← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 174

Sashe 39

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin sheshsheƙar ruman a cikin net ɗinta.

Mama ta kuma haskta da fitila ta ce "Ke dan ubanki fito daga cikin net É—in nan, ki zo ki gaya mini abin da aka yi miki?"

Ruma tayi saurin goge fuskarta tayi kamar bacci take yi.

A hasale mama ta ce "Ba zaki fito ba sai na zo?" Ruma ta janyo jikinta ta fito, ta zo gaban mama ta zauna, amma ta kasa magana.

"Gaya mini menene kuma? Ko wani ne yayi miki wani abun?"

Ruma ta girgiza kai, "to kukan me ki ke yi wa mutane, ki gaya mini ko na leƙa na kira miki dodon naki"

"Kiyi haƙuri, zan gaya miki amma kar ki ce na gaya miki"

Mama ta ce "Ina jinki" nan ruma ta kwashe komai ta gaya wa mama, sannan ta ɗora da cewa "Mama Allah ya bamu kuɗi, ya horewa su Yaya ya sa kar su daina zuwa makaranta, kuma ni ba sai an canza mini makaranta ba, Allah ya bamu kuɗi su daina shan wahala, yayana ya kwana biyu bai ci abinci ba mama, wai an kore shi daga kamfani bai gaya miki ba" ta ƙarasa maganar tana kuka.

Jikin mama yayi sanyi ainun, duk wauta sa rashin tunani irin na ruma ashe ta na da hankali wasu lokutan, biri ya yi kama da mutum, Abubakar ya rame amam yaƙi gaya mata meke faruwa.

Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ruma, kin ga wannan yana ɗaya daga dalilan da yasa nake miki faɗa a kan nutsuwa, ke gaki a gida amma sai abin da ki ke so shi zaki ci, kin ga yadda suke ta wahala da ƙoƙarin faranta mana, dan Allah ki daina rashin ji kin ji, ki yi ta yi muku addu'a, nima ina yi, yanzu ki je ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu kin san zaki tahfiz". Ruma ta jima ta kwanta, sai dai bayan kwanciyarta mama ta kasa barci, sai tunanin yadda za ta ɓullowa al'amuran.

*****
Kirarin da É—aya daga cikin hadiman Ammi ke ta rangaÉ—awa ne, wadda suke kira da Baba uwani, ya tabattar wa da su Iman da ke zazzaune a falo, takawa zai shigo, nan suka din ga kintsawa, ban da Iman da ta rashe a jikin Ammi, suna hira.
Sai dai Adam tare da Jabir suka shigo, hakan ya sanya Iman jan mayafi ta rufe kan ta.
Cikin girmamawa suka gaida Ammi, Jabir ya kalli Iman ya ce "Ke ba ki san girma ya zo ba ne?, Look at you, you are now a big girl duk kin bi kin danne mana Ammi"

"To idan ba ta danne ni ba wa zata danne? Ƙyaleta 'yar auta ce ai"

Jabir ya yi wani murmushi sannan ya ce "Ammi, biyo takawa na yi, na kawo miki ƙararsa, ko ke zai ji maganar ki"

Adam ya harari Jabir, amma Jabir ya maze ya cigaba da magana.

"Ammi kin san halin ƙasarmu sarai, kin san yadda abubuwa ke gudana, duk da kasancewar sa shima wani ne, amma gaba da gabanta ta yaya zai sako Senator wakili da mutanensa a gaba, ai duk wanda ya kwana ya tashi, ya san mutane ne masu ɗaurin gindi, dan me zai tsananta?"

Ammi ta ɗan numfasa ta ce "Ban ƙi ta taka ba Jabir, amma abin nan na ga duk sabgar aikinku ce, ni ba komai nake ganewa ba, amma nima ina yawan yi masa magana a kan ya san in da zai din ga kai kansa"

"Yanzu haka Ammi, wai akwa ibom zai je, na rasa abin da zai kai shi wata akwa ibom"

Ammi ta kalli takawa, da ya kashingiÉ—a ya lumshe ido, kamar ba a kansa ake tattaunawa ba, ta yi murmushi ta ce "Rabu da shi Jabir, zan yi magana da shi"

"Ai gara dai Ammi" ya mayar da kallonsa kan Iman ya ce "Iman, É—an sama mini abin sha mai sanyi mana, zan je garden in É—an yi wani aiki"

Haushi ne ya kama Iman, ga masu aiki amma bai saka kowa aikin ba sai ita, ga Ammi a zaune balle ta ce ba zata yi ba.
Haka ta tashi ta tafi kitchen dan haÉ—a masa wani abun.

Adam kuwa É—akinsa ya wuce, ya je ya nemi wuri ya kwanta, dan ya ji kansa ya fara yi masa ciwo, tun wayewar garin yau.

A garden ta tarar da Jabir, tun da ta ɓullo ya kafeta da idanunsa, da hakan sai da ya ƙona mata rai, ta yi tsaki.
Tana zuwa ta dire masa jug da kofi, za ta juya.
"ÆŠan tsaya mana" ta tsaya cak, sannan ta waiwayo ta kalle shi.

"A tunaninki haka kawai na ce ki zo ki sameni a garden, magana zamu yi".

Cikin yanayinta mai kama da shagwaɓa ta ce "Ni uncle J karatu fa zan yi, ina da exams"

Tashi yayi ya zagaya kusa da ita yana kallonta.

"Maganata ba ta da muhimmanci kenan?"

Ta É—an ja da baya ta ce "To ina jin ka"

"Iman me na yi miki ne ki ka tsaneni, ki ke guduna kwanan nan?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Sai gani yayi kamar ta É—an razana tana kallon wuri É—aya.

