Sashe 120
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya lumshe idanunsa ya na son bacci ya É—auke shi, saboda tarin matsalolin da suke kansa, sun sanya har wani zafi cikin kansa yake yi masa.
Yayi ta karanto adduoi, a hankali bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukarsa, cikin barcin ya ji muryar rumaisa da kan yi masa gizo tana faɗin "Sarki mai koriyar alkyabba ka ɗanani a kan doki" da ire-iren maganganun ta, suka dinga kai komo a kunnensa.
A hankali ya buɗe ido, haryanzu ya kasa daina mamakin yadda rumaisa take yawan yi masa gizo. Ya canza bugiren da yake kwance yana karanto adduoi, a take wani baccin yayi awon gaba da shi, sai dai a wannan karon aisha ya din ga mafarki, mafarkin ƙarshe da yayi da ita ya ɗan razana shi, aisha ya gani tana ce masa.
"Takawa, dan Allah ka bawa rumaisa ɗan ta, kar ka ɗau hakkinta, bana son wata damuwa ta sameta, ita ce maganin damuwowinka, ko ba ka aureta ba kar ka rabata da ɗanta" a razane ya sake farkawa yana wani irin gumi, ƙirjinsa na bugawa da sauri.
Da sauri ya saukko daga kan gadon, ya buÉ—e tagar É—akinsa, ya zubawa harabar gidan ido, ya tuna abubuwa da dama da suka wakana, shekarun da suka gabata.
Ganin bashi da wata mafita, ya sanya ya shiga banɗaki yayi alwala ya fito ya ɗau alƙur'ani.
Æangaren ammi ma tsayuwar dare take yi, tana kaiwa Allah kukanta a kan iyalanta, dan addu'arta bayan nemawa kanta gafarar ubangiji, Æ´aÆ´anta kawai take yi addu'a.
Ta haɗa da roƙon Allah ya ɗorata a kan iyayen rumaisa su yarda da auren nan da take son haɗawa, dan a jikinta take jin rumaisa alkairi ce ga ɗan ta.
Yau jikin mama da ɗan sauƙi, ruma sai shirin tafiya tahfiz take yi, su Huzaifa sun goge mata uniform ɗin, ta cika tsakar gida da waƙe-waƙe kamar an yi mata bushara da wani abu mai muhimmanci.
"Ruma ki rufe mini baki da waƙe-waƙen nan, ki yawaita tasbihi, wannan surutan da waƙe-waƙen ba in da za su kai ki"
"Mama ina tasbihin nan fa".
"A'a, ni wasu lokutan ina raina ibadar da ki ke yi, ki na da ƙarancin ibada rumaisa, idan kina cikin farinciki ki yawaita ambaton Allah, dan wasu lokutan idan kana cikin matsala ko damuwa sai addu'a ma ta gagareka, ki din ga yawaita ambaton Allah ba waƙa ba"
Cikin mamaki rumaisa ta ce "Mama yanzu sai damuwa ta yi wa mutum yawa ya kasa ambaton Allah, to ko a hannun 'yan bindiga, addu'a na yi ta yi musu, Allah ya ƙwatoni, amma ni mai zai dami mutum ya kasa addu'a "
Mama ta yi murmushi ta ce "Rumaisa kenan, lokaci yana nan zaki gane abun da nake nufi".
"Au fata ki ke yi mini" tayi maganar cikin tura baki.
"Ya za ayi in yi miki fata, faɗa nake yi miki, ki ƙara nutsuwa".
"To hajiya mama, yanzu dai ki bani kuÉ—in makaranta zan tafi"
"Ke idan babu kuɗin makarantar ba zaki ba kenan?" Huzaifa ya tambayeta yana ƙoƙarin ɗaukar agogonsa.
"Ni fa ba na son katsalandan ina ruwanka"
"Ni kar ku yi mini faÉ—a, ki É—auka ki tafi".
