← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 174

Sashe 124

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*Littafin kuɗi ne, ₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

Cikin tsananin farinciki ammi ta ce "Da gaske rumaisa kin amince?"

Ruma ta jinjina kai, ammi ta ce "Alhamdilillah, Alhamdilillah Ubangiji Allah ya yi muku albarka, Allah ya sanya muku albarka, in sha Allah tarayyar nan za ta zame muku alkhairi, Allah ya albarkaci rayuwarku".

Mama ta amsa da amin.

Mai sunan baba kuwa, yana so ya shigo iman tana tsaye a hanyar da zai wuce, sai waya take cike da iyayi da shagwaɓa, ya ɗan jira ta gama ya wuce, amma ba ta da niyyar gamawa dan ba ta ma san ya zo wurin ba.
Ga ƙamshin turaren da take yi duk ya cika masa hanci, yana neman ya sanya shi atishawa.

A ƙarshe dai ya ƙule cikin dakakkiyar muryarsa ya ce "Ke! Bani hanya zan wuce!"

A razane ta saki wayar ta ja da baya, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Cikin hanzari ta durƙusa ta ɗau wayarta da screen ɗin ya tsatstsage.

Ammi tana ta zuba addu'a, amma jikin rumaisa ya yi sanyi, sai dai duk da jikinta ya yi sanyi, bai hana ta yin dariya ba.
Ammi ta ce "Rumaisa, ya na ga kina dariya kuma, meya baki dariya ne?".

Rumaisa ta ce "Mai sunan baba ne ya tsorata miki Æ´a da wannan muryar ta sa"

Tana rufe baki sai ga iman ta shigo jikinta yana tsuma ta ce "Ammi wayata ta fashe".

Ruma ta ƙunshe baki tana dariya ta ce "Sorry, haka yake, ya daɗe yana jiran ki gama waya ya wuce, baki matsa ba, shi ne yayi miki tsawa".

Ammi ta ce "Subhanallah, maman rumaisa haka baban nan naki yake, daga baƙunta sai faɗa, bai san autar tawa matsoraciya ce ba, ai shikenan bari mu fita sai a sai wata wayar".

Mama ta ce "Hmm mai sunan baba ai sai dai Allah ya shirya, ƴaƴa ne gasu nan kowa da halinsa, ki yi haƙuri kin ji iman, ban ji daɗi ba wallahi"

Adam ya ce "Ammi lokaci fa, ina son yau zan kwana a gida, zan yi wani aiki".

Ammi ta ce "Haka ne, dare ya fara yi, rumaisa, ba zan fasa godiya ba, ubangiji Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sanya muku albarka, sauran magana duk yadda ake ciki zan yi magana in Allah ya yarda.

Suka fito tsakar gida, takawa ya kalli rumaisa wani takaici ya ƙule shi, wannan fitsararriyar abar ce zai aura.

Yaya Abubakar ne ya shigo, ammi ta kalleshi ta ce "Malam faruku kai ne ka razana mini Æ´a ko? Kuma ka ce baka son in haÉ—a auren Æ´aÆ´ana haba mai sunan baba laifin me muka yi haka ne"
Abubakar ya yi murmushi ya ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau ya gida ya ƙoƙari?"

"Alhamdilillah"
Iman ta ɗan ƙura masa ido, kamar ba wannan ne mai muryar nan ba.

Mama ta ce "ÆŠan uwan mai sunan baba ne, shi gashi can a bayanki yana jinki, wannan dattijon arziki kenan malam habu"

Ammi ta ce "Au, ashe fa Æ´an biyu ne ai ni duk kama suke yi mini" ta waiwaya ta kalli mai sunan baba ta ce "Mun zo neman aure gidanku ka hana, a sassauta adawar nan ba a san in da rana za ta faÉ—i ba, ina da tarin Æ´an mata a gidana kar ka zo neman aure nima na rama".

Suka yi dariya gaba É—aya, mai sunan baba ya É—an sunkuyar da kai be ce komai ba.

Ammi ta ɗora da "Dan Allah ayi mana addu'a, na samu duk sun amince in sha Allah lamarin nan alkhairi zai zama, tun da Allah a ka nufa da lamarin, ba za aji kunya ba, karatun rumaisa da komai zamu kula da shi, kuma adam zai riƙeta cikin mutunci da kulawa, mu sanya a ranmu wannan haɗin Allah ne, a tayamu da Addu'a".

Mai sunan baba ya ce "Allah ya tabattar da alkhairi "

Ammi ta ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, yauwwa mai sunan baba ko kai fa, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku, ya baku mataye nagari sanyin idaniya, ya tsare mana ku daga sharrin zamani". Ya amsa da amin.

Abubakar ya ce "Hajiya babu wata damuwa, har kullum alkhairi muke fata, kuma dama babban burinmu bai wuce rumaisa ta yi ilimi, sannan ta samu abokin rayuwa nagari ba, Allah ya sanya haÉ—in nan ya zama alkhairi".

"Amin ya Allah, na ji daÉ—i sosai na gode da karamcinku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya yayi muku jagora".

Adam har ya fara ƙulewa, gaba ɗaya ya gaji so yake su tafi, har ya je ya kunna mota, amma ammi tana ciki tana ta faman hira.

Iman tuni ta bi bayan Adam ta shige cikin motar, sai sauke numfashi take, saboda ba ƙaramin razanata mai sunan baba yake yi ba.

Aka yi sa'a mama ta yi musu sallama ta fito, maƙwabtan su rumaisa har sun fara surutun, yawan zuwan da mota daban-daban take yi ƙofar gidan su rumaisan.

Suna tafe a hanya ammi tana faÉ—in "Alhamdilillah, na ji daÉ—i an gama da wannan babin, gobe in Allah ya yarda zan je na samu turaki, sai dai dole mu yi shiru da bakinmu, babu wanda zai ji wa za ka aura, sai Allah ya kaimu lokacin".

Adam a ransa ya ce "Sai ka ce wata matar arziki, ni dan ta ni ba wanda zai san ma an yi auren, wannan har wani aure ne"

Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana saƙe-saƙensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ƙarasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.

Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a ɗakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ƙalubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ƙarata".

A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faÉ—uwa.

"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ƙaddarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wataƙila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wataƙila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"

Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.

***
Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.

Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na É—an bashi lokaci tukuna"

"Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"

"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"

Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"

"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ƙaddara sai ya fara aurenta ne"

"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman É—in, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".

"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"

"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"

Ta ƙaƙalo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".

"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"

"To Allah ya sauwwaƙe"

Ya amsa da amin ya fita.

***
Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba ɗaya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ƙyar take ci.

Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"

Ruma ta É—ago ta kalli mama.

"Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana"

Rumaisa duk ƙaunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ƙoshi tafiya zan yi"

Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ƙarasa ta zauna a gaban mama.

"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.

"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da Æ´an unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"

Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"

Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".

"Dan Allah mama ki gaya mini"

"Ba zan faÉ—a ba tashi ki tafi, karki makara"

Ganin mama ba ta da niyyar faɗa mata, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice, ta ƙudurce a ranta sai ta san ko menene.

Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ƙwala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ƙaraso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"

Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"

"Amma meyasa, kin haƙura da karɓar ɗan?"
Chapter 124 · 0% Book details