← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 174

Sashe 11

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daɗe, gashi an gama ƙarin Alqur'ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda" cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
Ruma ta kalleta ta ce "Ina aka biya É—in?".
Yarinyar ta buɗe Alqur'anin tana nunawa Ruma ta ce "Rabin shafi aka ƙara, gobe in Allah ya kaimu ma za a ƙara rabi, feji ɗaya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar".

Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

"Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buÉ—e sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi".

Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara ƙular da ita ta ce "To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji ɗaya bane ba, kuma sai a ƙara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaɗona da mai da yaji a cinye" galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

Bayan an kaɗa ƙararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za'a fara karɓar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haɗawa da wanda ake yi musu a aji.
Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
ÆŠa da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daÉ—i, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta É—aga kai taga Ruman a tsakar gida.

"Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?"

Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta ƙoshi, Sannan ta dubi mama ta ce "Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba".

"To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa".

"Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji É—aya ni za a kai aji É—aya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba"

Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

"Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta".

Ruma ta ce "Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi ƙuli-ƙulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai ƙari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taɓ ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

Yasir ya ce "Ai makarantar mu ba ta daƙiƙai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba".

Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana É—aki a kwance suke ta wannan zubar.

Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi zaƙewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

"To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki"

Ruma a ranta ta ce "Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki"

Ya kalli su Yasir ya ce "Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan daƙiƙiya ce, duk daɗewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, daƙiƙiya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki"

Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala'insa ya bar gidan.

Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ƙara musu ɗin ba, ta cigaba da sabgoginta.

Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haɗasu da alaƙaƙai.

Yau mama ta bata kuɗin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ƙofar shiga makarantar.
Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane É—alibi ya nutsu sun haÉ—a baki suna ta tilawa.

Taɓe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiɗa tana cin goribar ta a nutse.
Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
Ba ƙaramin ƙulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ƙaramar gaɓuwa ce ba yarinyar.

Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce "gani"

Ya ce "Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, ɗauko Alqur'anin ki ki karanta ƙarin da na yi muku, sannan ki bani hadda" ɗan waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce "Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya ɗaya ko biyu"

"Koma gefe ki tsaya" babu ban haƙuri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

Ya cigaba da sauraron tilawar 'yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya ɗaga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya ƙule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce "Ke zo nan"

Ta ƙaraso ta tsaya, miƙewa yayi ya ɗaga bulala zai daketa.
Ta ƙwalalo ido ta ce "Kar ka dakeni ba a dukana" bai saurari ruma ba, ya zuba mata a ƙafarta har sau biyu.

Wani uban ihu ta ƙwala, ta zube a kan ƙafarta tana jujjuya kai.
Gaba É—aya 'yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

"Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba" gaban malamin ne ya faÉ—i, amma ya maze ya cewa 'yan ajin su cigaba da karatu.
A ƙalla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ƙaƙƙautawa kuma taƙi tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, É—an ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
Malamai suka taru a kan ruma, amma taƙi tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa "Wallahi bai san ba ta da lafiya ba"

Malamin da yayi mata interview ya ce "Kuma ni a form É—inta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?"

"Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu"

"Su waye yayyen naki?" Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaɓi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
Ya miƙa mata hannu ya ce "Taso in mayar da ke gida"

"Ni na kasa motss ƙafata ciwo take mini" tayi maganar cikin kuka.

Huzaifa ya durƙusa ya ce "To hau bayana na mayar da ke" aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya ɗau jakarta ya ce bari ya kai ta gida.

Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ƙafafuwanta.

Ya kalleta ya ce "A gidan uban wa ki ke da sikila?"

"To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar".

Galala ya bi ruma da kallo, 'yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

"To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata"

Marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi haƙuri"

"Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau" yana gama maganar ya danƙeta ya saɓata a kafaɗarsa dan zata iya ƙwacewa ta gudu.

Ayshercool
08081012243
[22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following É—ina a arewabooks a kan account É—ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

*AFUWAN BAN EDITING BA*

P6
Chapter 11 · 0% Book details