← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 174

Sashe 142

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da asubar fari, rumaisa ta tashi ta fito, zata shiga banÉ—aki ta tarar da mutum a ciki, ta zuba ruwa a buta, ta zauna a gefe tana hamma.
Gajiya ta yi da zama, ta ce "Wai dan Allah waye a banÉ—akin nan, zan yi a tsakar gida fa".
Shiru aka yi ba a bata amsa ba, waÉ—anda suka yi alwala suka fara tafiya masallaci.
Usman ne ya buɗe ƙofar ya fito, yana hararta.

"Yaya usy wai dama kai ne a ciki? Wai dan Allah kai kullum sai ka yi wanka da asuba? Wankan me ka ke yi, ka yi da asuba, ka yi da safe zaka tafi makaranta, idan ka dawo da yamma ko da daddare sai ka yi, wanka da asuba ko sanyi baka...."

BuÉ—e baki yayi ya ce "Zan ci ubanki, saka mini ido ki ke yi ina ruwanki da ni".

Aliyu ne ya fito yana dariya, ya ce "Malam ka yi mata bayanin wankan uwar me kake yi da asuba?"

Tsuke fuska Usman ya yi ya ce "Ba na so"

"Meye ba ka so, tun da ba zai gaya miki ba, in anjima idan ya zo É—akin mama ki tambayeta, wankan me yake yi da asuba?"

"Ai ba sai ta tambaya ba, ita da zata yi aure kwanan nan, za ta yi ita ma".

"Aliyu ya ce "Kai fa ba ka da hankali".

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan wanka da asuba ba, sau É—aya zan din ga yi a rana, lokacin sanyi ma wataran ba zan yi ba"

Usman "ke dalla tashi ki bar wurin nan, munafuka cctv Camera, wuce ki je ki yi abun da zaki yi ko na karya miki wuya" tashi ta yi ta ja butar ta sum-sum ta tafi banÉ—aki.

Yau asabar ce, dan haka bayan sallar asuba, mai sunan baba ya dawo ya kwanta barci, sai dai wajen ƙarfe takwas na safe, wayarsa ta ishe shi da vibration a ƙasan pillow.

Cikin bacci ya É—au wayar, ya saka a kunne yana lumshe ido.

"Anty rumaisa, barka da safiya jiya ki ka yi bacci na kira kin yi barci".

"Ke! Ba wayarta bace kar ki sake kirana wayata ce ba tata ba" a wannan karon ma ba ƙaramar razana ta yi ba, cikin rawar murya ta ce "Yi haƙuri, na zata wayar mama ce".

"To ta umar ce, ki ka sake kirana ni da ke ne, an hana mutane barci tun jiya, ki yi ta wani yenyen, ba zaki buɗe baki ki yi magana ba" ya ƙarasa mitar yana kashe wayar.

Nusaiba da take gefenta ta ce "Wannan wane bala'e'en ne haka?" Iman ta girgiza kai ta ce "Ba kowa, ga Sabir nan bari na je na kwanta"
Nusaiba ta karɓi Sabir, ita kuma ta tashi ta tafi ɗakinta tana tunanin yadda mai sunan baba ya faɗa haka take magana.

Sunansa da ya faÉ—a umar ta sake maimaitawa, dole yayi masifa, ta faÉ—a a ranta.

Tana shiga ɗakinta ta ji tamkar an shaƙeta, kuma ta kasa gaba ta kasa baya, hannu ta saka tana riƙe wuyan nata, amma ta ji numfashinta yana neman ɗaukewa. Cikin fita hayyaci ta sulale Jikinta ta faɗi ƙasa.

Can katsina kuwa, Gwaggo har da taka rawa saboda murna, tana faÉ—in Allah ya dubi Æ´ar marainiyarta, za ta yi a gidan daraja, gidan sarauta gidan masu abun hannu.
Nan da nan ta ce ba zama, azo a kama wasu daga cikin dabbobinta a sayar, ta fara saye-sayen kayan da za a kai wa rumaisa.