Rumaisa ta É—au kuÉ—in, ta fice tana hararar Huzaifa.
Ammi ta din ga lissafin ta ina za ta ɓullowa wannan al'amari, turaki zata fara gayawa, ko kuwa ta fara nemo iznin majaifiyar rumaisa tukuna?
Daga bisani ta yanke za ta fara tuntubar ɓangaren rumaisa, idan sun amince shikenan, sai dai tana fatan su amince ɗin ma.
Takawa har garin Allah ya waye bai samu ya rintsa ba, abubuwa da yawa sun dame shi, kasancewar yau weekends ne, ya sanya karyawa ma a É—akinsa yayi bai fita ko ina ba. Dama shi ba wasu abokai ne da shi ba, daga abokan aikinsa sai su jabir.
Wayarsa ta cika masa kunne, duk da gandar da yake ji, da ya gaji da jin rurin wayar, sai da ya tashi ya É—auko wayar ya duba.
Kakin rundur Æ´an sanda ne cp baba habu yake kiransa, adam ya É—aga wayar tare da yin sallama.
Cp ya amsa masa suka gaisa sannan ya ɗora da cewa "Adam kana garin nan kuwa? Wai ba zaka fito ka yi magana a kan abun da yake faruwa ba, sai sharri ake yi maka kala-kala kai kuma ka ƙi magana"
Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Me zan ce? Ko na faɗa ba za a yarda da ni ba, ƙanin mahaifina ya fito ya wanke ni, amma ba a fasa surutu ba, me zan ce? Su yi ta yi idan sun gaji za su daina ne"
"Kana nufin ba zaka ce komai ba?"
"Ko na ce ba za a daina ba, ka ga maganar ba ta da amfani"
Cp ya ce "Ai shikenan, ɗazu mun yi magana da commissioner, saboda sabon posting ɗin da gidan jaridar nan ke cigaba da fitarwa, na yi magana da manema labarai, na sanar musu hukumar ƴan sanda mun san da case ɗin, sai dai abu ne na sirri da ba ya buƙatar a fito ayi ta yayatawa, shi ya sanya muka yi shiru muka yi ta bincike, kuma haryanzu muna kan yi ma."
Adam ya nemi wuri ya zauna a gefen gadonsa ya ce "To shikenan yallaɓai, na gode sosai da sosai"
"Kar ka damu, ai hakkinmu ne baka kariya, kuma abun da muka faɗa hakan yake ai, Allah ya tsare, wannan ba wani abu bane ba duk aikin maƙiya ne, kuma ba za su yi nasara ba"
Adam ya ce "Haka ne, na gode sosai"
"Masha Allah, Allah Ya ƙara tsarewa"
"Amin ya rabb sir, na gode" daga haka ya kashe wayar. Yana gama wayar ya ji zaman É—akin ya ishe shi, dan haka ya fita domin ya gaida ammi ya É—an fita.
Duk a falon sashen ammi ya tarar da su, har ammin, ana koyawa Sabir zama an shiryashi cikin wasu kaya masu kyau, an zaunar da shi a gefen kujera, cikin dabara iman tana taje masa sumar kansa, sai kai hannu yake yana turewa alamar ba ya so.
Adam ya fara gaida ammi, sannan ya É—au sabir ya zauna da shi a jikinsa.
Adam ya karɓi brush ɗin hannun iman, ya cigaba da taje masa kai, amma ya cigaba da kai hannu yana turewa yana son yin kuka.
"Kai rigimamme, baka son gayu?" Adam yayi maganar yana murmushi tare da kallon ɗan nasa cike da ƙauna.
Sabir yayi shiru yana kallonsa.
"Yi mini dariya mana, an ce kana dariya amma ba ka taɓa yi mini ba"
Ammi ta ce "Kai ai wannan ɗan naka kai ya yo, babarsa kawai yake washewa baki gaba ɗaya yayi mata dariya, har mamakin irin soyayyar da ke tsakaninsa da ita nake yi, da ya ganta har wani ƙara nutsuwa yake yi".
