← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 174

Sashe 174

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Iman ta ce "Ke dai kawai ki ce, an taɓa miki miji kin ji haushi. In dai yaya jamil ne sun saba, faɗa da takawa kuma daga baya su zo su shirya. Amma duk da haka na yi mamakin yadda ki ka iya kawo, yaya Mahmud sashen nan, ba ya son ammi da abun da ya shafe ta, balle adam. Lokaci na ƙarshe da ya zo, shi ne lokacin da aka fasa aurena, saboda rashin asali, ammi ta roƙe shi ya aureni, har da kukanta, ya ce ba ya so na, ba zai aureni ba". Ta yi maganar hawaye fal idonta.

Rumaisa ta yi shiru, ta ce "Wane irin abu ne wannan kuma? To duk saboda me? Ban gane ba ki da asali ba"

Iman ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce "Zan yi miki bayani, yanzu mu cigaba da addu'a papan mimi ya warke" ta yi maganar cikin ƙarfin hali tana murmushi.

"Shikenan, ara mini wayarki, na kira gida na gaya musu papa ba lafiya".

Iman ta ce "Amma idan mai sunan baba zaki kira, ki yi masa magana ta what's app, ya hana ni kiransa a waya".

Ruma ta ce "Au kuna waya ne dama?" Ta yi maganar tana dariya.

Da sauri Iman ta ce "A'a, ba waya muke yi ba, ke ce da ki ka kira rannan bai É—aga ba".

Ruma ta yi dariya ta ce "BuÉ—e mini data mu yi magana da shi".

Iman ta karɓa ta kunna mata data, ta ba ta, yaya umar ta ga iman ta yi saving number.
Ruma ba ta ce komai ba, ta yi masa voice message "Mai sunan baba, ni ce, ka gaya wa mama mijina ba shi da lafiya, mu na gidan ammi, idan ka ga message É—in dan Allah ka yi mini magana, rumaisa ce".

Iman ta zare ido ta ce "Ba kya jin kunya, ki ke cewa ace da ammi mijinki babu lafiya"

Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce "To me zan ce? Ai maman ma mijina take ce masa, bari na je na gani ko ya tashi, idan mai sunan baba ya yi magana, sai ki kira ni" ta fita daga ɗakin, ta tafi na ammi.

Ammi ba ta É—akin, ta tarar da adam a zaune, sai dai ta ga samha a zaune a gefen sa, da flask É—in abinci.

Wani abu ne mai nauyi, ya daki zuciyar rumaisa, da ba za ta iya tantance ko menene ba.

Iman kuwa ta cigaba da chatting É—in ta, sai ga video call na mai sunan baba.

Gudun kar ta yi laifi, kan ta kai wa ruma wayar ta katse, ya sanya ta É—aga, gabanta ya na faÉ—uwa.

Maimakon ya ga rumaisa, ya ga kyakywar fuskar iman, ta bayyana a kan screen É—in wayarsa.

Ta É—an sunkuyar da kai ta ce "Barka da yamma yaya umar"

Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ƙare mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa.

Ayshercool
08081012143
What's app only please, ban da kira please 🙏.
₦500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank.
Chapter 174 · 0% Book details