƙurawa rumaisa ido, ya nufi in da take, ya durƙusa a gabanta, ya saka hannu ya ɗaga zanin da jaririn ke ciki, ya kalli yaron. Bai yi magana ba ya ga ruma tana zubar da hawaye.

Bai ce mata komai ba, ya kwance mata ledar gabansa, koko ne da ƙosai a ciki, sai madarar peak guda biyar ya ce "Gashi nan, na ga da ki ka yi rashin lafiya kina ta amai, wataƙila har da ulcer, ga madara nan ga kuma abinci ki din ga kula da abinci, in anjima zan aiko yarona da abinci, ba a samo waina a in da ake sayo miki ba".

Maimakon ta yi masa godiya cikin kuka ta ce "Aisha ta mutu fa, jaririnta ne wannan".

"Na sani, ita tata ta ƙare, Allah ya karɓi shahadarta".

"Shikenan haka zan ta zama a nan wurin sai wahala ta kasheni? Ku baku kasheni ba, ku baku sakeni ba".

"Ke, ki mayar da hankali ki ci abinci na ce".

"Ba zan ci ba, ka kwashe tsiyarka" kallonta ya yi a fusace ya ce "Ni ki ke gayawa haka?"

"Eh ɗin" sai kuma ta ɗan yi shiru ta ce "ka yi haƙuri dan Allah, na gaji ne ban san a halin da mama da yayyena suke ciki ba, na gaji da zaman wurin nan, dan Allah a tunaninka abin da ku ke yi ɗin nan kun yi mana adalci, kalli fa jaririn nan, ya rasa mamanshi an haife shi a tsakiyar daji, ko kaya babu a jikinsa fa, ga yunwa yana ji, kalli wurin kwananmu, yau a kashe wannan, gobe a wulaƙanta wancan ya kuke so mu yi? Galibinmu fa duk talakawa ne, ba 'yan masu kuɗi ba".

"Kin san meyasa nake ta baki kariya kar a kashe ki?" Ta girgiza masa kai.

Ya ce "Gyaɗar da ki ka bani a kasuwa, ki ka ce idan ina da 'ya'ya in kai musu, na gaza samun tsaro a ƙasata, a kan idona na rasa iyayena, da 'ya'yana biyu da yunwa ce ta kashe ɗaya, saboda hare-haren 'yan ta'adda bana iya fita samo musu abun da zasu ci, aka sace ɗan uwana, sai da na sayar da komai nawa domin karɓo shi, aka kashe shi, shiyasa da aka yi mini tayin wannan harkar ban ji ko ɗar ba na karɓa na shiga, idan ya so duk ayi mutuwar kasko, kuma na samu ƙwarin gwiwa ne, tun bayan da na san iyayen gidanmu su ne tsaro a ƙasar nan..... Sule ne ya kaste barde ta hanyar cewa "Kai fa nake jira mu yi magana, ya za ayi ka karɓo mana jaririn nan mu kashe shi, mun riga mun yi wa mutanen smoke wannan alƙawarin, yarinyar nan ta ƙeƙashe ƙasa ta hana yaron nan, ina tsoron muyi mata illa, mu saɓa waccan yarjejeniya da ke tsakaninmu da ku".

Barde ya kalli rumaisa, sannan ya kalli sule ya ce "Kar ka damu, gobe zamu kawo muku mutanenku, ku bamu ita, mai gida da kansa zai zo wurin nan"

Sule ya yi murmushi ya ce "To madalla, ai hakanma yayi"

Suka cigaba da tattaunawa, ruma kuwa ta samu wata ledar pure water, ta zuba kokon nan a ciki, ta zazzaga madara, ta dinga bawa jaririn nan.

Haka nan yaron nan ya din ga shan kokon da ruma ke ɗura masa, ba ta san ya ƙoshi ba, sai da ya din ga kwarara amai ta hanci ta baki.

"Rumaisa ya zaki bawa jaririn kwana biyu koko, ai sai ki ja masa wani abun" cewar wata dattijuwar mata.

"To baba ko in baki shi ki shayar da shi ne? Idan ban bashi koko ba mai zan bashi, da ma aka samu kokon, tausayinsa nake ji, da mamansa na nan, da ya samu sauƙin wani abun, ka yi haƙuri ka ji yarona, Allah ya kula mini da kai, ya jiƙan anty aisha" tayi maganar tana zubar da hawaye tana goge masa aman da yayi da zanin da yake ciki.

Bayan tafiyar barde, sule ya cewa ruma "Sai ki gode Allah, gobe zasu bamu mutanenmu dan su karɓeki, mu kuma a goben zamu kashe ki, ba zamu basu ke ba".

Duk da tsiwar da ruma take yi musu, a kan su kasheta, sai da gabanta ya faÉ—i jin ya ce gobe zasu kashe ta, to yaya jaririn nan zai kasance kenan? A zahiri kuwa ko gezau ba ta yi ba, sai cigaba da gogewa jaririnta amai da ta cigaba da yi.
Azabar galabaita ta sanya yaron ko kukan kirki ya daina yi, sai dai yai kaɗan yayi shiru, ga wani irin numfashi da yake yi, iya ƙirjinsa kai da gani ka san ba shi da cikakkiyar lafiya.

Yau tun da garin Allah ya waye, bayan rumaisa ta yi sallar asuba, ta zubawa wurin da suke zama ita da aisha ido,, sai wasi-wasi take yi, tayaya jaririn nan zai rayu? Ance kasheta za ayi, waye zai kula da ɗan ta san dai ƙarshenta shi ma kashe shi za su yi, ga wata irin soyayyar yaron da ke ratsa zuciyar rumaisa.
Chapter 77 · 0% Book details