← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 174

Sashe 135

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalifa ya ce "Haka ne Daddy, na yi duk iya yi na, ka sani na zaci yadda maganganun nan suka yamutsa hazo za su gigita shi, amma ya mayar da mutane mahaukata wato mu je ma mu yi ta yi kenan"

Senator ya yi murmushi ya ce "Na jinjinawa ƙoƙarin ka Khalifa, ban taɓa zaton zaka iya wannan ƙoƙarin ba ma, ka bani mamaki sosai kuma na yabawa ƙoƙarin ka, labarin da yake zuwar mini, hankalin yaron nan ba ya kanmu yanzu, kuma waɗanda suke jagorantar aikin tare da su, na saye wasu daga cikinsu, sannan kuma dama shi yake jagorantar aikin, kuma hamkalinsa ba ya kan aikin yanzu, na yi magana da shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa, mun gama magana ba wani abu zasu wanke ni"

"Amma daddy kana ganin hakan ya wadatar, kar fa ya kuma ɓallo mana ruwa".

"Ai ba haka zan bar shi ba, ba ka da wata damuwa, na san abun da nake yi"

Khalifa yayi murmushi ya ce "To shikenan daddy"

***
Adam yana zaune yana aikinsa a office É—in sa, ya É—au wayarsa ya kira Bashir.
Suka gaisa Adam ya ce "Ka je ka maƙale ka ƙi dawowa, akwai update ne?"

Bashir ya ce "Babu wani update, sai dai na haɗu da barrister Sa'ad, ya ce akwai yiwuwar kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa a kan senator Usman wakili ba zai yi wani tasiri ba"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na sani, dama ban ji a raina za su yi wani abun kirki ba, amma babu damuwa, zuwa next week ko upper in sha Allah zan shiga Abuja, ina son zuwa EFCC".

Bashir ya ce "Meyasa ba zaka shigo next week ba?"

"Wallahi ammi ce ta sakoni a gaba da wani batu, yanzu da na ce zan yi tafiyar nan, za ta ce ban É—au abun da muhimmanci ba"

"Eh kuma haka ne, to shikenan Allah ya kaimu upper week É—in, ni ranar sunda in sha Allah zan shigo kano, dama da zaka zo next week É—in ne sai na jiraka, duk yadda ake ciki dai za mu yi waya"

"To shikenan Bashir, Allah ya yi mana jagora "

"Amin ya rabb, a tashi lafiya".

Ya ajiye wayar kenan, Jabir yayi sallama a office É—in Adam, Adam ya kalleshi ya ce "Me ka ke yi a nan lokacin aiki?"

Jabir ya harare shi ya ce "Ban sani ba, sai avoiding É—ina kake, ba na samunka a gida, gidanka ma baka nan, na ce bari na zo na ritsaka a nan"

"Amma dai ka san lokacin aiki ne yanzu ko?"

Jabir ya ce "Ai lokacin salla ne kawai ba zan datseka ba, kuma sai ka saurareni, ai ka san abun da ka yi ba ka kyauta ba, dole ka yi ta gudun haÉ—uwarmu"

Adam yayi masa shiru, ya cigaba da aikinsa.

"Adam, ka san yanzu kaf idon duniya a kan kan ka yake, amma na lura kai ba ka damuwa da hakan, baka gudun janyo wa kan ka magana, yanzu dan Allah da wani mummunan abu ya faru da Mahmud saboda zuciyarka me zaka ce? Yakamata ka sassauta wa zuciyarka wannan ƙiyayyar da ka ke yi masa, ko kana so ko ba ka so ɗan uwanka ne shi"

Adam ya yi masa shiru, wanda wannan shirun shine halayarsa da ta fi ɓatawa makusantansa rai.

"Ko ka kulani, ko kar ka kulani, na san dai kai ba kurma bane ba, kuma ka na jina, jibi in Allah ya kaimu zan je duba galadima" sai a yanzu Adam ya É—ago ya kalli Jabir ya ce "Ubangiji Allah ya tsare hanya, ka ce ina gaishe shi" Jabir ya girgiza kai ya tashi ya fice, dan halin Adam sai shi wasu lokutan.

***
Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba.
Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya ɗauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata alƙawarin yin hakan, a duk lokacin da ta buƙata.
Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faɗi, saboda tana matuƙar fargabar haɗuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba ɗayansa tsoro yake bata.

Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini.

Da la'asar suka shirya, aka shirya Sabir suka fito domin tafiya gidansu rumaisa, Adam na gaba iman na bin sa a baya da Sabir. kasancewar Mahmud ƙafarsa ta fara sauƙi, ya fara yawonsa a cikin gidan, hango Iman yayi da yaron a hannunta, wanda ko ba a gaya masa ba ya san shi ne jaririn, haka nan ya ji ya kwaɗaitu da son ganin fuskar yaron, tun da a yanzu, kansa kawai ya hango, mai ɗauke da tulin suma baƙa wuluk.

Suna tafe a hanya Iman na yi wa sabir wasa, yana ta miƙa hannu yana son kamo sitiyarin motar.

"Iman" Adam ya kira sunanta.

"Na'am yaya".

"Abubuwa sun fara yi mini zafi, na san magana zata fara yawo a kan auren nan nawa, dan Jamil ya zo ya tutsiyeni na gaya masa idan maganar gaske ne, kuma na tabattar masa da gaske ne, abun da nake so da ke, dan Allah ku yi shiru da bakinku, kar wanda ya san wa zan aura, idan an yi auren sa ganta"

"Yaya kunya ka ke ji ace rumaisa ce matarka?"

