Sashe 153
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta É—au ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin Æ´an mata.
'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta.
Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ƙawar amarya an sha ɗauri, ƴar baƙa kyakykyawa.
Iman ta ƙarasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku ɗaya, koda yake na san yaya Aliyu"
Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske, Æ´ar balarabiya ya aka yi ne?".
Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa".
Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri ɗaya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ƙamwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi haƙuri da ita, idan aka taɓata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza "
Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taɓa haɗata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.
Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.
Jabir ya ƙaraso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ƙarasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane".
"Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan ɗazu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaɓa.
"Yes na ji, zo mu je dai, ko na É—agaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a É—aura auren da namu"
Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.
Suna yin gaba ya hau ta da faÉ—an, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta É—aga kai suka yi ido huÉ—u, da sauri ta koma cikin wurin dinner.
Kwaɓe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".
"Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta ƙarasa maganar bilhaƙƙi za ta yi kuka.
"Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?"
Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ƙi fasawa, wayyo mama ni na gaji"
A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faÉ—a.
Mc kuwa koɗasu kawai yake yi, saboda shagwaɓa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga yaƙe, dan kar a fahimci wani abu.
Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.
Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?"
"Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare"
"Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.
Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya É—ebi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.
Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.
An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta É—aga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.
Hatta ammi ta je wurin, an yi mata liƙi sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi liƙi.
Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata liƙi, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu.
Adam ma basarwa yayi, ya din ga yi mata liƙi, kuɗi ba kaɗan ba, ta din ga kallonsa ta ga ko yana sane, amma yaƙi kallonta kar ta yi wani shirmen. Babban abun da ya fi burgeta, shi ne fareti, da kuma crossing sword ɗin da abokan aikin su Adam suka yi musu.
Gajiya kam rumaisa ta yi ta, dan har gyangyaɗi ta fara, da ƙyar take iya buɗe idonta, ga takalmi mai tsinin gaske a ƙafarta.
Sai sha É—aya da rabi na dare aka tashi, rumaisa tana ta sauri ta bi su yaya Abubakar, amma takawa ya sakata a gaba zuwa motar da suka zo.
Tana shiga ta zauna ce "Wayyo Allahana, na gaji"
Ya kalleta yayi shiru, basu je ko ina ba ta hau bacci, gaba É—aya ta kife masa a jiki, kai da jin yadda take sauke numfashi ka san ta gaji da yawa.
Sidi ya ce "Sir amarya ta gaji da yawa"
Adam ya ce "Gashi har ta yi bacci"
Sidi ya ce "Allah mai iko, ba zan manta scene É—in da ku ka yi making, ranar da ku ka fara haÉ—uwa ba, and she's now your wife"
Adam ya ce "Shhhhh, a daina tayar da wannan maganar"
"Sorry sir"
Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya ɗaukar pose ɗin ta, ya buɗe, ga sababbin kuɗi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya riƙeta a hannun sa.
Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya.
A ƙofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ƙaraso, ya sauke glass ɗin motar, gaba ɗaya suka ƙaraso.
"Ta yi bacci fa" ya faÉ—a yana kallon Usman.
Usman ya ce "Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar Æ´ar kaza".
Adam ya É—agata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi.
Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ƙanwarsa a kwance a jikin wani ƙato. Takawa ya ɗaga kai suka haɗa ido da shi, ya wani cukule fuska.
Aliyu ya zura hannunsa, ya ɗauko rumaisa gaba ɗaya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce "Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karɓa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai"
Aliyu ya ce "Tuba nake, zan kula sosai"
Juyawa mai sunan baba ya yi, ya shiga gida, ƙasan zuciyarsa istigfari, da tunanin meye nasa na jin haushi kuma, bayan komai daɗewa dole wataran ta zama matar wani.
Aliyu ya shimfiÉ—e rumaisa a katifar mama, Gwaggo cewa take "Wannan an yi shashasha amarya, haka take da wannan nauyin bacci haka, ta bar mutane da dakonta".
Mama ta ce a tasheta ta yi sallar isha'i, lawisa ta ce sun yi salla a gidan kwalliya, kafin su tafi.
Tana magagin, mama ta dafa ruwa, ta kaita banɗaki ta wanke mata fuska, ta yi mata wanka tas, ta lulluɓota ta kawota ɗaki, ƴan biki na ta yi mata dariya, sai dai har a cikin ranta ji take ruman ba ta wuce wankan ba, ƙaddarar aure zata rabata da ƴar da take matuƙar ƙauna.
Ɗakin samarin nan kuwa, kusan kwana suka yi babu bacci, suna ta ɗan tattaunawa, a kan biki, da kuma jajanta rabuwa da tilon ƙanwarsu, kuma kallabi a cikin rawunansu.
Mai sunan baba kuwa ya naÉ—e, ya lumshe idanunsa ya yi shiru, ba abun da yake ganowa sai kai wa da komowar iman a wurin nan, da yadda suke yawan haÉ—a ido. Tsaki ya ja ya nemi wuri ya kwanta, sai dai tunanin gobe dai-dai lokacin, rumaisa na gidan wani, ya hana shi bacci, ya din ga yi mata addu'ar shiga gidan miji a sa'a.
Bayan idar da sallar juma'a, aka É—aura auren rumaisa da adam, Æ´an unguwar da basu san waye mijin ba a ranar suka ji.
Unguwar ta cika da dawakai, da manyan motoci na alfarma, duk in da ka kalla, jami'an tsaro da kuma masu rawuna ne.
Sai dai tun da aka É—aura auren nan, rumaisa jikinta yayi sanyi, take ta uban kuka, duk yadda aka so rarrashinta abun ya gagara.
Tuni hotunan biki suka zaga duniya, kowa da abun da yake tofawa, na alkhairi da akasin haka.
Samha kuwa kaiwa take ta yi tana komowa a ɗakinta, tana fatan aikin da ta bayar ayi mata, ya yiwu ba tare da samun wata matsala ko akasi ba, dan ta riga ta ƙudirce wa kan ta ɗaukar fansa, ko da tsiya ko da arziki.