Iman kuwa ba a tashi sanin halin da take ciki ba, sai bayan wasu awanni, da nusaiba ta ji ta shiru, ta shiga ɗakin ta tarar da ita a ƙasa a sume.

A kiÉ—ime ta je ta sanar da ammi halin da ake ciki, ranga-ranga aka É—auki Iman zuwa asibiti, ba tare da ta san waye a kanta ba ma.

***
Gidansu ruma kuwa, mama ma ta fara shirin tafiya kasuwa, domin fara saye-sayen da za a buƙata, dan ba ta taɓa kawo wa rumaisa aure yanzu ba, amma cikin ikon Allah, sai gashi ba tare da wani shiri ba, dan ko ƴan kwanuka ba ta fara saya ba.

Rumaisa na uwar ɗakan mama, tana ta zane-zanenta, mama sai mita take ba ta son zane-zanen nan, wataƙila ma zanen ne yake sanyata firgita cikin dare.
Rumaisa ta yi dariya ta ce "Haba mama, zanen ne zai tsortani, kin ganni nan kin san bana tsoron kowa sai Allah, balle wani zane".

"Kya ji da shi dai" ta yi maganar tana fita falo.

Yaya Abubakar ya yi sallama a falon mama, mama ta amsa masa ta ce "Garbatina ya aka yi ne?"

"Fita zaki yi ne?"

Mama ta ce "Eh, kasuwa zan shiga na fara saye-saye".

"To da magana nake son mu yi, amma idan kin dawo ma yi"

"A'a, zauna ka gaya mini sai na fita"

Suka zauna, Abubakar ya kalli mama ya ce "Mama, kamar yadda muka yi da ke, na je na ɗan zazzaga unguwar ina tambayar ya yanayin gidansu yake, da kuma shi kansa mu'amalarsa da mutane, to sai dai sakamakon baki ya rabu biyu. Wasu suk ce mutumin kirki ne, mai yawan kyauta, da girmama mutane kuma miskili ne, wasu kuma sun ce ba shi da kirki, yana da faɗa da zafin rai wai kwanan nan ya taka ƙaninsa da mota, ba wannan ne ya fi ɗaga mini hankali ba, wai ana kyautata zaton maye ne, kuma yana da taɓin hankali!!!

Ayshercool
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Dafe ƙirji mama ta yi tana salati, ta ce "Ɗan nan, da gaske kake wannan maganar?"

Abubakar ya ce "Wallahi da gaske nake, kuma ba a bakin mutum É—aya ba, ni da wani abokina Abdurrahman muka je, abun da na jiyo kenan".

Mama ta ce "Ya salam! Yanzu menene abun yi?"

"Ba wata maita a musulunci, haka malaminmu ya gaya mana, to so suke a fasa shikenan a fasa bani Sabir ɗin, ko kuma kuɗin da aka kawo ɗin suke so a mayar, ƴan baƙin ciki ne kawai".

Mama ta kalleta ta ce "Ke! Waye ya saka da ke? Da ke ake ke zaki yanke wa kanki hukunci?"

"Mama ba haka bane ba, to kuÉ—in za a mayar, idan aka mayar kuma an fasa ba za a bani Sabir ba fa kenan"

Aliyu ya shigo yana tambayar meyafaru?.

Mama ta gaya masa abun da ya faru, Aliyu ya kalli ruma da ta kumbura baki ya ce "Ke ki na son sa a haka?"

"Ba fa maye bane ba, ƙarya suke yi. Ni fa bana son shi, amma idan aka fasa ba fa zasu bani Sabir ɗin ba, kuma mama ba kwanan nan aka ce shi ya kashe Anty Aisha ba, kuma ƙarya ake yi masa ba? To wannan ma ina ga ƙarya ake yi masa, ni dai ko za a fasa, kar a mayar da kuɗin nan, kuma a bani Sabir".
Chapter 142 · 0% Book details