"Ke rabu da ni kawai, banda rigimar ammi, ina ni ina wannan Yarinyar da a rayuwarta babu wanda ta raina kamar ni, kuma bana son a cutar da ita, Samha haryanzu tana son aurena, a wannan karon ma ba zai yiwu ba, shiyasa bana son kowa ya san wacece".

"In sha Allah yaya ba zan faÉ—awa kowa ba, ammi ma ta gargaÉ—emu a kan hakan"

Ya ce "Good, ku shiga ki kai mata shi, ni zan je gidan gona, wancan karon ban samu na je ba, saboda wani dalili " yayi maganar lokacin da ya yi parking.

Ta ce "To shikenan, sai ka dawo" ta sauka ta É—auki kayan rumaisa da ammi ta sake bayarwa a bata, ta shiga gidansu rumaisa da sallama.

Sai dai gidan shiru, babu alamar aksai mutane a gidan.

Iman ta yi sallama, sai dai muryar da ta amsa mata sallamar ce ta razanata. Kasa shiga ta yi, ta kuma kasa komawa baya.

Shi kuma bai kuma tankawa ba, sallama ta kuma yi, ya ce "An amsa a shigo mana" daga É—akin mama take jiyo muryarsa, kamar mai shirin arangama da horo, ta shiga É—akin.

Mai sunan baba ne a zaune yana cin abinci, mama kuma tana salla.

Cikin ɗar-ɗar, ta shiga ta zauna hannunta rungume da Sabir, kanta a ƙasa ta ce masa "Ina wuni?"

Bai kalleta ba ya ce "Lafiya lau" Sabir ya ƙurawa mai sunan baba ido, "Miƙo mini shi" yayi mata maganar cikin umarni.

Kai a ƙasa ta miƙa masa Sabir, ya rungume shi yana cewa "My boy, ka ƙara girma Masha Allah" bai yi masa ƙyuya ba, ya cigaba da cin abincin sa, iman ƙoƙarin satar kallon mai sunan baba take tana tsoro, shi kuma da ya lura da hakan, sai ya tsareta da idonsa tana ɗaga ido suka yi ido huɗu, aikuwa ta razana ta sunkuyar da kanta.

'Yarinyar nan tana da hankali kuwa?' mai sunan baba ya tambayi kansa.

Mama ta idar da salla da addu'a, ta juyo tana yi wa iman sannj da zuwa.

Iman ta gaisheta mama ta amsa mata cikin sakin fuska, Iman ta ce "Ammi ce ta ce a kawo wa Anty rumaisa Sabir"

Mama ta ce "Allah sarki, yanzu za ta shigo daga islamiyya, ya babansa?"

"Yana lafiya shi ya kawomu, zai dawo ya É—aukemu ma"

Mama ta kalli Sabir ta ce "Mutumin, zo mu gaisa mana" ya sake kwanciya a jikin mai sunan baba, yana cin hannunsa.

"Allah ka aika munafukinmu ƙarshen nesa, mamarmamar, igiyar ƙasa ko da lafiya ko babu mamarmamar" Rumaisa ta shigo tana waƙe-waƙenta, da ƴan ciye-ciye.

Tana shiga falon mama sabir ta fara gani, ta buga tsalle zata É—auke shi, mai sunan baba ya ce "Fita ki yi sallama" sumi-sumi, ta koma ta yi sallama, sannan ta É—au sabir tana murna.

Ta kalli Iman ta ce "Anty iman sannu da zuwa, ya ammi?"

"Tana lafiya tana gaishe ki"

Babban abun da ya bawa mama mamaki, bai wuce yadda Sabir ya saki fuskarsa ba da ya ga rumaisa.

Rumaisa ta shimfiÉ—a tabarma a tsakar gida ta ce "Anty Iman, dawo daga nan mu yi hirarmu, ya fi iska"

Haka yayi wa iman daÉ—i, dan mai sunan baba ya takurata.

Rumaisa ta cire wandon uniform ɗin ta, daga  ita sai rigar uniform, ba hijjabi ba ɗankwali, sai murna take yi.

"Anty Iman, bari na zubo mana abinci"

Iman ta ce "Wallahi a ƙoshe nake"

"Ba kya cin abincin gidan talakawa dai"

Da sauri Iman ta ce "A'a wallahi"

Rumaisa ta ce "To kawai zan zubo ki ci".

Rumaia ta zubo wa Iman jallof rice, mai kyau har da nama, ta kawo mata ruwa, ita kuma ta É—auko tukunyar da aka yi girkin da cokali da yaji ta zo ta zauna.

"Anty rumaisa me zaki yi da tukunya kuma?"

"Ƙanzon shinkafa zan ci ya fi daɗi"

Iman ta zuba mata ido tana dariya, rumaisa ta din ga kankarar ƙanzo ta na ci, Sabir ya din ga zura hannu yana nema ya ci shi ma.

Iman ta na cin abincin tana yi wa rumaisa santin abinci yayi daÉ—i.

"Garadan mama ne suka girka, kuma ba wani daÉ—i yayi ba kar su ji ki ziga su" hira suke yi sosai da iman.

Suna tsaka da hirar suka ji sallamar Adam a ƙofar shigowa gidan, suka amsa masa, mama ta ce ace ya shigo, mai sunan baba ya tashi ya baro ɗakin mama, dan ya san nan zai shiga.
Chapter 135 · 0% Book details