A ransa ya ce 'Aikuwa ba zan ba ta riƙonsa ba, ya tashi a sangarce da rashin kunya kamarta ba' ya ɗaga kai yana kallon ƙwayar idon sabir, take aisha ta sake faɗo masa a rai, dan suna ɗinar kama da sabir, duk da ya fi kama da shi.
Ammi ta ce "Ina ta magana ka yi shiru, tunanin me ka ke yi ne?" Yana É—ago ido Ammi ta ga hawaye kwance a idonsa.
Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"
Yayi murmushi ya ce "Lafiya lau ammi"
Ammi za ta yi magana, hadimarta ta shigo, ta durƙusa ta ce su Samha ne suke neman iso.
Ammi ta ce, ace su shigo.
Samha ce da ruƙayya, suka shigo tare tana ganin adam sai da ta yi hamdala a zuciyarta, ta wani lumshe ido, wata irin ƙaunarsa da soyayyarsa na sake ratsata.
Suka ƙarasa, suka gaida ammi ta amsa musu cikin fuska, samha ta kalli adam ta ce "Yaya ina kwana?" Ta yi maganar cikin rausaya.
"Lafiya ƙalau, kuna lafiya?"
"Lafiya ƙalau, sabir na zo gani, ammi yaushe za'a kai mana shi ne? Na gaji da jiran na kasa jurewa".
Ammi ta ce "Banda abunki samha, yaron ai haryanzu jariri ne, ba a haÉ—aku da jego ba".
"Haba ammi, tun da muka rasa fulani ai shi ne madadinta"
Ta matsa kusa da adam, za ta ɗau sabir a hannunsa, sai da ta taɓa shi, wani irin kallo take masa ji take kamar ta rungume shi, ko ta samu sassauci a kan abun da take ji game da shi.
Ta ɗauki sabir tana yi masa murmushi, wanda a ƙasan zuciyarta ji take kamar ta buga shi da ƙasa, dan yadda ba ta ƙaunar uwarsa shi ma ba son sa take yi ba.
Miƙa sabir yayi ya hau kuka, duk yadda ta so ta rarrashe shi yaƙi yin shiru, ya cigaba da kuka ba shiri adam ya karɓe ɗan sa, ta ji tamkar ta dunƙule hannu ta daki kan yaron ko ta huce.
Cikin iya siyasa ta ce "Ammi wai har ya iya ƙyuya ne?"
"To gashi dai ya yi miki, É—an na ku ne É—an ganin dama, ko dariyarsa babarsa kawai yake yi wa"
Da sauri samha ta ce "Wace babar ta sa?"
"Rumaisa, yarinyar da ta zo da shi"
Jin an ambaci labarin da Mummy ke son ji ya sanya ruƙayya cewa "Ai ammi haryanzu tana nan?"
"Tana nan mana, ina za ta je?"
"To ammi zuwa take ta ganshi?"
Kan ammin ta bata amsa samha ta ce "Ai an ce mini an kai ta wurin turaki rannan ko?"
Ammi ta ce "Eh"
Ruƙayya ta sake cewa "To ammi gidan nan take zuwa?"
Maimakon ammi ta ba ta amsa sai ta ce "Ruƙayya an ce mini Mahmud ya zo gari ko?"
"Eh ya dawo"
Ammi ta ce "To masha Allah"
Iman ta É—auko baby carrier ta ce "Yaya kawo na saka shi a Carrier ko zai koma barci, na ga yana ta rigima dama yau da wuri ya tashi"
Adam ya ce "Zo ki É—au abunki iman, na fuskanci duk abin da na yi iman sai kin nuna mini ban iya ba, ni ban san a ina ki ka koyi raino ba, tun da mu dai ba jariri ne da mu ba"
Iman ta yi dariya ta ce "Ni na isa?"