Waiwaya ya yi domin ya ga mai take kallo, Mahmud ya gani a tsaye yana kallonta, gaba É—aya ta ruÉ—e.

"Zo nan" Mahmud ya faÉ—a cikin isa yana kallonta.

Jabir ya ce "Kamar yaya ta zo, haka ake yi?"

"Ban saka da kai ba, kar ka ɓata mini rai"

Jiki na tsuma, Iman ta sunkuyar da kai ta nufi in da Mahmud ya ke.

"Amma Mahmud kamar ba ka ikon nuna wa iman wannan isar, tun da dai ba wani abu a tsakanin ku"

"Jabir, kafi kowa sanin waye ni, idan ba ka kiyayeni ba, za a ji kaina da kai, ba ruwana da abin da ku ka laɓe a lambu kuna yi, abin da ya dameni shi zan yi"

Waro ido Iman ta yi, jin abin da Mahmud ya faɗa, sai dai ko kusa ba ta ga fuskar da zata kare kanta ba, haka zalika ba ta da zaɓin da ya wuce ta bi umarnin Mahmud.

Ya tasata a gaba har sashin su na Mummy, da Mummy da Fuziyya da ruƙayya duk suna falon sai kuma Samha da dama tun tasowarta kusan kullum tana gidan su.

"On your knees" yayi maganar cikin tsawa. Cikin mamaki iman ta yi abin da ya ce, tana son jin laifin da ta yi.

"Ke saboda baki da mutunci, Mummy ta aika a kiraki amma ki ce ba zaki zo ba aiki ki ke yi wa Ammi, Mummy sa'arki ce?"

Cikin rashin fahimta iman ta ce "Ni kuma? Wallahi ba wanda ya zo ya kirani"

Mummy ta ce "Au iman ruƙayya ƙarya za ta yi miki kenan, ai da ka ƙyaleta, dama ta daɗe tana nuna mini ba ni na haifeta ba, dama ba wani abun ne ya sa na ce a kirata ba, dogwayen riguna ne na saya musu, nace ta zo ta karɓi nata".

"Wallahi Mummy ban haɗu da Ruƙayya ba jiya, ruƙayya a ina muka haɗu?"

Ruƙayya ta ce "Ni zaki rainawa hankali, kina falo fa kina kallo a lokacin ki ka ce mini ba zaki zo ba"

Samha ta girgiza kai ta ce "Yaya Mahmud, ta ina zaka yi tsammanin tarbiyya a wurin 'yar da ba jinin sarauta ba, 'yar karere 'yar riƙo"

Haka suka din ga jifan iman da miyagun maganganu.

Tun da ta taso, ta buɗi ido a gidan Galadima, take fuskantar ƙalubale sharri gami da makircin hajiya Jamila wato Mummy, makira ce ta gaske.
Suka ƙare mata cin mutunci, Fauziyya ta watso mata dogwayen rigunan a jiki, Mahmud ya ce ta yi godiya ta ɗauka ta bar sashen.
Ba yadda ta iya, ta aikata abin da ya ce ta tashi ta fita gwiwa a sanyaye.

Mummy tayi murmushi, a ranta ta ce bari mu gani, yarinyar nan zata gayawa wancan mahaukacin ne ya zo yayi hayagaga ko kuwa? Idan har ya zo yayi mana tashin hankali, zan tabattarwa da Samha akwai alaƙa a tsakanin iman da Adam, ko kuma in cigaba da amfani da wannan damar, wurin rura wutar ƙiyayya tsakanin Mahmud da shi, ina baƙantawa matar nan.

*****
Mama tayi ta faÉ—i tashi, ta tarawa Abubakar kayan abinci na komawa makaranta, wanda sam shi bai san ma tana yi ba, tun da ya dawo yake ta buga-buga yana tara É—an abin da zai tafi da shi, ranar da zai koma mama ta tambaye shi babu wata matsala, ya ce mata eh ai yana da komai.
Mama ta yi murmushi, ta nuna masa watto bagco ta ce ya É—auko, ya duba. Ya É—auko ya duba, kayan abinci ne da ta tara masa.

Ya ce "Mama na gaya miki fa ina da komai, Meyasa zaki takura kan ki?"

"A'a ni ban takura kaina ba, Ubangiji Allah ya bada sa'a ya taimaka" yayi ta yiwa mama godiya, mai sunan Baba ya raka shi tasha, ya bashi dubu biyar, amma sai da suka kai ruwa rana Sannan ya karɓa.

Ruma ce ta fito daga wanka, ta tsaya a gaban mudubi daga ita sai pant, tana kallon kanta.
Mama ta kalleta ta ce "Meye haka ne ki ke tsaye tsirara ki nemi kaya ki saka"

Ruma ta juyo ta kalli mama cikin damuwa ta ce "Mama kalleni"

"Na ganki meyafaru?"

"To ba abin da ki ka gani?"

"Ni banga komai ba"

"Mama wai baki ga ƙirjina kamar ya kumbura ba?"

Mama tayi murmushi ta ce "Na gani"

"Mama to ya kike dariya, ba alamomin ciwon Cancer bane?"

Mama ta ce "A'uzubil'ahi, ba wannan bane ƙirga dangi ki ka fara"

Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Wane dangin na ƙirga, ni ina zan iya ƙirga danginmu?"

"Ba wannan ake nufi ba, girma ki ka fara zaki zama budurwa, fitowa za su yi"

Ruma ta haÉ—e rai ta ce "Ni bana son su fito"

Mama tayi dariya ta ce 'Saboda me?"

"Da nace ina son su fito a daina ce mini ƙwaila, Yaya Aliyu ya ce gara na yi zamana a haka, ai suma basu da shi"
Chapter 39 · 0% Book details